“Za Mu So Mu Ce ‘E!’ ”
OFISHIN reshe na Shaidun Jehovah a Nijeriya ya sami wata wasiƙa wadda kaɗan daga ciki ya ce:
“Ɗanmu, Anderson, ya mutu yana da shekaru 14. Kafin ya mutu, yana kiwon zakaru guda biyu. Yana son ya sayar da su domin ya aika wa ofishin reshe kuɗin gudummawa ga aikin wa’azi na dukan duniya. Amma ya mutu kafin a sayar da su.
“Domin muradinsa, mu iyayensa, mun yi kiwon zakarun kuma mun sayar da su. Muna aika muku da kuɗin a matsayin gudummawa na Anderson. Domin alkawarin Jehovah muna da tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba—za mu ga Anderson. Za mu so mu ce, ‘E!’ idan ya tambaye mu ko mun cika muradinsa. Hakika, muna sauraron lokacin da za mu ga Anderson da ‘taron shaidu masu ɗumbun yawa’ da za a ta da daga matattu.’—Ibraniyawa 12:1; Yahaya 5:28, 29.
A yadda wasiƙar sama ta nuna, imani ga tashin matattu shi ne begen da ke ƙarfafa Kiristoci na gaskiya. Miliyoyin iyalai kamar iyalin Anderson za su yi farin ciki sa’ad da za su marabci ƙaunatattunsu wadda magabciya mutuwa ta ɗauke!—1 Korantiyawa 15:24-26.
Kalmar Allah ta miƙa mana wannan bege mai ƙarfafawa na tashin matattu cewa ɗaya ne daga cikin abubuwan da za su auku a cikin sabuwar duniya ta adalci a Mulkin Allah. (2 Bitrus 3:13) Sa’ad da yake bayyana abubuwan da Allah zai yi wa mutane a wannan lokacin, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”—Wahayin Yahaya 21:4.