Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 4/1 p. 32
  • Tsufa Ba ta Hana Koyo

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tsufa Ba ta Hana Koyo
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 4/1 p. 32

Tsufa Ba ta Hana Koyo

KSENIYA an haife ta a shekara ta 1897. Tana da ’ya’ya mata uku, ɗa, jikoki 15, da kuma tattaɓa-kunnuwa 25. A dukan rayuwarta ta yi abin da iyayenta suka koya mata. Ko da yake ta zo Moscow tana gudun hijira daga Jamhuriyar Abkhaz da yaƙi ya ragargaza, wadda ke tsakanin Baƙin Teku da kuma Caucasus, ta gamsu da rayuwarta, musamman abin da ta kira imanin da ta gada.

A shekara ta 1993, ’yar Kseniya, Meri, ta zama Mashaidiyar Jehovah. Meri ta fara gaya wa Kseniya game da Jehovah Allah da kuma Littafi Mai Tsarki, amma ba ta son ta saurara. Kseniya tana ta gaya wa ’yarta, “Na makara na koyi wani sabon abu.”

Duk da haka, ’yarta Meri; matar jikarta, Londa; da kuma tattaɓa-kunnuwanta Nana da Zaza, waɗanda dukansu sun zama Shaidun Jehovah, suka ci gaba da yi mata magana game da Littafi Mai Tsarki. A wani maraice a shekara ta 1999, suka karanta wa Kseniya wani nassi da ya motsa zuciyarta. Kalmomi masu motsawa ne na Yesu ga manzanninsa masu aminci lokacin da yake kafa Abincin Maraice na Ubangiji. (Luka 22:19, 20) A shekararta 102, Kseniya ta yanke shawara, a maraicen za ta fara nazarin Littafi Mai Tsarki.

“Bayan rayuwa ta shekara 102,” in ji Kseniya, “na fahimci ma’anar rayuwa. Yanzu na gane cewa babu abin da ya fi kyau da bauta wa Allahnmu mai girma, mai ƙauna, Jehovah. Ina cike da ƙarfi da kuma isashiyar lafiya. Ina karatu ba tare da madubi ba kuma ina tarayya sosai da iyalina.”

A ranar 5 ga Nuwamba, 2000, aka yi wa Kseniya baftisma. Ta ce: “Yanzu na ba da raina ga Jehovah in bauta masa cikin ƙauna. Ina ba da jaridu da warƙoƙi yayin da nake zama a kusa da tashar safa safa kusa da gidana. Dangi sukan zo ziyara, da farin ciki kuwa ina gaya musu gaskiya game da Jehovah.”

Kseniya tana saurarar ranar da ‘naman jikinta zai zama kamar a ƙuruciya, kuma ta sake samun ƙarfinta na matashiya.’ (Ayuba 33:25) Idan wadda ta wuce ƙarni guda ba ta ga ta tsufa ba ta koyi game da ma’anar rai cikin Littafi Mai Tsarki, kai fa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba