Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Taimako a Riƙe Tsarkakar Jini
A DUKAN duniya bayin Jehovah sun nuna aminci ga Allah a batun tsarkakar jini. (Ayukan Manzanni 15:28, 29) Ajin bawa mai aminci mai hikima ya ba da taimako ga ’yan’uwanci na Kirista. (Matta 24:45-47) Bari mu ga sakamakon wannan a Philippines.
Reshen Philippines ya ba da rahoto: “A shekara ta 1990 aka gaya mana cewa wakilai za su zo daga Bethel na Brooklyn su yi taro a nan Philippines. An gayyaci ’yan’uwa daga rassan Asiya, haɗe da Koriya, Taiwan, da kuma Hong Kong. Manufar wannan domin a taimaka a kafa Masu Ba da Bayani Game da Asibitoci da kuma Kwamitin Hulɗa da Asibitoci. Da farko an kafa kwamitocin a manyan birane huɗu a Philippines.” Kwamitocin suna ƙoƙari su nemi likitoci da za su yarda su ba mu haɗin kai game da matsayin Kirista a batun jini. Za su kuma taimaki ’yan’uwa yayin da matsala ta taso game da jini.
An zaɓi Remegio ya zama ɗaya cikin Kwamitin Hulɗa da Asibitoci a Baguio. Bayan ɗan lokacin, likitoci suka soma fahimtar amfanin ayyukan kwamitin. Remegio ya tuna wani lokaci da likitoci da suka sadu da Kwamitin Hulɗa da Asibitoci suka nemi su san yadda za su yi wa Shaidu majiyyata da suka ƙi jini magani. Remegio ya ce: “Likitoci suka soma yin tambayoyi, sai na ga wata tangarɗa ce domin tambayoyin na masana ne.” Ya yi addu’a ga Jehovah domin taimako ya bi da wannan ƙalubale. Remegio ya ci gaba: “Bayan kowacce tambaya, wasu likitoci sai su ɗaga hannu kuma su faɗi yadda suka magance irin wannan yanayi.” Remegio ya yi farin ciki da taimakon, musamman ma domin lokacin tambaya da ba da amsa da aka yi sa’o’i biyu.
Yanzu da akwai kwamitin guda 21 a dukan ƙasar, da ’yan’uwa 77 da suke ciki. Danilo, wani Mashaidi da likita ne, ya ce: “Likitoci sun fahimci cewa Shaidu majiyyata suna da goyon bayan ƙungiya da take kula da su cikin ƙauna.” Wani likita da farko ya yi jinkirin ya yi wa wani ɗan’uwa fiɗa ba tare da amfani da jini ba. Amma, ɗan’uwan ya tsaya tsayin daka. Aka yi fiɗar babu matsala. Masu Ba da Bayani Game da Asibitoci suka ba da rahoto cewa: “Likitan ya yi mamakin yadda ɗan’uwan ya sami sauƙi. Ya ce: ‘Bisa ga abin da ya faru a nan, idan wani cikinku yana bukatar irin wannan fiɗar, zan yi murnan yinsa ba tare da ƙarin jini ba.’ ”