Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 11/1 p. 32
  • “Na Sami Abokantaka, Ƙauna, da Kuma Kulawa”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Na Sami Abokantaka, Ƙauna, da Kuma Kulawa”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 11/1 p. 32

“Na Sami Abokantaka, Ƙauna, da Kuma Kulawa”

“BISA ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Daidai da kalmomin Yesu, ƙauna ta zama abin da aka san ’yan’uwanci na Kirista na farko da ita. Da yake rubutu fiye da shekaru ɗari bayan mutuwar Kristi, Tertullian ya yi ƙaulin abin da waɗanda suka lura suka ce: ‘Dubi yadda suke ƙaunar juna da kuma yadda suke a shirye su mutu domin juna.’

Ana iya samun irin wannan ƙaunar a duniya har yanzu kuwa? E. Ka yi la’akari da misalin wata wasiƙa da ofishin reshe na Shaidun Jehovah a Brazil suka samu. Wata mace mai suna Marília ce ta rubuta wasiƙar, ta ce:

“Lokacin da muke zama a Villa Mercedes, Argentina, mamata wadda Mashaidiyar Jehovah ce ta yi ciwon amosanin gaɓa da ya sa ta gazawa daga kwankwasonta zuwa ƙasa. A watanni takwas na ciwonta, Shaidu da suke Villa Mercedes ne suka kula da ita da kyau. Sun kula da kome, suna share gidanta kuma suna dafa mata abinci. Ko lokacin da take asibiti ma, kullum akwai wadda take tare da mama, dare da rana.

“Da daɗewa ni da mama mun koma Brazil, kuma tana samun sauƙi. Shaidu da suke a inda muke a yanzu suna iyakacin ƙoƙarinsu su taimaka wa mama a samun sauƙin.”

Marília ta kammala wasiƙarta haka: “Na yarda ni ba Mashaidiya ba ce, amma na sami abokantaka, ƙauna, da kuma kulawa daga Shaidu.”

Gaskiya ne, har ila akwai mutane da suke bin ƙaunar Kirista ta gaskiya. A yin haka, suna nuna yadda ikon koyarwar Yesu take iya shafi rayuwanmu.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba