Sahihanci Kawai Ake Bukata a Faranta wa Allah Rai?
ANA BUKATAR sahihanci kuwa a rayuwarmu ta yau da kullum? Sahihanci rashin maguɗi ne ko ha’inci; yin gaskiya; rashin yaudara; inganci. Hakika, wannan hali yana da amfani wajen ƙarfafa abota da wasu. Manzo Bulus ya yi gargaɗi: “Ku bayi, cikin abu duka ku yi biyayya da waɗanda su ke iyayengijinku bisa ga tabi’ar jiki; ba da bautar ganin ido ba, kamar masu-gamin mutane, amma da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.” (Kolossiyawa 3:22) Waye ba zai yi farin ciki ba ya sami irin wannan mutum yana masa aiki? A yau, mutane masu gaskiya su ke da zarafin samun aiki da kuma kasancewa a bakin aikinsu.
Abin da ya sa sahihanci ya kasance abin da ake bukata ma domin yadda yake shafar dangantakarmu da Allah ne. Isra’ilawa na dā sukan more albarkar Allah sa’ad da suka kiyaye dokokin da kuma bukukuwa. Sa’ad da yake magana game da tsabta ta ikilisiya, Bulus ya aririci Kiristoci: “Mu fa, bari mu yi idinmu, ba tare da tsohon [yisti] ba, ba kuwa da [yisti] na ƙeta da na mugunta ba, amma da gurasa marar-[yisti] ta sahihanci da ta gaskiya.” (1 Korinthiyawa 5:8) Domin Allah ya karɓi bautarmu, sahihanci ba ana bukatarsa ba ne kawai amma ya zama wajibi. Duk da haka, ka lura cewa sahihanci kawai ba shi ke nan ba. Dole ne ya bi gaskiya.
Magina jirgin ruwan nan Titanic da kuma fasinjojinta wataƙila sun yi imani cewa jirgin ba mai nitsewa ba ne. Amma a tashinsa na farko a shekara ta 1912, ya yi karo da ƙanƙara mutane 1,517 suka rasa rayukansu. Wasu Yahudawa na ƙarni na farko wataƙila sun yi imani da gaske da hanyar da suke bauta wa Allah, amma, himmarsu “ba bisa ga sani ba” ce. (Romawa 10:2) Domin Allah ya amince da mu, imaninmu dole ne ya kasance bisa cikakken sani. Shaidun Jehovah a yankinku za su taimaka maka ka bincika abin da bauta wa Allah da sahihanci da gaskiya ya ƙunsa.