Tambayoyi Daga Masu Karatu
Ta yaya muka sani cewa yadda aka kwatanta hikima a Misalai 8:22-31 ya shafi Yesu Kristi ne kafin ya zama mutum?
Kwatanci na hikima a cikin littafin Misalai ta ce: “Ubangiji ya yi ni tun farkon hanyarsa, tun gaban ayyukansa na dā . . . Tun duwatsu ba su kafu ba, tun gaban tuddai aka fito da ni . . . Lokacin da ya shirya sammai ina nan . . . Sa’annan ina nan wurinsa, gwanin mai-aiki ne, kowace rana ni ne abin daularsa, kullum ina farinciki a gabansa, . . . daulata tana wurin ’yan adam.”
Wannan nassi ba ya magana kawai a kan hikima ta Allah ko kuma hikimar da ba a gani ba. Me ya sa? Saboda hikima da aka kwatanta a nan an “yi” ko halicce ta ne a farkon hanyar Jehobah. Jehobah Allah yana wanzuwa koyaushe kuma a koyaushe yana da hikima. (Zabura 90:1, 2) Hikimarsa ba ta da mafari; kuma ba a halicce ta ba. Ba a kuma ‘fito da ita ba.’ Bugu da ƙari, irin wannan hikima an ce tana magana kuma tana aiki, wannan yana wakiltar mutum.—Misalai 8:1.
Littafin Misalai ya ce tun da daɗewa hikima tana tare da Jehobah, Mahalicci, a matsayin “gwanin mai aiki.” Babu shakka, wannan ya shafi Yesu. Kafin ya zo duniya, Yesu ya yi aiki tare da Jehobah, shi ya sa kalmar Allah ta ce: “Shi ne kuwa gaba da dukan abu, a cikinsa kuwa dukan abu suna harhaɗe.”—Kolossiyawa 1:17; Ru’ya ta Yohanna 3:14.
Ya dace a ce Ɗan Allah ne hikima, tun da shi ne ya bayyana manufar Jehobah mai kyau da kuma dokarsa. Kafin ya zama mutum, Yesu Kalmar Allah ne, ko kuma Kakakinsa. (Yohanna 1:1) An kwatanta shi a matsayin “ikon Allah, da hikimar Allah.” (1 Korinthiyawa 1:24, 30) Wannan kwatanci ne mai kyau wanda aka yi wa Ɗan Allah, wanda ƙaunar da yake da shi ga mutane ya motsa shi ya ba da ransa fansa don mutane!—Yohanna 3:16.
[Hoto a shafi na 27]
Kafin “duwatsu . . . aka fito da ni”