Yadda Ɗa Ya Taimaki Ubansa
JAMES, daga Ingila, a farkon shekarunsa na 30, yana da taɓin hankali mai tsanani. Duk da haka, ya halarci taron Shaidun Jehovah na shekaru da yawa da mamarsa da kuma yarsa. Amma, babansa bai taɓa nuna yana son imaninsu ba. Da wani maraice bayan taro da ya nuna yadda za a gayyaci idon sani zuwa Bikin Tuna mutuwar Kristi, James ya hanzarta ya shiga ɗakinsa. Cikin damuwa, mamarsa ta bi shi kuma ta same shi yana bincike tsofaffin jaridun Hasumiyar Tsaro da kuma Awake!. Ya zaɓi ɗaya da ke da hoton Bikin Tunin a shafi na baya ya ruga zuwa wurin babansa. Ya nuna hoton da fari sai ya nuna wa babansa ya ce “Kai!” Mamarsa da babansa suka dubi juna cikin mamaki da suka fahimci cewa James yana gayyatar babansa ne zuwa Bikin Abin Tuni. Baban ya ce wataƙila zai halarta.
A maraicen Bikin Abin Tunin, James ya je cikin akwatin babansa, ya zaɓi wando, ya kai wa babansa, ya yi alamar cewa babansa ya sa. Baban ya ce ba zai tafi taron ba. Saboda haka, James da mamarsa suka kama hanya zuwa Majami’ar Mulki su kaɗai.
Amma daga baya, James ba ya ba da haɗin kai sa’ad da mamarsa take ƙoƙari ta sa ya shirya don ya halarci taron ikilisiya, ya gwammace ya zauna a gida da babansa. Wata Lahadi da safe, James ya sake ƙin ya bi mamarsa da take ƙoƙarin ta sa ya shirya ya je taro. Ga mamakinta, baban James ya juya wajensa ya ce: “James, idan na tafi taro yau, kai ma za ka je?” James ya yi murna. Ya rungumi babansa ya ce “E!” sai dukansu uku suka kama hanya zuwa Majami’ar Mulki.
Daga wannan ranar, baban James ya ci gaba da halartar dukan taron ranar Lahadi, ba da daɗewa ba ya ce idan yana so ya ci gaba, to dole ne ya halarci wasu taron ma. (Ibraniyawa 10:24, 25) Kuma hakan ya yi, bayan wata biyu ya fara nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai. Ya samu ci gaba da hanzari, ya yi canje-canje da ake bukata a rayuwarsa, kuma bai daɗe ba ya fara wa’azin Mulki. Shekara ɗaya bayan ya fara nazarin Littafi Mai Tsarki, ya keɓe kansa ga Jehovah kuma ya nuna hakan ta wajen nitsarwa cikin ruwa. A yanzu yana hidima ta bawa mai hidima a ikilisiyarsa. Yanzu duka a cikin iyalin suna bauta wa Jehovah cikin haɗin kai.