Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • rj kashi 5 pp. 12-15
  • Ku Komo “Wurin Makiyayi da Mai tsaron Rayukanku”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Komo “Wurin Makiyayi da Mai tsaron Rayukanku”
  • Ka Komo ga Jehobah
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Juyo Gare Ni”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Zai Karfafa Ka
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • Jehobah Yana Kaunarka Sosai!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ku Taimake Su Su Dawo Babu Ɓata Lokaci!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Ka Komo ga Jehobah
rj kashi 5 pp. 12-15

SASHE NA BIYAR

Ku Komo “Wurin Makiyayi da Mai Tsaron Rayukanku”

Shin ka taɓa samun kanka kana fama da wasu ƙalubale da aka tattauna a cikin wannan ƙasidar? Idan haka ne, ba kai kaɗai ba ne. Amintattun bayin Jehobah Allah a dā da kuma a zamaninmu sun fuskanci irin waɗannan yanayin. Jehobah ya taimaka musu su sha kan waɗannan ƙalubalen, kuma zai taimaka maka kai ma.

Jehobah zai kasance tare da kai yayin da ka komo gare shi

KA TABBATA cewa Jehobah zai kasance tare da kai idan ka komo gare shi. Zai taimaka maka ka daina alhini da kuma ɓacin rai. Ƙari ga haka, za ka sami kwanciyar hankali don za ka kasance da lamiri mai kyau. Za ka sake yin marmarin bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwa masu bi. Yanayinka zai kasance kamar na wasu Kiristoci a ƙarni na farko da manzo Bulus ya ba wa wannan shawarar: “Dā kuna ɓacewa kamar tumaki; amma yanzu kun komo wurin Makiyayi da Mai tsaron rayukanku.”—1 Bitrus 2:25.

Babu abin da za ka yi da zai fi shawarar da ka yi na sake bauta wa Jehobah. Me ya sa? Don za ka faranta wa Jehobah rai. (Misalai 27:11) Kamar yadda ka sani, abubuwan da muke yi za su iya sa Jehobah baƙin ciki ko farin ciki, amma ba ya tilasta mana mu bauta masa. (Kubawar Shari’a 30:19, 20) Jehobah ya ba mu damar yin zaɓi, saboda haka, ba ya tilasta mana mu bauta masa. Idan muka bauta wa Jehobah da son rai da kuma ƙauna, muna nuna masa cewa mu masu aminci ne, kuma hakan yana faranta masa rai sosai. Hakika, ba abin da zai sa mu farin ciki kamar yin ibada ga wanda ya cancanci bautarmu, wato Jehobah.—Ayyukan Manzanni 20:35; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

Ana marabtar wata ‘yar’uwa da ta daina zuwan taro da fita wa’azi sa’ad da ta dawo cikin ikilisiya

Bugu da ƙari, idan ka soma bauta wa Jehobah kamar yadda ka yi a dā, za ka ƙarfafa dangantakarka da shi kuma za ka gamsu. (Matta 5:3) Ta yaya? Mutane a ko’ina suna so su san abin da ya sa muke raye. Suna neman amsoshi ga tambayoyi game da rayuwa. ’Yan Adam suna so su san amsoshin don Allah ya halicce su da wannan burin. Allah ya yi mu don mu bauta masa kuma mu ji daɗin rayuwa yayin da muke yin hakan. Babu abin da zai sa mu farin ciki kamar sanin cewa muna bauta wa Jehobah don muna ƙaunarsa.—Zabura 63:1-5.

Don Allah ka tuna cewa Jehobah yana so ka komo gare shi. Ta yaya za ka tabbata da hakan? Ka yi la’akari cewa kafin a shirya wannan ƙasidar, an natsu kuma an yi addu’a sosai. Wataƙila wani dattijo ko kuma wani ɗan’uwa ne ya ba ka ƙasidar. Hakan ya sa ka marmarin karantawa kuma ka ɗauki wasu matakai saboda shawarwarin da ke ciki. Hakan ya nuna cewa Jehobah bai yi watsi da kai ba. Akasin haka, yana jan hankalinka da sannu-sannu don ka sake bauta masa.—Yohanna 6:44.

