Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/1 p. 17
  • Mai Ta da Matattu Luka 7:11-15

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mai Ta da Matattu Luka 7:11-15
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • “It Can’t Be True!”
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
  • Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • “Ku Sani Kuma Ƙaunar Kristi”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Mene ne Za Mu Iya Koya Daga Muꞌujizan Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/1 p. 17

Ka Kusaci Allah

Mai Ta da Matattu Luka 7:11-15

WANI na kusa da kai ya rasu? Idan haka ne, to ka fuskanci ɗaya daga cikin abubuwa na baƙin ciki a rayuwa. Mahaliccinmu ya fahimci baƙin cikinmu. Fiye ma da haka, zai iya ta da matattu. A cikin Littafi Mai Tsarki, ya ba mu labarai game da tashin matattu a dā domin ya nuna mana cewa shi ba rai kawai yake bayarwa ba amma kuma yana iya ta da matattu. Bari mu bincika ɗaya daga cikin tashin matattu da ya ba wa Ɗansa, Yesu Kristi ikon yi. Labarin wannan mu’ujizar yana rubuce cikin Luka 7:11-15.

A shekara ta 31 A.Z. Yesu ya yi tafiya zuwa birnin Nayin da ke Galili. (Aya ta 11) Wataƙila yamma ta yi kusa sa’ad da ya isa bayan garin. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da ya kusanci ƙofar birni, sai ga wani matace, ana ɗauke da shi, tilo ne ga uwatasa, ita kuwa gwauruwa ce: mutane dayawa kuma daga cikin birni suna tare da ita.” (Aya ta 12) Za ka iya fahimtar irin baƙin cikin wannan matar gwauruwa? Da mutuwar ɗanta tilonta, ta yi rashin mai yi mata tanadi kuma mai kāre ta sau biyu ke nan.

Yesu ya mai da hankalinsa a kan mamar yaron, wadda ƙila tana tafiya kusa da makarar da aka ɗauki gawar ɗanta a ciki. Labari ya ce: “Sa’anda Ubangiji ya gan ta, ya yi juyayi bisa gareta, ya ce mata, Kada ki yi kuka.” (Aya ta 13) Matsalar gwauruwar ya dami Yesu ƙwarai. Wataƙila shi ma yana tunanin mamarsa, ƙila ita ma gwauruwa ce a lokacin, wadda ba da daɗewa ba za ta yi baƙin ciki dominsa.

Yesu ya tunkari mutanen, amma ba domin ya bi su ba. Ya Je ya taɓa makarar da iko kuma dukan jama’ar suka tsaya. Da muryar wanda aka ba wa iko bisa mutuwa ya ce: “Saurayi, ina ce maka, Ka tashi. Mataccen ya tashi zaune, ya soma yin magana. Ya bada shi ga uwatasa.” (Luka 14, 15) Da wannan saurayin ya mutu ya kasance ba na mamarsa ba ne kuma. Saboda haka sa’ad da Yesu ya “bada shi ga uwatasa,” suka sake zama iyali ɗaya. Baƙin cikin wannan gwauruwar babu shaka ya koma hawayen farin ciki.

Zuciyarka tana muradin samun irin wannan farin ciki ne, kana so ka sake saduwa da ƙaunatattunka waɗanda suka mutu? Ka tabbata cewa Allah ya san yadda kake ji. Juyayin Yesu ga wannan macen ya nuna juyayi ne na Allah, domin Yesu ya nuna mutumtakar Ubansa. (Yohanna 14:9) Littafi Mai Tsarki ya koyar da mu cewa Allah yana da muradin ya ta da waɗanda suka mutu da bai mance da su ba. (Ayuba 14:14, 15) Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ya ba mu bege mai ban sha’awa, wato, begen rayuwa a cikin aljanna a nan duniya kuma za mu ga tashin waɗanda muke ƙauna daga matattu. (Luka 23:43; Yohanna 5:28, 29) Me ya sa ba za ka ƙara iliminka na Mai ta da matattu ba da kuma yadda za ka sami wannan bege?

[Hoto a shafi na 17]

“Matacen ya tashi zaune, ya soma yin magana. Ya bada shi ga uwatasa”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba