Abin da ke Ciki
SASHE NA 1 ME YA SA YA DACE KA KOMO GA JEHOBAH?
Bayin Jehobah a dā sun fuskanci irin ƙalubalen da muke fuskanta. Jehobah bai yi watsi da su ba. Maimakon haka, ya taimaka musu. Hakazalika, zai taimaka mana a yau. Shi Makiyayi ne mai ƙauna, yana biɗan tumakinsa da suka ɓace kuma yana gayyatar su su komo gare shi.
Sashe na 1 Zan Nemo Wanda Ya Ɓata
SASHE NA 2-4 WAƊANNE ƘALUBALE NE WAƊANDA SUKE SO SU KOMO GA JEHOBAH SUKE FUSKANTA?
A wani lokaci, amintattun bayin Allah suna samun kansu a wani yanayi da ke sa alhini da ɓacin rai. Ƙari ga haka, sukan yi tunani cewa suna da alhaki a kansu. Wannan yanayin yakan sa su yi sanyin gwiwa a ibadarsu. Ka bincika yadda Jehobah ya taimaka musu su sake tarayya da mutanensa kuma su bauta masa da farin ciki kamar yadda suka yi a dā.
Sashe na 2 Alhini—Muna Fuskantar Takura a Kowane Ɓangare
Sashe na 3 Ɓacin Rai—Sa’ad da Wani Ya Ɓata Mana Rai
Sashe na 4 Alhakin Laifi—“Ka Tsarkake Ni Daga Zunubina”
SASHE NA 5 YADDA ZA KA KOMO GA JEHOBAH
A wannan sashen, za mu ga wasu dalilai da suka nuna cewa Jehobah yana so ka komo gare shi. Za ka koyi yadda wasu Kiristoci da dama suka komo ga Jehobah da yadda ’yan’uwa a cikin ikilisiya suka marabce su. Ƙari ga haka, za ka ga yadda dattawa suka taimaka musu su sake bauta wa Jehobah da ƙwazo.