Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Rayuwar Iyali Mai Farin Ciki Tana Jawo Wasu Wajen Allah
JEHOVAH ya albarkace Yusuf da hikima mai yawa da fahimi. (Ayukan Manzanni 7:10) Saboda haka, basirar Yusuf “ya yi kyau ga ganin Fir’auna, da dukan bayinsa.”—Farawa 41:37.
Hakanan ma a yau, Jehovah yana ba mutanensa basira da fahimi ta wajen nazarinsu na Littafi Mai-Tsarki. (2 Timothawus 3:16, 17) Wannan hikima da fahimi yana fid da ’ya’ya masu kyau yayin da an yi amfani da gargaɗi mai tushe cikin Littafi Mai-Tsarki. Halayensu masu kyau sau da yawa ‘ya yi kyau ga ganin waɗanda suke lura da su,’ yadda labarai na biye daga Zimbabwe ya nuna.
• Wata mata tana da maƙwabta waɗanda Shaidun Jehovah ne. Ko da yake ba ta son Shaidun, tana sha’awar halayensu, musamman ma rayuwarsu na gida. Ta lura cewa mata da mijin suna da dangantaka mai kyau sosai, kuma cewa yaransu suna da biyayya. Musamman ma ta lura cewa mijin yana ƙaunar matansa sosai.
Wani abin da aka yarda da shi a wasu al’adun Afirka shi ne cewa idan maigida yana ƙaunar matarsa, wataƙila matar ta yi amfani da magani don ta “riƙe” shi ne. Sai matar ta doshi mata Mashaidiyar ta tambaye ta: “Don Allah za ki ba ni maganin da ki ka ba maigidanki don maigidana ya so ni yadda na ki yake son ki sosai?” Mashaidiyar ta amsa: “To, zan kawo maki gobe da rana.”
Washegari, ’yar’uwar ta ziyarce maƙwabciyarta da ‘maganinta.’ Menene ne? Littafi Mai-Tsarki ne, tare da littafin nan Sanin Da Ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Bayan sun bincika bayani daga littafin nan Sanin game da batun “Ginin Iyali Mai-Girmama Allah,” ta ce wa matar: “Wannan ne ‘maganin’ da ni da mijina muka yi amfani da shi don mu ‘riƙe’ juna, kuma shi ya sa muke son juna sosai.” Aka soma nazarin Littafi Mai-Tsarki, kuma matar ta ci gaba da sauri har an yi mata wankan nutsarwa na nuna keɓewar kanta ga Jehovah.
• Majagaba na musamman guda biyu da aka aika su zuwa wata ƙaramin ikklisiya kusa da kan iyaka a arewa maso gabashin Zimbabwe da Mozambique ba su fita wa’azin ƙofa zuwa ƙofa na makonni biyu ba. Me ya sa? Domin mutane suna zuwa wurinsu su ji abin da suke faɗa. Ɗaya cikin majagaban ya ba da labarin yadda wannan ya faru: “Muna tafiyar kilomita 15 don mu tafiyar da nazarin Littafi Mai-Tsarki na gida kowane mako da wani mutum da ya nuna marmari. Zuwa wurin ba shi da sauƙi. Muna tafiya cikin taɓo, kuma mu ƙetare kogi masu gudu da ke kai wa wuyarmu. Wannan ya ƙunsa mu sa tufafinmu da takalma a kanmu, mu ƙetare kogin, kuma mu sa tufafinmu bayan mun ƙetare.
“Himmarmu ta burge maƙwabtan wannan mutum da ya nuna marmari sosai. Ɗaya cikin waɗanda suka lura shi ne shugaban wani ƙungiyar addini na yankin. Ya ce wa mabiyansa: ‘Ba ku son ku kasance da himma kamar waɗannan samari biyu da su Shaidun Jehovah ne? Washegari, mabiyansa da yawa suka zo gidanmu su san abin da ya sa muka nace haka. Ƙari ga haka, makonni biyu na gaba, mutane da yawa sun ziyarce mu har ba mu da lokaci ma da za mu dafa abincin da za mu ci!”
Ɗaya cikin mutane da suka ziyarce gidan majagaban a wannan makonni biyu shi ne shugaba na addinin. Ka ga farin cikin majagaban nan yayin da ya yarda a yi nazarin Littafi Mai-Tsarki na gida da shi!