Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Waɗanda Suke Ƙaunar Jehovah Suna da Tamani a Gare Shi
LEBANON an san da ita tun lokacin mutanen Littafi Mai Tsarki domin dunbin arzikin ƙasarta. (Zabura 72:16; Ishaya 60:13) Musamman wanda ya fi daraja itatuwanta masu kyau na al’ul, da ake bukata sosai domin gine-gine saboda kyaunsu, ƙamshinsu, da kuma jurewarsu. A ƙarni na farko, wani abu mafi tamani ya fito daga Lebanon. Lingilar Markus ta ba da rahoto cewa daga Taya da Sidon, da suke yankunan Lebanon ta dā, “babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da [Yesu] yake yi.”—Markus 3:8.
Haka ma a yau, Lebanon ta ci gaba da ba da amfani da suke da tamani a idanun Jehovah. Labarin da yake gaba ya nuna haka.
• An ce wani matashi Mashaidi mai suna Wissam ya ba da jawabi na minti 30 a ajinsa a makaranta. Wissam ya yi shawara cewa wannan zai zama zarafi ne mai kyau ya yi wa’azi. Sai ya yi amfani da littafin nan Life—How Did It Get Here? By Evolution or by Creation? ya shirya jawabi a kan batun halitta. Da ya ga abin da ya shirya, malamin Wissam ya ce tun da yake batu ne mai muhimmanci, ya ce Wissam zai iya jan jawabinsa zuwa minti 45.
Da Wissam ya fara jawabinsa, sai malamin ya dakatar da shi ya aika a kira shugabar makarantar. Ba da daɗewa ba sai shugabar ta iso, Wissam ya fara jawabin kuma. Da ta ji tambayoyi da Wissam ya yi na gabatar da jawabinsa, shugabar ta ji daɗi ta ce kowane ɗalibi ya karɓi falle guda na jawabin.
Daga baya wani malami, da yake shigewa, ya lura da murna da ake yi a cikin ajin ya yi tambaya menene yake faruwa. Da aka gaya masa, sai ya sake tambaya me Wissam yake so ya ba da tabbaci a kai, halitta ko kuma ra’i na bayyanau. “Halitta,” aka amsa. Da ya fahimci cewa Wissam Mashaidin Jehovah ne, sai malamin ya ce wa ajin: “Kun ga daga jawabinsa kimiyya tana goyon bayan halitta ne ba ra’i na bayyanau ba.”
Ya kasance cewa wannan malamin yana da littafin nan Creation kuma yana amfani da shi wajen yin lacca a jami’a! Kafin ya tafi, ya yi tambaya ko zai iya zuwa da ɗalibansa washegari don Wissam ya yi wa ajinsa jawabi. Wannan ma ya kasance wani zarafi ne mai kyau na yin wa’azi game da Jehovah.
• Nina ’yar shekara 22 tana ƙishin ruwan gaskiya. Wata rana ɗan babarta ya ba ta Littafi Mai Tsarki kuma ya gabatar da ita ga cocin Pentecostal. Nina tana karatun Littafi Mai Tsarki da farin ciki kuma daga karatunta ta koyi cewa ya kamata Kiristoci su yi wa’azi, saboda haka sai ta fara yi wa idon sani wa’azi. Duk wanda ta yi wa wa’azi sai ya tambaye ta: “Ke Mashaidiyar Jehovah ce?” Hakan ya ba ta mamaki.
Bayan shekara shida, Shaidun Jehovah suka zo gidansu Nina suka faɗa mata game da Mulkin Allah. Da farko ba ta yarda da abin da suke koyarwa ba. Amma, ta ga amsoshinsu daidai ne kuma daga Littafi Mai Tsarki.
Abin da Nina ta koya daga ƙarshe—sunan Allah, Jehovah; albarkar Mulkin, da kuma wasu abubuwa—sun huɗubantar da ita cewa ta sami gaskiya. Ta keɓe kanta ga Allah kuma ta yi baftisma. Nina tana hidima ta cikakken lokaci na shekara bakwai ke nan da suka shige. Hakika, Jehovah yana ba da albarka ga waɗanda suke ƙaunarsa da gaske.—1 Korantiyawa 2:9.