Sanin cewa Jehobah bai manta da bayinsa da suka ɓace ba yana da ban ƙarfafa. Abin da wata ’yar’uwa mai suna Donna ta fahimta ke nan. Ta ce: “Da sannu a hankali na bar gaskiya, amma a wasu lokatai nakan yi tunani game da abin da aka rubuta a  Zabura 139:23, 24 cewa: ‘Ka yi bincikena, ya Ubangiji, ka san zuciyata: Ka auna ni, ka san tunanina: Ka duba ko da wata hanyar mugunta daga cikina, ka bishe ni cikin tafarki na har abada.’ Na san cewa ni ba na duniya ba ne kuma ban ji daɗin rayuwa ba sa’ad da na daina bauta wa Jehobah. Na san cewa ya kamata in kasance a cikin ƙungiyar Jehobah. Sai na soma fahimta cewa Jehobah bai yi watsi da ni ba; ni ne ke bukatar in komo gare shi. Abin da na yi ke nan kuma ina farin ciki cewa na yi hakan!”

“Sai na soma fahimta cewa Jehobah bai yi watsi da ni ba; ni ne ke bukatar in komo gare shi”

Muna fata cewa kai ma za ka sake samun “farin ciki na Ubangiji.” (Nehemiya 8:10) Ba za ka taɓa yin da-na-sani cewa ka komo ga Jehobah ba.

Amsoshin Tambayoyi Game da Yadda Za Ka Komo ga Jehobah

YAYA ZAN SOMA?

Wata ‘yar’uwa da ta daina zuwan taro da fita wa’azi tana karanta Littafi Mai Tsarki

Ya dace mutumin da ya yi rashin lafiya ya soma aiki da sannu-sannu. Hakazalika, ya dace ka soma hidimomin da ka saba yi a matsayinka na Kirista ta wajen yin akalla wani abu kowace rana don ƙarfafa dangantakarka da Jehobah. Kada ka ɗauka cewa kana bukatar ka yi abubuwa da yawa a lokaci guda. Za ka iya karanta ko saurari karatun Littafi Mai Tsarki, za ka iya yin nazarin wani littafinmu ko kuma ka shiga dandalinmu na jw.org/⁠ha. Kuma ka yi kokari ka halarci taron ikilisiya nan da nan. Ƙari ga haka, yana da muhimmanci sosai ka yi addu’a ga Jehobah don neman taimakonsa. Ka ‘zuba dukan alhininka a bisansa, domin yana kula da kai.’​—⁠1 Bitrus 5:⁠7.

Wata ‘yar’uwa mai suna Eeva ta ce: “Na yi sanyin gwiwa har na kasa yin addu’a bayan na daina bauta wa Jehobah tare da ‘yan’uwa a ikilisiya. Da na yi addu’a, sai wani dattijo ya zo ya tattauna da ni. Kuma ya taimaka min in san cewa Jehobah yana so na har ila. Ya ba ni shawara in karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. Yin hakan ya ƙarfafa ni kuma na soma halartan taro. Da shigewar lokaci, na soma yin wa’azi. Ina farin ciki cewa Jehobah bai manta da ni ba.”

’YAN’UWA ZA SU MARABCE NI KUWA?

Ka kasance da tabbaci cewa ‘yan’uwa za su marabce ka sosai. Ba za su kushe ka ba kuma ba za su zarge ka ba. A maimakon haka, za su nuna cewa suna ƙaunarka kuma za su yi iya ƙoƙarinsu don su ƙarfafa ka.​—⁠Ibraniyawa 10:​24, 25.

Wani dan’uwa da ake kira Javier ya bayyana cewa: “Na ji kunyar zuwa Majami’ar Mulki. Ina ta tunanin yadda ‘yan’uwa za su bi da ni. Wata ‘yar’uwa da ta manyanta wadda take tarayya da ikilisiyar tun shekaru 30 da suka shige ta ce mini, ‘Maraba Dana!’ Hakan ya taba zuciyata sosai. Hakika na dawo gida.”

Marco ya ce: “Sa’ad da na je Majami’ar Mulki, na zauna a kujerar baya don kada ‘yan’uwa su san cewa ni ne. Amma, ‘yan’uwa da yawa sun gan ni kuma suka tuna cewa na halarci taro sa’ad da nake yaro. Sun marabce ni kuma sun rungume ni sosai, kuma hakan ya sa na kasance da kwanciyar hankali. Kamar na dawo ne daga wata tafiya mai nisa.”

DATTAWA ZA SU TAIMAKE NI KUWA?

Dattawa za su mutunta ka. Za su yaba maka don ƙoƙarin da ka yi ka sake ‘ƙaunar’ Jehobah kamar yadda ka yi a dā. (Ru’ya ta Yohanna 2:⁠4) Za su taimake ka ka daidaita duk wani kuskuren da ka yi, kuma za su yi hakan cikin “tawali’u.” (Galatiyawa 6:1; Misalai 28:13) Dattawa za su iya gaya wa wani ya yi nazari da kai, wataƙila za su ce ya yi amfani da littafi kamar Ka Kusaci Jehovah ko kuma “Ku Tsare Kanku Cikin Kaunar Allah.” Ka tabbata cewa dattawa za su ƙarfafa ka kuma su tallafa maka a duk yanayin da kake ciki.​—⁠Ishaya 32:​1, 2.

Wani dan’uwa mai suna Victor ya ce: “Dattawa sun rika kawo min ziyara a shekaru takwas da na daina tarayya da ‘yan’uwa a ikilisiya. Wata rana, wani dattijo ya nuna mini wasu hotuna da muka dauka tare. Hakan ya sa na tuna da abubuwa masu ban farin ciki da suka faru a lokacin da nake bauta wa Jehobah, kuma na yi marmarin komowa ga Jehobah saboda haka. Dattawa sun taimaka mini in sake daukan matakai don ƙarfafa dangantakata da Jehobah.”

Zai “Ƙarfafa” Ka

’Yan’uwa mata biyu suna amfani da littafin waka guda yayin da suke rera waka a taron ikilisiya

Littafin wakarmu Sing to Jehovah, yana dauke da wakoki masu motsa rai kuma wadannan wakokin za su karfafa ka don ka soma bauta wa Jehobah kamar yadda ka yi a dā. Alal misali, ka yi la’akari da kalmomin waka ta 60. An dauko wakar ne daga 1 Bitrus 5:10 kuma jigon wakar shi ne Zai “Karfafa” Ka.

  1. Allah ya kira ka zuwa cikin gask’ya

    Daga cikin duhu zuwa haske.

    Ya ga zuciyarka, da kwazon da ka yi

    Don ka bauta ma sa da aminci.

    Ka yi alkawarin yin nufinsa;

    Zai taimake ka har abada fa.

  2. Allah ya ba da Dansa Yesu dominka;

    Domin Yana so ka yi nasara.

    Bai yi jinkirin hadaya da Dansa ba,

    Ka tabbata zai karfafa ka fa.

    Zai tuna amincin da ka nuna;

    Zai kula da dukan mutanensa.

    (AMSHI)

    Ta wurin fansar Yesu, ka zama bawan Jah.

    Zai tallafa maka, zai karfafa ka fa.

    Zai maka kāriya da ja-gora koyaushe.

    Zai tallafa maka, zai karfafa ka fa.

Sing to Jehovah​—⁠Vocal Renditions

Ka yi scan din wannan alamar da na’urarka ko kuma ka shiga dandalin www.jw.org don ka saurari wannan wakar da kuma wasu. Ka duba karkashin PUBLICATIONS > MUSIC.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba