Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 37 p. 90-p. 91 par. 1
  • Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Sama’ila Ya Manne wa Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ya Ci Gaba da Yin Girma a Gaban Jehobah
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Sama’ila Ya Ci Gaba da Yin Abin da Ya Dace
    Ku Koyar da Yaranku
  • Ɗan Yaro Ya Bauta Wa Allah
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 37 p. 90-p. 91 par. 1
Sama’ila ya bude kofar mazaunin

DARASI NA 37

Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila

Eli Babban Firist yana da yara biyu da suke hidimar firist a mazauni. Sunayensu Hophni da Finehas ne. Ba su yi biyayya ga Jehobah ba kuma suna ba mutane wahala. Idan mutane suka kawo hadaya ga Jehobah, sai Hophni da Finehas su ɗauki nama mai soka su ci. An gaya wa Eli abin da yaransa suke yi amma bai yi musu kome ba. Shin Jehobah zai bar su su riƙa yin haka ne?

Ko da yake Hophni da Finehas sun girme Sama’ila, amma bai koyi halinsu ba. Abin da Sama’ila ya yi ya sa Jehobah farin ciki sosai. Wata rana da yake barci da dare, sai ya ji wani yana kiransa. Ya tashi da gudu ya je wurin Eli ya ce: ‘Ga ni!’ Amma Eli ya ce masa: ‘Ban kira ka ba. Ka koma ka yi barci.’ Sai Sama’ila ya koma ya kwanta. Sai aka sake kiransa. Da hakan ya faru sau uku, sai Eli ya gane cewa Jehobah ne yake kiran Sama’ila. Sai Eli ya gaya wa Sama’ila cewa idan ya sake jin kiran, ya ce: ‘Jehobah, ka yi magana bawanka yana sauraro.’

Sama’ila ya gaya wa Eli abin da Jehobah ya ce masa

Da Sama’ila ya koma ya kwanta, sai ya ji ana cewa: ‘Sama’ila, Sama’ila!’ Sai ya ce: ‘Ka yi magana, bawanka yana sauraro.’ Sai Jehobah ya ce masa: ‘Ka gaya wa Eli cewa zan yi wa shi da iyalinsa horo. Ya san cewa yaransa suna yin abubuwa marasa kyau a mazauni, amma bai yi musu kome ba.’ Da safe ya yi, sai Sama’ila ya buɗe ƙofofin mazaunin kamar yadda ya saba. Amma yana jin tsoro ya gaya wa Eli abin da Jehobah ya gaya masa. Sai Eli ya kirawo shi ya ce: ‘Ɗana, mene ne Jehobah ya gaya maka? Kar ka ɓoye mini kome.’ Sai Sama’ila ya gaya wa Eli kome da kome.

Jehobah ya ci gaba da kula da Sama’ila yayin da yake girma. Duk mutanen ƙasar sun san cewa Jehobah ne ya zaɓi Sama’ila ya zama annabi da kuma alƙali.

“Ka tuna da Mahaliccinka kuma a cikin kwanakin ƙuruciyarka.”​—Mai-Wa’azi 12:1

Tambayoyi: Ta yaya Sama’ila ya yi dabam da Hophni da Finehas? Wane saƙo ne Jehobah ya ba Sama’ila?

1 Sama’ila 2:​12-17, 22-26; 3:​1-21; 7:6

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba