Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Wani Tsarin Telibijin Ya Ɗaukaka Allah
MANZO Bulus ya ce “waɗansu dai suna yin wa’azin Kristi da husuma, waɗansu kuma da nufin alheri.” (Filibbiyawa 1:15) Wani lokaci wasu da suke so su ɓata sunan mutanen Jehovah ma, ba da saninsu ba sun sa masu zuciyar kirki su bi gaskiya.
A Nuwamba 1998, an nuna a cikin wani tsarin telibijin na ƙasan a yaren French game da ayyukan da ake yi a Bethel, reshen Shaidun Jehovah da ke Louviers, Faransa. Ko da yadda mutane suka ji game da shi ya bambanta, an sami sakamako mai kyau da ba a yi tsammani ba.
Anna-Paula tana cikin waɗanda suka kalli tsarin, tana zama mil 35 kawai daga Bethel. Anna-Paula wadda aka yi mata kisan aure ce, mai yara biyu, da take neman aiki. Saboda haka, washegari da safe, ta yi waya zuwa Bethel tana neman aiki a wajen. Ta ce: “Na fahimci cewa wuri ne mai kyau kuma aikin da ake yi a wurin mai amfani ne.” Ta yi mamaki da ta ji cewa masu aiki a Bethel masu hidima ne waɗanda suke ba da kansu! Bayan an ɗan bayyana mata ayyukan Shaidun Jehovah, ta yarda wata Mashaidiya ta ziyarce ta.
Sa’ad da Léna, majagaba a wata ikilisiya ta ziyarce ta, suka jima suna taɗi, sai Anna-Paula ta amshi littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada.a Kafin ziyara ta gaba, Anna-Paula ta riga ta karance littafin kuma tana tambayoyi da yawa. Ta yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Anna-Paula ta ce: “A gare ni zarafi ne, na sanin Kalmar Allah. Ban taɓa riƙe Littafi Mai Tsarki a hannuna ba.”
A Janairu, Anna-Paula ta ziyarci Bethel, kuma a mako na gaba ta halarci taronta na farko na Kirista. Ba da daɗewa ba bayan haka, ta fara nazarin Littafi Mai Tsarki da yaranta kuma tana wa abokanta wa’azi. Ta ce, “ba zan iya ƙin gaya wa wasu abin da nake koya ba. Ina so in gaya wa mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki kuma in yi musu ta’aziyya.” Bayan ta yi ta kokawa ta sha kan wasu matsaloli, Anna-Paula ta fara halartan taro a kai a kai. Cin gabanta ya yi sauri kuma aka yi mata baftisma a 5 ga Mayu, 2002.
Ban da haka, domin misalin Anna-Paula mai kyau da ƙwazo a wa’azi, mamarta, ta fara nazarin Littafi Mai Tsarki, ba da daɗewa ba aka yi mata baftisma. Anna-Paula ta ce: “Ta yi farin ciki sosai. Kowacce rana ina gode wa Jehovah da ya sa in san shi da kuma dukan albarka da ya yi mini.”
[Hasiya]
a Shaidun Jehovah ne suka buga.
[Hotuna a shafi na 3]
A sama: Anna-Paula
A ƙasa: Ƙofar ofishin reshe na Faransa