Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 5/1 p. 3
  • Yadda Gwauranci Ya Shafi Wasu Mata Biyu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Gwauranci Ya Shafi Wasu Mata Biyu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Makamantan Littattafai
  • Kyauta wa Karnukana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Taimaka Wa Gwauraye Mata Cikin Gwadawarsu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • “Waɗanda Aka Ƙadara” Suna Sauraron Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • How Can I Live With My Grief?
    Yayin da Wani Wanda Ka ke Ƙauna Ya Mutu
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 5/1 p. 3

Yadda Gwauranci Ya Shafi Wasu Mata Biyu

SANDRA gwauruwa ce da take da zama a Australiya. Lokacin da maigidanta ya mutu wasu shekarun baya, mutuwar ta sa Sandra ta gigita ƙwarai. “Fahimtar cewa na yi rashin abokin aurena da kuma abokina na kud da kud ya rufe ni. Ban iya tuna yadda na dawo gida ba a lokacin daga asibiti ko kuma abin da na yi a ranar gabaki ɗaya. A makonni da suka biyo baya, tsoron da nake ji ya zama mini ciwon jiki.”

Sandra tana da wata abuyarta da ta girme ta, Elaine, wadda ita gwauruwa ce na shekara shida. Elaine ta yi jinyar maigidanta, David, na wata shida kafin ya mutu daga ciwon daji. Ta yi baƙin ciki sosai har da ba da daɗewa ba bayan mutuwar maigidanta, ta makance na ɗan lokaci. Shekara biyu bayan haka ta fāɗi kawai wata rana a cikin jama’a. Likitanta bai ga wani alamun ciwo ba a jikinta. Amma, ya gano cewa Elaine ba ta fid da baƙin cikinta ba, saboda haka ya shawarce ta ta je gida ta yi ƙoƙari ta yi kuka. Ta ce: “Ya ɗauki lokaci kafin na jure wa baƙin cikina,” ta daɗa cewa lokacin da ta kaɗaita, “sai na shiga cikin ɗaki na rufa fuskata da tufafin David.”

Hakika, mutuwar ƙaunacaccen abokin aure takan jawo damuwa dabam dabam, domin gwauranci ya ƙunshi fiye da zama babu miji kawai. Alal misali, Sandra da daɗewa ba ta jin daidai take kamar dā ba. Kamar wasu gwauraye mata na baya bayan nan, ita ma ta damu, babu kwanciyar rai. Sandra ta tuna: “Domin maigidana ne yake tsai da shawara na saba da wannan, farat ɗaya gashi ya ƙyale ni da tsai da shawarwari. Barcina babu daɗi. Nakan ji gajiya ƙwarai. Ba na sanin ma abin da ya kamata na yi.”

Kullum muna jin labarai irin na Sandra da Elaine a dukan duniya. Ciwo, haɗari, yaƙe-yaƙe, sharan ƙabila, da kuma nuna ƙarfi suna sa a sami ƙarin gwauraye.a Yawanci waɗannan mata suna wahala ba sa furta damuwarsu, domin ba su san na yi ba. Menene abokai da dangi za su yi domin su taimaka wa waɗanda suke ƙoƙari a zaman gwauranci? Talifi na biye yana da wasu shawarwari da za su iya taimakawa.

[Hasiya]

a Wasu mata suna cikin yanayi mai kama da na gwauraye domin mazansu sun bar su. Ko da yake yaji a aure da kisan aure suna da nasu matsaloli, da yawa cikin ƙa’idodin da za a tattauna cikin talifi na biye zai iya taimaka wa mata da suke cikin irin waɗannan yanayi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba