Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 8/1 p. 32
  • Darasi Daga Shamuwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darasi Daga Shamuwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 8/1 p. 32

Darasi Daga Shamuwa

‘I,KO SHAMUWA cikin sama tana sane da kwanakinta . . . Amma mutanena ba su san shari’ar Ubangiji ba.’ (Irmiya 8:7) Da waɗannan kalmomi, annabi Irmiya ya sanar da hukuncin Jehovah a kan mutanen Yahuda da suka yi ridda, waɗanda suka bar Jehovah Allahnsu suka juya ga bauta wa baƙaƙen alloli. (Irmiya 7:18, 31) Me ya sa Irmiya ya zaɓi shamuwa ya ba da darasi ga Yahudawa marasa aminci?

Ga Isra’ilawa, shamuwa tsuntsuwa ce da aka san ta da ƙaura ta tsakanin ƙasashe na Littafi Mai Tsarki. Sunan Ibrananci na wannan babbar tsuntsuwa mai doguwar ƙafa, na nufin “aminiya; mai ƙauna ta alheri.” Wannan ya dace, domin ba kamar yawancin tsuntsaye ba, shamuwa namiji da tamace na kasancewa tare duk rayuwarsu. Bayan sun je wurare masu ɗumi lokacin sanyi, yawancinsu suna dawowa kowacce shekara, sau da yawa suna komawa ga sheƙarsu ta dā.

Halin shamuwa kwatanci ne na aminci a wasu hanyoyi na ban mamaki. Namijin da tamacen duka suna saka hannu wajen ɗuma ƙwansu da kuma ciyar da ’yan tsaki. Littafin Our Magnificent Wildlife ya yi bayani: “Shamuwa masu ’ya’ya suna nuna aminci sosai ga juna. Shamuwa namiji a Jamus ya tashi sama har ya shiga wayar wutar lantarki kuma wayar ta kashe shi. Abokiyar zamansa ta ci gaba da ɗuma ƙwanta ita kaɗai na kwana 3, sai ta bar sheƙarsu sau ɗaya kawai na ɗan lokaci don ta nemi abinci. . . . Wani lokaci kuma, sa’ad da aka kashe shamuwa tamace, baban ya yi renon ’yan tsakin.”

Hakika, ta wajen nuna aminci ga abokiyar zama da kula da ’yan tsaki, shamuwa na rayuwa daidai da ma’anar sunanta—“aminiya.” Da haka, shamuwa misali ne da ya dace ga Isra’ilawa masu taurin kai marasa aminci.

Ga mutane da yawa a yau, aminci, ra’ayin dā ne—abu mai kyau amma ba ya yiwuwa. Kisan aure da ke ƙaruwa, yasarwa, cin kuɗi da wasu irin ha’inci sun nuna cewa ba a daraja amana kuma. Akasin haka, Littafi Mai Tsarki na daraja amana da ƙauna da kuma alheri suka motsa. Ya aririci Kiristoci su “yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Afisawa 4:24) Hakika, sabon mutum na taimaka mana mu kasance da aminci, amma kuma za mu koyi darasi game da aminci daga shamuwa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba