Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 11/1 p. 19
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Makamantan Littattafai
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Darussa Daga Littafin Ayuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 11/1 p. 19

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Yaya ne tsawon lokacin da Ayuba ya sha wahala?

Wasu mutane suna tunani cewa jarabbobin Ayuba ya kai shekaru da yawa, amma littafin Ayuba bai nuna cewa wannan wahalar ta dogon lokaci ba ne.

Somi na jarabobbin Ayuba, halakar ’ya’yansa da kayayyaki, ya bayyana kamar a ɗan lokaci ne. Mu karanta: “Wata rana fa ’ya’yan [Ayuba] maza da mata suna ci suna shan ruwan anab a cikin gidan wansu.” Ayuba ya sami labari bi da bi cewa ya yi hasarar—shanunsa, jakansa, tumakinsa, raƙumansa, da bayi da suke kula da su. Babu shakka, bayan haka Ayuba ya ji mutuwar ’ya’yansa maza da mata, da suke “ci suna shan ruwan anab a cikin gidan wansu.” Kamar dai dukan wannan sun faru ne rana ɗaya.—Ayuba 1:13-19.

Sashe na biye na jarabobbin Ayuba ya fi ɗaukan lokaci. Shaiɗan ya je wurin Jehovah kuma yi da’awa cewa Ayuba zai saɓa idan wahalar ta taɓa shi—jikinsa. Sai aka harɓi Ayuba da “gyambuna masu-ciwo, tun daga tāfin sawunsa har kan kansa.” Ƙila ya ɗan ɗauki lokaci kafin ciwon ya bazu a dukan jikinsa. Kuma mai yiwuwa ya ɗauki lokaci kafin labarin “dukan masifan nan” ya kai waɗanda wai su masu ta’aziyya ne, da suka zo wurinsa.—Ayuba 2:3-11.

Eliphaz ya zo daga Teman a ƙasar Edom, kuma Zophar daga wajajen arewa maso yammacin Arabiya, saboda haka garinsu ba shi da nisa da na Ayuba a Uz, wanda wataƙila a arewacin Arabiya ne. Amma Bildad Bashuhi ne, kuma an fahimci cewa mutanensa na zama a bakin kogin Euphrate. Idan Bildad yana garinsu a lokacin, to, mai yiwuwa ya ɗauki makonni ko watanni kafin ya ji yanayin Ayuba kuma ya yi tafiya zuwa Uz. Amma, yana yiwuwa cewa dukan mutane uku suna garin su Ayuba lokacin da wahalarsa ta soma. Ko yaya dai, lokacin da abokanan Ayuba uku suka iso, “tare da shi fa suka zauna a ƙasa har kwana bakwai, dare da rana” ba su ko ce uffan ba.—Ayuba 2:12, 13.

Sai ya zo sashe na ƙarshe na jarabobbin Ayuba, labarin da ya cika surori da yawa na littafin. An yi mahawara ko maganganu da yawa na waɗancan da wai su masu ta’aziyya ne, sau da yawa kuma Ayuba yana amsawa. Bayan wannan ya ƙare, saurayi Elihu ya yi horo, kuma Jehovah ya yi wa Ayuba gyara daga sama.—Ayuba 32:1-6; 38:1; 40:1-6; 42:1.

Saboda haka, wahalar Ayuba da zartarwar mai yiwuwa sun auku cikin watanni kaɗan, wataƙila shekara guda babu kaɗan. Mai yiwuwa ka sani daga abin da ya same ka cewa jarabobbi masu wuya sukan zama kamar sun daɗe sosai. Duk da haka, kada ka manta cewa suna ƙarewa, yadda na Ayuba ya ƙare. Ko yaya jarabobbi da muke fuskanta suka daɗe, bari mu tuna da taimakon Allah, yadda huraren kalmomi suka nuna: “Ƙuncinmu mai-sauƙi, wanda ke na lokaci kaɗan, yana aika dominmu nauyin daraja madawwami gaba gaba ƙwarai.” (2 Korinthiyawa 4:17) Manzo Bitrus ya rubuta: “Allah kuwa na alheri duka, wanda ya kiraye ku zuwa cikin madawwamiyar darajatasa cikin Kristi, bayan da kun sha wuya ’yan kwanaki, da kansa za ya kammala ku, shi kafa ku, shi ƙarfafa ku kuma.”—1 Bitrus 5:10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba