Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 7 p. 24-p. 25 par. 1
  • Hasumiyar Babel

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hasumiyar Babel
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Mutane Sun Gina Babbar Hasumiya
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Jirgin Nuhu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 7 p. 24-p. 25 par. 1
Bayan Jehobah ya canja yaren mutane, sai hakan ya hana su gina Hasumiyar Babel tare

DARASI NA 7

Hasumiyar Babel

Bayan Ambaliyar Ruwan, yaran Nuhu sun haifi yara da yawa. Sai suka soma yawa kuma suka soma zama a wurare dabam-dabam a duniya, kamar yadda Jehobah ya ce su yi.

Amma wasu daga cikin jikokin Nuhu ba su yi biyayya ga Jehobah ba. Sun ce: ‘Bari mu gina birni kuma mu zauna a ciki. Za mu gina babban gida wanda tsawonsa zai kai sama. Haka zai sa a san mu sosai.’

Abin da mutanen suka yi ya sa Jehobah fushi, sai ya ce zai hana su yin ginin. Ka san yadda ya yi hakan? Ya sa sun soma yin yare dabam-dabam. Tun da ba su fahimci juna ba, sai suka daina ginin. Birnin da suka gina ne ake kira Babel, wato “Ruɗewa.” Sai mutanen suka soma zama a ƙasashe dabam-dabam. Amma sun ci gaba da yin abubuwa marar kyau a waɗannan wuraren. Kana ganin da akwai mutumin da ke ƙaunar Jehobah a duniya a lokacin? Za mu sami amsar a babi na gaba.

“Allah yana ƙin mai girman kai, amma yana yin alheri ga mai sauƙin kai.”​—Yaƙub 4:​6, Juyi Mai Fitar da Ma’ana

Tambayoyi: Mene ne mutanen Babel suka yi? Mene ne Jehobah ya yi don ya hana su yin abin da suke so?

Farawa 11:​1-9

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba