Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 11/1 p. 32
  • Zaman Lafiya ta Duniya Ta Yaya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Zaman Lafiya ta Duniya Ta Yaya?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 11/1 p. 32

Zaman Lafiya ta Duniya Ta Yaya?

AN KUSA a samu zaman lafiya ne? Wasu sun yi tunanin haka dā amma yanzu suna shakka. In ji wani rahoto da yake tattauna kaluɓale da za mu fuskanta a nan gaba, wanda aka buga a cikin jaridar Daily Mail & Guardian na Afirka ta Kudu, “abin da aka faɗa game da sabon yanayi na ƙasashe duka shekaru 10 kawai da suka shige, yanzu kamar dai ba yadda za a yi ya kasance.”

Marubucin ya nuna begen da ya kasance ne shekaru 10 kawai da suka shige. Yaƙin Wutar Ƙaiƙayi yanzu ya ƙare, kuma babu kokawa don ɗaukaka tsakanin masu iko na duniya. Abin da ya kasance kamar wayewar sabon zamani, da yawa sun yi zaton cewa ’yan Adam za su samu ci gaba wajen magance talauci, cututtuka, da kuma batutuwan mahalli. “Wannan abin da aka faɗa yanzu ya zama kamar mafarki ne kawai,” in ji rahoton. “Sababbin hargitsi sun ɓarke a wajajjen da ba a sani ba; talauci ya ci gaba da ƙaruwa. Da akwai masu iko da makaman nukiliya guda biyu. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɓata sunanta ta wajen kasa magance tarzomar ’yan Adam a kai a kai. Yanayin yana matsawa daga abin da aka yi mafarkinsa kawai zuwa mafarkin wajen zama mai ban tsoro.”

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun san cewa ƙoƙarin mutane ko yaya kyansa, ba zai taɓa yin nasara ba. Me ya sa? Domin, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, “duniya duka kuwa tana hannun Mugun.” (1 Yahaya 5:19) Yayin da take ƙarƙashin ikon Shaiɗan, ba za a iya mai da duniya ta zama da yanayi na Aljanna ba kamar yadda Allah ya halicce ta ta zama.

Duk da haka, akwai dalilin yin bege. Jehovah Allah ya yi alkawarin kawo zaman lafiya a duniya, ba ta wajen yin facin wannan tsarin abubuwa ba, amma ta wajen kawo “sabuwar duniya” in da “adalci zai yi zamansa.” (2 Bitrus 3:13) Hakika, ta wajen Mulkin Allah, duniyarmu za a juya ta ta zama da zaman lafiya, gida mai farin ciki, inda rayuwa da ayyuka za su zama abin murna kullum ga dukan mutane masu biyayya. Ƙari ga haka, Allah ya yi alkawari “zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.” Waɗannan alkawura ba a kafa su a kan abin da mutane suka faɗa ba wanda babu tushe. Maimakon haka, suna bisa Maganar Mahalicci ce wadda ba ta da kure, wanda ba ya ƙarya.—Wahayin Yahaya 21:4; Titus 1:2.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba