Nazarin Littafi Mai Tsarki—Yana Da Wani Amfani A Gare Ka Kuwa?
“KADA a karanta idan ba a gaban firist ba.” Wannan gargaɗin ya bayyana a shafin farko na wasu Littafi Mai Tsarki da ’yan Katolika suke da shi. “Mu Katolikawa ba a ba mu damar karatun Littafi Mai Tsarki ba,” in ji Kay Murdy na Makarantar Littafi Mai Tsarki na Katolika a Los Angeles, “amma wannan yana canjawa.” Da zarar Katolikawa sun fahimci cewa Nassosi Masu Tsarki za su shafi rayuwarsu, ta lura da cewa, “sai su koyi jin yunwa da kishin Littafi Mai Tsarki da kansu.”
Game da wannan canjin, jaridar U.S. Catholic ta ɗauko abin da wani mai gudanar da ilimantarwa na addini wanda ya ce wai Katolikawa waɗanda suka shiga ajujuwan nazarin Littafi Mai Tsarki suna jin “an hana su Katolikawa, kuma da akwai arziki da yawa cikin Littafi Mai Tsarki. Suna so su samu arziki da yawa da suke jin sun yi rashinsa.”
Ko yaya dai, wane “arziki” ne ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai samu? Ka yi la’akari: Za ka so ka san yadda za ka bi da damuwa na rayuwar yau da kullum? Ta yaya za ka samu zaman lafiya a cikin iyali? Menene dalilin da ya sa ake mugayen halaye da kuma waɗanda jama’a suka ƙi? Menene abin da yake haddasa nuna ƙarfi a tsakanin matasa a yau? Tabbatattun amsoshi ga waɗannan da kuma wasu tambayoyi masu ba da mamaki za a same su cikin Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, kuma za su kasance “arziki” ne da gaske, ba kawai ga Katolikawa da ’yan Farostatan ba amma kuma ga ’yan Buddha, ’yan Hindu, Musulmai, ’yan Shinto, har da masu musun wanzuwar Allah, da ’yan mulhidi. Kamar yadda mai Zabura ya ce, ‘Kalmar Allah fitila ce ga sawayensa, haske ne ga tafarkinsa.’ Zai kasance haka nan a gareka.—Zabura 119:105.