Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 59 p. 142-p. 143 par. 5
  • Matasa Hudu da Suka Yi wa Jehobah Biyayya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa Hudu da Suka Yi wa Jehobah Biyayya
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Yara Huɗu A Babila
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Hananiya da Mishayel da kuma Azariya
    Ka Koyi Darussa Daga Abokan Jehobah—Ayyuka
  • Darussa Daga Littafin Daniel
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Abin da Littafi Mai Tsarki ya Ce Game da Daniyel?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 59 p. 142-p. 143 par. 5
Daniyel da Hananiya da Mishayel da kuma Azariya sun ki cin abincin sarkin

DARASI NA 59

Matasa Huɗu Sun Yi Biyayya ga Jehobah

Sa’ad da Nebuchadnezzar ya kai hakiman Yahuda ƙasar Babila, ya sa Ashpenaz wanda shi ma’aikaci ne a fādar ya riƙa kula da su. Sarki Nebuchadnezzar ya gaya wa Ashpenaz cewa ya zaɓo samari masu ƙoshin lafiya da kuma hikima sosai a cikinsu. Za a horar da su har shekara uku. Wannan horarwar za ta taimaka musu su zama ma’aikata a Babila. Ana so matasan su koyi karatun Babila da rubutunsu da kuma yarensu. Ana kuma so su ci irin abincin da sarki da kuma waɗanda suke fādar suke ci. Sunayen huɗu daga cikin waɗannan matasan su ne Daniyel da Hananiya da Mishayel da kuma Azariya. Ashpenaz ya ba su sunan mutanen Babila, wato Belteshazzar da Shadrach da Meshach da kuma Abednego. Abubuwan da aka koya musu za su sa su daina bauta wa Jehobah kuwa?

Waɗannan matasan sun ƙuduri niyyar cewa za su yi wa Jehobah biyayya. Sun san cewa bai kamata su ci abincin sarkin ba domin Dokar Allah ta haramta cin wasu daga cikin abincin. Hakan ya sa suka gaya wa Ashpenaz cewa: ‘Don Allah kada ka sa mu mu ci abincin sarki.’ Sai Ashpenaz ya ce: ‘Sarki zai kashe ni idan kuka ƙi cin abincin kuma ya ga cewa ba ku da ƙoshin lafiya!’

Daniyel ya yi wani tunani. Sai ya gaya wa mai kula da su cewa: ‘Don Allah, ka ba mu kayan lambu da kuma ruwa kawai har kwana goma. Bayan haka, ka gwada mu da sauran mazan da suka ci abincin sarkin.’ Sai mai kula da su ya amince da hakan.

Bayan kwana goma, Daniyel da abokansa uku sun fi sauran mazan ƙoshin lafiya. Jehobah ya yi farin ciki sosai don sun yi masa biyayya. Har ma ya ba Daniyel basirar fahimtar wahayoyi da kuma mafarkai.

Da aka gama horar da su, sai Ashpenaz ya kawo su wurin Nebuchadnezzar. Sarkin ya yi magana da su kuma ya ga cewa Daniyel da Hananiya da Mishayel da kuma Azariya sun fi sauran mazan ilimi da ƙwazo. Sai ya zaɓe su su yi aiki a fādarsa. Sarkin yakan nemi shawararsu a kan wasu batutuwa masu muhimmanci. Jehobah ya ba su hikima fiye da sauran mutane masu hikima a ƙasar.

Ko da yake suna wata ƙasa dabam, Daniyel da Hananiya da Mishayel da kuma Azariya ba su manta cewa su mutanen Jehobah ba ne. Shin za ka ci gaba da bauta wa Jehobah ko a lokacin da iyayenka ba sa tare da kai?

“Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata.” ​—⁠Misalai 27:⁠11

Tambayoyi: Me ya sa Daniyel da abokansa uku suka yi wa Jehobah biyayya? Ta yaya Jehobah ya taimaka musu?

Daniyel 1:​1-21

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba