Tambayoyi Daga Masu Karatu
Daidai ne a kashe dabba da mowa ce da take ciwo ko kuma ta tsufa?
Yawancin mutane suna ɗaukan dabbobi abin so kuma da ake morewa. Wasu dabbobin gida sukan zama abokai sosai. Alal misali, an san da cewa karnuka suna biyayya kuma suna nuna son ubangidansu. Saboda haka, a kan fahimta irin so da mutane suke wa waɗannan dabbobi, musamman ma idan sun daɗe suna tare na shekaru.
Amma, rayuwar dabbobi da yawa ba ta da tsawo sosai. Karnuka suna iya rayuwa na shekaru 10 zuwa 15, haka ma ƙyanwa, ya dangana da irinsu. Idan sun tsufa, dabbobi suna iya ciwo ko kuma naƙasa da zai sa ubangidansu ɓacin rai idan ya tuna lokacin da dabbar take ƙarama. Daidai ne a ƙarar da wahalar dabbar ta wurin kashe ta?
Kirista zai so ya bi daidai da nufin Allah lokacin da yake bi da dabbobi. Idan ba a bi da su da kyau ba ba zai yi daidai da nufin Allah ba, domin Kalmarsa ta ce: “Mai-adalci yana kula da ran dabbansa.” (Misalai 12:10) Amma, wannan ba ya nufin cewa Allah yana ɗaukan dabbobi yadda yake ɗaukan mutane. Yayin da Allah ya halicci mutane, ya nuna cewa da akwai bambanci sarai tsakaninsu da dabbobi. Alal misali, ya ba mutane begen rai na har abada, amma bai taɓa ambata wannan game da dabbobi ba. (Romawa 6:23; 2 Bitrus 2:12) Domin shi Mahalicci ne, yana da iko ya sa dangantakar da ta dace tsakanin mutane da dabbobi.
Farawa 1:28 ta gaya mana yadda dangantakar nan take. Allah ya gaya wa mutane na farko: “Ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari, da kowane abu mai-rai wanda ke rarrafe a ƙasa.” Haka kuma Zabura 8:6-8 ta ce: “[Allah ya] sa abu duka ƙarƙashin sawayensa [mutum]: Dukan tumaki da shanu, i, har da namomin jeji: Tsuntsayen sama, da kifin teku.”
Allah ya bayyana sarai cewa mutum zai iya amfani da ya dace da dabba ko kuma kashe yadda ya dace. Alal misali, ana iya amfani da fatarsu a yin tufafi. Allah kuma ya ba da izini mutane su ci namansu bayan Rigyawa na zamanin Nuhu, ya daɗa musu abin ci ba ganyaye kawai ba yadda yake a asali.—Farawa 3:21; 4:4; 9:3.
Wannan bai ba da izini a dinga karkashe dabbobi kawai don wasa ba. A Farawa 10:9, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Nimrod da cewa “ƙaƙarfan mai-farauta.” Ayar kuma ta ce hakan ya sa yana “gāban Ubangiji.”
Saboda haka, ko da yake mutum yana da iko bisa dabbobi, ba zai ɓata ikon da aka ba shi ba amma zai yi amfani da shi daidai da ƙa’idodin Kalmar Allah. Wannan zai iya haɗa da kada mutum ya ƙyale dabba ta wahala domin tsufa, lahani, ko kuma ciwo. A irin yanayin nan hakkin Kirista ne ya tsai da abin da zai yi. Idan ya shawarta cewa jinƙai ne kada ya ƙyale dabbar ta ci gaba da wahala da ba za ta warke ba, yana iya sa ta kwanta dama.