Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 5/1 p. 32
  • Ya Mutu Domin Bin Ƙa’ida

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Mutu Domin Bin Ƙa’ida
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 5/1 p. 32

Ya Mutu Domin Bin Ƙa’ida

“MUN tuna da August Dickmann (an haife shi a shekara ta 1910), ɗaya ne daga cikin Shaidun Jehovah.” Haka rubutu da aka yi a kan allo ya fara (da aka nuna nan) wanda aka buɗe ba da daɗewa ba a sansanin fursuna na dā na Sachsenhausen. Me ya sa ɗaya daga cikin Shaidun Jehovah ya sami irin wannan matsayin? Sauran rubutun ya ba da labarin: “SS (’yan sanda na Hitler) sun harɓe shi a idon jama’a a ranar 15 ga Satumba, 1939, saboda addininsa.”

An kama August Dickmann an tsare shi a sansanin fursuna na Sachsenhausen a shekara ta 1937. Kwanaki uku bayan ɓarkewan Yaƙin Duniya na II, a 1939, aka umurce shi ya sa hannu a takarda na zama soja. Da ya ƙi, sai shugaban sansanin ya je wajen Heinrich Himmler shugaban SS (Schutzstaffel, rukuni mai girma na masu tsaron Hitler), ya nemi izini ya kashe Dickmann a gaban dukan sauran fursunoni na sansanin. A ranar 17 ga Satumba, 1939, jaridar The New York Times ta ba da rahoto daga Jamus: “An harɓe August Dickmann ɗan shekara 29 . . . a nan.” Jaridar ta ce shi ne Ba’jamushe na farko da ya ƙi yaƙi domin addininsa.

Bayan shekara 60, a ranar 18 ga Satumba, 1999, Ƙungiyar Brandenburg Memorial ta yi bikin tuna mutuwar Dickmann, yanzu allon tunawa da mutuwarsa yana tunatar da masu ziyara gaba gaɗinsa da kuma imaninsa mai ƙarfi. Allo na biyu da yake garun waje na sansanin na dā yana tunatar da masu ziyara cewa Dickmann ɗaya ne kawai cikin Shaidun Jehovah 900 waɗanda suka wahala a Sachsenhausen domin abin da suka gaskata. Wasu da yawa sun wahala a wasu sansanonin. Hakika, har a cikin mummunan yanayi na sansanin fursunan, da yawa cikin aminci sun bi ƙa’idodin Allah.

Ga Shaidun Jehovah, hakinsu ne na Kirista su yi “biyayya da ikon masu-mulki.” (Romawa 13:1) Amma, idan gwamnatoci suka yi ƙoƙarin su saka su dole su karya dokokin Allah, suna yin koyi da manzannin Kristi, waɗanda suka ce: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.” (Ayukan Manzanni 5:29) Wannan ya sa, a wurare inda gāba tsakanin ƙabilu da kuma ƙiyayya tsakanin zuriya ya kai ga ta’addanci, Shaidun Jehovah a ko’ina, kamar August Dickmann, suna neman zaman lafiya. Suna bin gargaɗin Littafi Mai-Tsarki: “Kada ku rinjayu ga mugunta, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.”—Romawa 12:21.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba