Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 2/1 p. 32
  • Kana Kama Da Bishiyar nan Lagani Auna Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Kama Da Bishiyar nan Lagani Auna Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 2/1 p. 32

Kana Kama Da Bishiyar nan Lagani Auna Kuwa?

AWANI ƙauye bayan garin Port Moresby a Papua New Guinea, masu hidima biyu suna dawowa daga wa’azi. Sa’ad da suke tafiya, suka ga wata kyakkyawar bishiya. Tsohon ya ce, “ga lagani auna!” Ya dubi matashin, ya ci gaba: “Wannan sunan yana nufin ‘bishiyar shekara shekara.’ Kowace shekara tana zubar da ganyenta sai ka ga kamar ta burshe ba kamar sauran bishiyoyi da ke cikin jeji ba. Amma, idan aka soma damina sai ta farfaɗo ta yi furanni, kuma ta zama kyakkyawa.”

Da darassi da za a koya daga bishiyar lagani auna. Wasu gwanaye sun ce yana cikin itatuwa guda biyar masu furanni mafi kyau da muke da su a duniya. Ko da tana kaɗe furanni da ganyenta da rani, bishiyar tana tara ruwa. Tushen yana da ƙarfi kuma zai iya yin girma cikin duwatsu mai zurfi cikin ƙasa. Ta haka tana tsayawa a lokacin iska mai ƙarfi. A taƙaice, tana cin gaba ta wajen jimrewa a yanayi mai wuya.

Muna iya iske kanmu cikin yanayi da zai gwada bangaskiyarmu. Menene zai taimake mu mu jimre? Kamar bishiyar lagani auna muna iya sha da kuma tara ruwan Kalmar Allah mai ba da rai. Ya kamata mu manne wa ‘dutsenmu’ Jehobah gam gam, da kuma ƙungiyarsa. (2 Sama’ila 22:3) Hakika, bishiyar lagani auna abin tuni ne mai kyau cewa ko a yanayi mai wuya ma, muna iya samun ƙarfi na ruhaniya da kuma jamala idan muka yi amfani da tanadi da Jehobah yake yi mana. Ta yin haka, za mu “gāda alkawura” da ya yi mana, har da alkawarin rai madawwami.—Ibraniyawa 6:12; Ru’ya ta Yohanna 21:4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba