Gayyata Zuwa Jawabi na Musamman Za Ka Sami Kwanciyar Rai A Duniyar Nan Ta Wahala!
Za a ba da wannan jawabi da ke bisa Littafi Mai Tsarki a ƙasashe 230 a duka duniya. A yawancin wurare, za a ba da jawabin ne a ranar Lahadi, 15 ga Afrilu, 2007. Menene za ka koya? Ka yi la’akari da waɗannan:
Menene ya sa biliyoyin mutane a duniya ba su da kwanciyar rai?
Yaushe ne ainihin kwanciyar rai ta ɓace?
A ina, kuma ta yaya za ka sami ainihin kwanciyar rai?
Za ka sami amsoshin waɗannan tambayoyin idan ka saurari wannan jawabin mai muhimmanci da ke bisa Littafi Mai Tsarki, da za a ba da a wurare da yawa. A wurare da yawa, za a ba da jawabin ne a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah. Shaidu da suke yankinku za su yi farin cikin ba ka adireshin wurin taron da kuma lokacin taron. Muna gayyatarka zuwa wannan jawabin Littafi Mai Tsarki mai ƙarfafawa.