A Waɗanne Hanyoyi ne Bayin Allah Suke Kamar Itatuwa?
DA YAKE maganar mutum da yake farin ciki a ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma yana amfani da su a rayuwarsa, mai Zabura ya ce: “Za ya zama kamar itacen da aka dasa a magudanan ruwaye, wanda yana bada ’ya’yansa a cikin kwanakinsa; ganyensa ba ya yi yaushi ba; kuma cikin iyakar abin da ya ke yi za shi yi albarka.” (Zabura 1:1-3) Me ya sa wannan kwatancin ya dace?
Itatuwa na iya rayuwa na dogon lokaci. Alal misali, an ce wasu itatuwan zaitun a wuraren Bahar Maliya sun yi rayuwa na shekaru dubu ɗaya zuwa dubu biyu. Haka nan ma, itatuwan kuka na Afirka ta tsakiya suna rayuwa na shekara aru-aru, kuma an ce wata bishiyar fayin (bristlecone pine) a California ta yi rayuwa na shekaru 4,600. A cikin daji, itatuwa da suka yi girma sosai sau da yawa suna da amfani ga mahallinsu. Alal misali, dogayen itatuwa suna ba da inuwa ga ƙananan itatuwa, kuma ganyaye da suke faɗiwa daga itatuwan suna kyautata ƙasa.
Itatuwa da suka fi tsawo a duniya suna girma tare a kurmi, inda itatuwa suke tallafa wa juna. Tun da yake saiwoyinsu suna sarƙan juna, itatuwa da yawa da suke haɗe haka suna iya tsayayya wa hadari fiye da itace da shi kaɗai yake tsaye a fili inda ciyayi suke. Saiwa mai zurfi na sa itace ya samu isashen ruwa da abinci daga cikin ƙasa. A wani lokaci, saiwar na iya zurfi sosai fiye da tsawon itacen, ko kuma saiwoyi za su iya faɗaɗa sosai fiye da ganyen itacen.
Manzo Bulus mai yiwuwa yana maganar itace sa’ad da ya bayyana cewa ya kamata Kiristoci su “yi tafiya a cikin [Kristi] hakanan, dasassu, ginannu kuma cikinsa, kafaffu cikin bangaskiya.” (Kolossiyawa 2:6, 7) Hakika, Kiristoci za su iya dage cikin bangaskiyarsu idan sun dasu ƙwarai cikin Kristi yadda itace yake tsaye sosai a ƙasa da saiwarsa mai ƙarfi.—1 Bitrus 2:21.
A waɗanne hanyoyi kuma za a kamanta bayin Allah da itatuwa? Yadda itatuwa da suke tare suke samun taimako daga itatuwan da ke kusa da su, haka dukan waɗanda suke kusa da ikilisiyar Kirista suke samun taimako daga ’yan’uwa masu bi. (Galatiyawa 6:2) Kiristoci masu aminci da suka ƙware da suke da saiwoyi na ruhaniya masu zurfi suna taimakon ’yan’uwa sababbi su kasance da ƙarfi cikin bangaskiya, har lokacin da suke fuskantar hamayya mai kama da hadari. (Romawa 1:11, 12) Sababbin Kiristoci suna iya girma a ‘inuwar’ kāriya na bayin Allah da suka fi ƙwarewa. (Romawa 15:1) Dukan waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista na dukan duniya suna amfana daga abinci na ruhaniya mai ƙarfafawa da raguwar shafaffu da sune “itatuwa na adalci,” suke tanadinsa.—Ishaya 61:3.
Abin farin ciki ne cewa dukan bayin Allah suna da begen ganin cikar alkawarin da ke cikin Ishaya 65:22, wanda ya ce: “Kamar yadda kwanakin itace su ke, hakanan kwanakin mutanena za su zama.”
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 19]
Godo-Foto