“Na Sami Dukan Abin da Nake Bukata”
AN KIMANTA cewa baƙin ciki, yana shafan mutane fiye da miliyan 120 a duk duniya, in ji rahoto daga Ƙungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya ke nan. Kowacce shekara, mutane miliyan suke kashe kansu, mutane tsakanin miliyan 10 zuwa miliyan 20 suke ƙoƙarin yin haka. Wane taimako za a iya yi wa waɗanda suke baƙin ciki? Magani zai iya kawar da wahalar, amma mafi muhimmanci tallafawa ne ga motsin rai. Ban da haka ma, waɗanda suke da baƙin ciki sun sami ƙarin taimako daga littattafai masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki na Shaidun Jehovah, yadda wasiƙa ta gaban nan daga Faransa ta nuna.
“A kwanan bayan nan, ban ga dalili na ci gaba da rayuwa ba. Na yi wa Allah addu’a ya sa in mutu. Ina ji kamar dai na riga na mutu a ciki. Wajen neman ja-gora, na yi wa Jehovah addu’a. Sai kuma na shawarta na karanta 2002 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, na karance shi cikin kwanaki uku. Hakika, ya ƙarfafa ni kuma ya sa bangaskiyata ta ƙarfafa.
“Na yi bincike cikin Hasumiyar Tsaro da kuma Awake!, na ga abin mamaki! Na karance waɗannan jaridu a kai a kai na shekaru 15, amma ban taɓa tunanin irin ƙarfafa da kuma motsawa da waɗannan talifofi suke da shi ba. Sun cika da ƙauna—inganci da ba a gani a kwanakin nan. Na sami dukan abin da nake bukata.”
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda su ke da ruhu mai-tuba.” (Zabura 34:18) Babu shakka, dukan waɗanda suke da “karyayyar zuciya” ko kuma “ruhu mai-tuba” za su iya samun ƙarfafa da bege na nan gaba cikin Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehovah suna rarraba littattafai masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki domin taimakon waɗanda suke amfana daga hurarren tushen ta’aziyyar nan.