Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
‘Maganar Allah Tana Aikatawa’
ATSIBIRIN Caribbean na Jamaica, yawancin mutane sun saba da Littafi Mai Tsarki. Ana samun fassarar King James Version, a kusan kowanne gida, kuma wasu mutane sun sani cewa “maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.” (Ibraniyawa 4:12) Wannan aikin yana sake rayuka, kamar yadda ya faru a labari na gaba.
Wani mutum, sunansa Cleveland ya dawo ke nan daga wajen aiki sai wani Mashaidin Jehovah ya ziyarce shi. Bayan ya tattauna wasu Nassosi da shi, Mashaidin ya bar masa abin koyon Littafi Mai Tsarki, littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Cleveland bai san yadda Kalmar Allah za ta yi aiki a rayuwarsa ba.
Da ma Cleveland yana addu’a sau uku kowacce rana, yana roƙon Allah ya taimake shi ya sami hanyar da ta dace ya bauta Masa. Cleveland ya tabbata cewa iyayensa ba su yi bauta a hanyar da ta dace ba, amma bayan ya bincika wasu addinai, bai gamsu ba. Ko da yake ya taɓa ji game da Shaidun Jehovah, yana shakkar ko suna da gaskiya. Duk da shakkarsa, Cleveland ya yarda Mashaidin da ya zo gidansa ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Menene dalilinsa? Domin ya tabbatar wa Shaidun cewa addininsu ba gaskiya ba ne!
Ba da daɗewa ba Cleveland ya fahimci cewa nasabarsa da mata biyu ba ta gamsar da Allah. (1 Korinthiyawa 6:9, 10) Bayan nazari sau biyu kawai ya tsai da shawarar ya daina sha’ani da matan. Ya soma halartan taron Kirista a Majami’ar Mulki. Amma wannan ya zama wani gwaji.
Cleveland ya shaƙu sosai cikin rukunin ƙwallon ƙafa na ƙauyen, kuma lokacin wasan yana saɓawa da na halartan taro. Me zai yi? Duk da matsi ƙwarai daga abokan wasan, shugaban, da kuma abokai, Cleveland ya tsai da shawarar ya daina buga ƙwallon. Hakika, Kalmar Allah ta soma aiki, ta motsa shi domin amfaninsa!
Aikin Kalmar Allah ya bayyana kuma a lokacin da Cleveland ya soma gaya wa wasu game da Littafi Mai Tsarki. (Ayukan Manzanni 1:8) Saboda wannan, biyu cikin abokansa na wasan ƙwallon suka soma halartan taron Shaidun Jehovah. Bayan da Cleveland ya ƙware ya zama mai shelar bishara, ya sami farin ciki ƙwarai cikin hidimar, yana amfani da Kalmar Allah ya taimaki wasu.
Domin yadda Kalmar Allah ta motsa shi, Cleveland a ƙarshe ya keɓe kansa ga Jehovah ta wurin baftisma cikin ruwa kuma ya samu gatar hidima ta cikakken lokaci, yana hidimar bawa mai hidima a ikilisiyarsu.
A Jamaica da kuma a duniya baki ɗaya, dubban mutane sun fahimci cewa Kalmar Allah da gaske, “mai-rai ce, mai-aikatawa.”
[Map/Hoto a shafi na 3]
J A M A I C A
[Inda aka Dauko]
Taswira da duniya : Mountain High Maps® Copyright © 1997 Digital Wisdom, Inc.