Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 76 p. 180-p. 181 par. 2
  • Yesu Ya Tsabtacce Haikalin

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Ya Tsabtacce Haikalin
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Yesu Ya Tsabtace Haikali
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • “Lokaci Ya Yi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 76 p. 180-p. 181 par. 2
Yesu ya yi amfani da bulala ya kori dabbobin da ke haikalin kuma ya ture teburan masu canjin kudi

DARASI NA 76

Yesu Ya Tsabtacce Haikalin

Yesu ya tafi Urushalima, a watan Afrilu na shekara ta 30 bayan haihuwarsa. Akwai mutane da yawa da suka zo Idin Ƙetarewa. Ana miƙa hadayu a haikalin a lokacin bikin. Wasu mutane suna zuwa tare da dabbobinsu, wasu kuma sukan saya a Urushalima.

Sa’ad da Yesu ya shiga haikalin, sai ya ga mutane suna sayar da dabbobi a ciki. Sun mai da gidan Allah wurin kasuwanci! Mene ne Yesu ya yi? Ya ɗauki bulala kuma ya kori dabbobin daga cikin haikalin. Ya ture teburan masu canja kuɗi kuma ya zubar da kuɗaɗen a ƙasa. Yesu ya gaya wa masu sayar da tsuntsaye cewa: ‘Ku fitar da waɗannan abubuwan daga nan! Kada ku mai da gidan Ubana wurin kasuwanci!’

Mutane sun yi mamakin ganin abin da Yesu ya yi. Hakan ya sa mabiyansa suka tuna da annabcin da aka yi a kan Almasihu cewa: ‘Himma domin gidan Jehobah za ta cinye ni.’

Yesu ya sake tsabtacce haikalin a shekara ta 33 bayan haihuwarsa. Ba zai bar kowa ya rena gidan Ubansa ba.

“Ba dama ku sa ranku ga bin Allah ku kuma sa ga kuɗi.”​—Luka 16:​13, Juyi Mai Fitar da Ma’ana

Tambayoyi: Mene ne Yesu ya yi sa’ad da ya ga mutane suna sayar da dabbobi a cikin haikali? Me ya sa Yesu ya yi hakan?

Matta 21:​12, 13; Markus 11:​15-17; Luka 19:​45, 46; Yohanna 2:​13-17; Zabura 69:9

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba