Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Kai wa ga Sanin Allah Mai Ƙauna
ASHEKARARSA ta 16, Antônio ɗan Brazil rayuwa ta ishe shi. Jin ba shi da amfani ya kai shi ga shan miyagun ƙwayoyi da kuma yin maye. Sau da yawa ya yi tunanin zai kashe kansa. A cikin wannan yanayin ne ya tuna da abin da uwarsa ta gaya masa: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Amma a ina wannan Allah mai ƙauna yake?
A ƙoƙarin ya farfaɗo daga shaye shayensa, Antônio ya nemi taimako daga wajen firist na coci. Ko da yake Antônio ya zama mai ƙwazo sosai a Cocin Katolika, har ila yana da tambayoyi da yawa. Alal misali, kalmomin Yesu, “ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda ku” sun rikita shi. (Yohanna 8:32) Wane irin ’yanci Yesu ya yi alkawarinsa? Coci sun kasa ba da takamaiman amsa ga wannan tambayar. A ƙarshe, Antônio ya bauɗe ya sake komawa halinsa na dā. Abin taƙaici, shaye shayensa ya yi tsanani.
A wannan lokacin, matar Antônio, Maria, ta fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da Shaidun Jehovah. Ko da yake bai hana ta nazari ba, Antônio bai ba su hankali ba don yana ganin Shaidu “addinin Amirka ne waɗanda suke yi wa gwamnatin Amirka aiki.”
Maria ta bar Hasumiyar Tsaro da kuma Awake! da suke magana a kan wasu abubuwa da take tsammanin Antônio zai so a cikin gida. Tun da Antônio yana son karatu, wani lokaci yana karanta jaridun idan matarsa ba ta wajen. Lokaci na farko ke nan da ya sami amsoshin tambayoyinsa na Littafi Mai-Tsarki. “Na fara ganin ƙauna da kirki da matata da Shaidun suke nuna mini,” in ji shi.
A tsakiyar 1992, Antônio ya shawarta cewa shi ma zai so ya yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da Shaidun Jehovah. Duk da haka, ya ci gaba da shan miyagun ƙwayoyi da giya. Wata rana da suke komowa daga unguwar ’yan iska shi da abokinsa cikin dare ’yan sanda suka tsare su. Da ’yan sandan suka sami hodar iblis a wurin Antônio, sai suka fara bugunsa. Wani ɗan sanda ya jefa shi cikin taɓo ya ɗaura bindiga kusa da fuskarsa. “Ka gama da shi!” in ji ɗayan ɗan sandan.
Da yake kwance cikin taɓon, Antônio ya yi tunanin rayuwarsa. Abin kirki da ya tuna a rayuwarsa su ne iyalinsa da kuma Jehovah. Ya yi gajeriyar addu’a, ya roƙi taimakon Jehovah. Babu dalili ’yan sandan suka ƙyale shi. Ya je gida da tabbacin cewa Jehovah ya kiyaye shi.
Antônio ya fara nazarin Littafi Mai-Tsarki da sabon ƙwazo. A hankali a hankali, ya yi gyara domin ya faranta wa Jehovah rai. (Afisawa 4:22-24) Da ya koyi kame kai, sai ya fara gwagwarmaya da matsalarsa ta shan ƙwaya. Duk da haka, yana bukatar magani daga asibiti. Wata biyu a asibitin farfaɗowa da mashaya ya ba shi zarafin karanta littattafai da yawa na Littafi Mai-Tsarki, har da littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Sai Antônio ya gaya wa wasu majiyata abin da ya koya daga littattafan.
Bayan an sallami Antônio daga asibitin, Antônio ya ci gaba da nazarin Littafi Mai-Tsarki da Shaidun Jehovah. A yau, Antônio, Maria, da ’ya’yansu mata biyu, mamar Antônio duka suna bauta wa Jehovah tare a iyali mai farin ciki da kuma zumunci. Antônio ya ce: “Yanzu na fahimci ma’ana ta gaskiya ta kalmomin nan ‘Allah ƙauna ne.’ ”
[Hoto a shafi na 18]
Wa’azi a Rio de Janeiro