“Kalmar Allah Tana Da Iko Ƙwarai!”
“MAGANAR Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.” (Ibraniyawa 4:12) Da yake ba da tabbacin ikon Kalmar Allah, 2003 Calendar of Jehovah’s Witnesses ya ba da labarin rayuwar mutane shida kewaye da duniya. A ƙarƙashin jigon nan “Before and After,” (Kafin Kuma Bayan Haka), kalandar ta nuna yadda aikin ilimantarwa na Shaidun Jehovah yake taimakon mutane su kyautata ɗabi’arsu, su bar mummunar yayin rayuwa, su ƙarfafa rayuwar iyalinsu, kuma su gina dangantaka da Allah.
An samu wasiƙun godiya game da kalandar 2003. Ga wasu:
“Wannan kalanda tabbaci ne ga Kiristoci na gaskiya cewa akwai wasu kamar su da suke yaƙi ƙwarai domin bangaskiya. Yanzu suna iya kallon hotuna da zai tuna musu canje-canje da wasu suka yi.”—Steven, daga Amirka.
“Ina son na rubuta waɗannan kalmomin domin ku san yadda kalanda ta 2003 ta motsa zuciyata. Babu kalanda da ta shafe ni haka. Zan riƙa ɗaukan wannan kalanda a jakar wa’azina domin na nuna wa mutane misalai da kuma tabbaci na yadda Littafi Mai Tsarki yake shafan mutane.”—Marc, daga Belgium.
“Kalandar ta motsa ni ƙwarai. Na cika da tsotsuwar zuciya da na karanta kuma na ga yadda Jehovah ya sake waɗannan mutane. Domin haka, na motsa na ci gaba da yin canji a rayuwata. Yanzu na fi ji ina tare da ’yan’uwanmu ta dukan duniya.”—Mary, daga Amirka.
“Yesu ya motsa ƙwarai don yanayi na ruhaniya na taron. Na gode muku da kuka yi koyi da misalin Kristi ta wajen buga labaran rayuwa da suka fito a kalandarmu ta 2003. Kalanda ba ta taɓa sa na yi hawaye haka a rayuwata ba.”—Cassandra, daga Amirka.
“Sa’ad da nake ’yar shekara 11, na soma shan taba; bayan haka na soma shan ƙwayoyi. Sau da yawa na yi tunanin kashe kaina. Sa’ad da na san Jehovah, an taimake ni na daina waɗannan halaye. Wannan kalanda tana da muhimmanci a gare ni. Misalan ’yan’uwana kewaye da duniya sun ƙarfafa ni. Yanzu na san cewa ba ni kaɗai ba ce nake wannan yaƙi kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne mu ƙaunaci Jehovah kuma mu bauta masa da dukan zuciyarmu.”—Margaret, daga Poland.
“Kalmar Allah tana da iko ƙwarai! Sa’ad da na samu kalanda ta 2003, na yi ƙoƙari kada na yi kuka. Waɗannan labarai, har da hotuna, suna ƙarfafa bangaskiya.”—Darlene, daga Amirka.
“Yayin rayuwar dā na wasu cikin waɗannan mutane sun yi kama da yayin rayuwata ta dā. Jehovah ya ba ni ƙarfi na daina mummunar halaye. Na gode muku ƙwarai don waɗannan labaran rayuwa na gaske.”—William, daga Amirka.