Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 8/1 pp. 3-4
  • Kana Fama da Yadda Kake Ji?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Fama da Yadda Kake Ji?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Zai Sa Ka Sami Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Jehobah Zai Iya Taimaka Maka Idan Ka Yi Sanyin Gwiwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Jehobah Yana Tare da Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • How Can I Live With My Grief?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 8/1 pp. 3-4

Kana Fama da Yadda Kake Ji?

AYAWANCIN rayuwarta, Lena ta yi ta fama da rashin jin daɗi game da kanta. Ta ce: “Shekaru da yawa da aka yi ana lalata da ni lokacin da nake yarinya ya kashe mini daraja.” “Na ji ba ni da wani amfani.” Simone ma ta tuna lokacin da take yarinya, ta ce, “A can cikin birnin zuciyata ina jin ba ni da wata daraja.” Irin matsanancin baƙin ciki da yake samuwa daga sakamakon irin wannan yanayi kamar dai ya zama ruwan dare a yau. Wasu masu ba da shawara ta tarho ga matasa sun ce kusan rabin waɗanda suke yi musu magana suna furta “rashin martabarsu.”

In ji wasu masana, rashin daraja yana samuwa ne sa’ad da mutane suka sa wasu su ji ba su da martaba. Irin wannan yanayi yana samuwa ne sa’ad da aka riƙa cin mutuncin mutum, aka riƙa kushe shi, ko kuma aka riƙa zaginsa. Ko da menene dalilin, sakamakon yana raunanawa yana iya halakarwa ma. Wani bincike na masana lafiya da aka yi a baya bayan nan ya nuna cewa yawancin mutane waɗanda ba sa jin daɗi game da kansu suna da yawan rashin amincewa da kansu da kuma wasu mutane, saboda haka cikin rashin sani suna yi wa abokantaka da dangantaka zagon ƙasa. Wani rahoto ya ce, “suna jawo irin yanayi da ba sa so.”

Mutane da suke jin haka sau da yawa sun faɗa cikin abin da Littafi Mai Tsarki ya kira “alhini.” (Zabura 94:19) Suna jin cewa ba su cancanta ba. Idan wata matsala ta samu, a take sai su ga laifin kansu. Ko da yake wasu za su yabe su saboda abin da suka cim ma, a can cikin zuciyarsu sai su ji ba da daɗewa ba za a fallashe su. Domin sun gaskata cewa ba su cancanci farin ciki ba, da yawa cikin su sai su faɗa cikin halaye masu halakarwa da suke jin ba yadda za su yi su yi gyara. Lena, da aka ambata da farko ta sami matsala mai tsanani na cin abinci domin tana jin ba ta da martaba, kuma ta ce, “na ji ba yadda zan yi in yi gyara.”

Waɗanda suke kokawa da irin wannan “alhini” haka za su ƙarasa ke nan? Ko akwai wani abin da za a iya yi a yi kokawa da wannan yanayi? Littafi Mai Tsarki ya ba da mizanai da shawarwari da za su taimaka a yi nasara a wannan kokawa. Menene ne waɗannan mizanai, kuma ta yaya suka taimaki waɗanda suke fama, suka sami farin ciki a rayuwa? Talifi na gaba zai ba da bayani.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba