‘Sulemanu Bai Yi Ado da Ya Kai na Ɗayansu Ba’
IRIN waɗannan furanni ana ganinsu ko’ina a hanyoyi ta kudancin Afirka. Ana kiransu cosmos ana samunsu a yankuna masu zafi na Amirka. Irin waɗannan furanni masu ƙawa za su iya tunasar mana darasi da Yesu ya koyar. Mutane da yawa da suke sauraronsa matalauta ne, suna alhini game da bukatunsu na jiki, abinci da kuma tufafi.
Yesu ya yi tambaya: “Don menene kuma ku ke alhini da zancen tufa? Ku lura da furanni na jeji, girman da su ke yi; ba su yi wahala ba, ba su yi kaɗi ba: duk da haka ina ce muku, ko Sulemanu, da darajarsa duka, ba ya yafa ƙawa kamar guda ɗayansu ba.”—Matta 6:28, 29.
Da akwai ra’ayi dabam dabam game da irin fure na musamman da Yesu yake nufi. Amma Yesu ya ci gaba da kwatanta furen da ganyaye da ke ko’ina, yana cewa: “Idan fa Allah ya kan yi ma ganyayen saura sutura haka, abin da ke rayuwa yau, gobe ana jefawa cikin tanderu, balle ku, ku masu-ƙanƙantar bangaskiya?”—Matta 6:30.
Ko da cosmos ba furen Isra’ila ba ne, suna tokara wa darasi da Yesu yake koyarwa. Ko idan an dube shi daga nesa ko kuma kurkusa, lallai suna da kyau sosai kuma abin da masu ɗaukan hoto da ’yan zane-zane suke fara’arsa ne sosai. Hakika, ba zugugu ne ba da Yesu ya ce, “ko Sulemanu, da darajarsa duka, ba ya yafa ƙawa kamar guda ɗayansu ba.”
Akwai wani darasi ne gare mu a yau? Waɗanda suke bauta wa Allah sun tabbata cewa zai taimake su su samu abin biyan bukata har a lokatan wahala ma. Yesu ya bayyana haka: “Ku biɗi mulkin [Allah], waɗannan abu [su abinci da sutura] kuma za a ƙara muku su.” (Luka 12:31) Babu shakka, akwai fa’idoji na gaske daga biɗan Mulkin Allah. Amma ka san abin da Mulkin Allah yake da kuma abin da zai yi wa mutane? Shaidun Jehovah za su yi farin ciki su taimake ka ka samu amsoshi daga Littafi Mai Tsarki.