Ya Kamata Imani Ya Kasance Bisa Hujja Ne?
“Akwai ‘mutane masu imani’ da yawa da suke yin addini don kawai ba sa so su yi tunani,” in ji wani shugaban makarantar tauhidi a Amirka. Ya daɗa cewa, “suna so ne kawai su yi na’am da kome game da ‘imani.’ ”
DAMUWAR ita ce yawancin mutane da suke da’awar suna da imani ba sa tunanin hujjar da ta sa suka yi imani da abin da suka yi, ko da hujjar wannan imaninsu ne. Abin da ya sa ke nan addini ya zama abin da mutane da yawa suke jinkirin maganarsa.
Abin baƙin ciki kuwa, irin waɗannan ayyuka na yin amfani da siffofi da addu’o’i da ake maimaitawa suna hana yin tunanin kirki. Waɗannan ayyuka, haɗe da manyan gine-gine, tagogi masu gilas masu launi da aka yi amfani da su, da kuma kaɗe-kaɗe, sune abubuwa da miliyoyin mutane suka sani cikin addininsu. Ko da yake wasu coci suna da’awar cewa imaninsu bisa Littafi Mai Tsarki ne, saƙonsu na ka ‘gaskata da Yesu, za ka tsira’ yana rage darajar yin nazarin Littafi Mai Tsarki da gaske. Wasu sun juya ga wa’azin bisharar gamsar da jama’a ko kuma na siyasa. Menene sakamakon dukan waɗannan?
Game da yanayin a Amirka ta Arewa, wani marubuci na addini ya ce: “Kiristanci . . . ya zama abin yi ne sama sama, [kuma] masu yinsa ba su da isashen ilimi game da imanin.” Har wani mai bincike ya kai ga kwatanta Amirka da cewa “al’umma ce da take cike da jahilan Littafi Mai Tsarki.” A ƙashin gaskiya, waɗannan abubuwan da aka lura za su iya zama daidai a wasu ƙasashen da wai ƙasashen Kiristoci ne. Addinai da yawa da ba Kiristoci ba ma ba sa ba da zarafin yin tunani, suna nanata waƙe-waƙe, maimaita addu’o’i, da kuma wasu bimbini dabam dabam da suka ƙunshi wawan tunani, maimakon tunani na haziƙanci, mai kyau.
Duk da haka, a rayuwarsu ta yau da kullum, mutanen ne da ba sa tunani a kan gaskiya da kuma daidaitan imani na addininsu sau da yawa sukan bincika wasu abubuwa na ƙwarai. Ba ka mamaki ne cewa mutumin da yake bincike ƙwarai domin kawai ya sayi mota—wadda wata rana za ta ƙarasa a bola—zai ce game da addininsa, ‘Idan yana da kyau ga iyaye na, yana da kyau a gare ni’?
Idan da gaske muna son mu faranta wa Allah rai, bai dace ba mu bincika sosai gaskiyar abin da muka gaskata game da shi? Manzo Bulus ya faɗa game da wasu mutane masu bin addini a zamaninsa, da suke da “himma domin Allah, amma ba bisa ga sani ba.” (Romawa 10:2) Za a iya gwada irin waɗannan da wani mai aikin shafa fenti da yake aiki tuƙuru ya shafa wa wani gida fenti amma ya yi amfani da launi da bai dace ba domin bai saurari abin da mai gidan ya faɗa ba. Wataƙila mai fentin zai yi farin ciki da aikinsa, amma mai gidan zai gamsu da aikin kuwa?
Menene ke gamsar da Allah game da bauta ta gaskiya? Littafi Mai Tsarki ya amsa: “Wannan mai-kyau ne, abin karɓa kuwa ga Allah Mai-cetonmu. Shi wanda ya ke nufi dukan [iri-irin] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Timothawus 2:3, 4) Wasu suna jin ba za a iya samun irin sanin nan ba a addinai masu yawa na yau. Amma ka yi tunani—idan nufin Allah ne cewa mutane su samu cikakken sanin gaskiya, zai ɓoye ta daga gare su ne? Ba daidai ba ne da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, da ya ce: “Idan ka biɗe [Allah], yā samu gareka.”—1 Labarbaru 28:9.
Yaya Allah yake sa waɗanda suke biɗansa da gaske su san shi? Talifi na gaba zai ba da amsa.