Hagu: Wata ’yar’uwa mai wa’azi na cikakken lokaci tana bishara a Koriya, a 1931; dama: Yin wa’azi a yaren kurame a Koriya a yau
SASHE NA 2
Wa’azin Mulkin—Yadda Ake Yaɗa Bishara a Dukan Duniya
KA YI shirin fita wa’azi a safiyar ranar da ka sami hutu daga wajen aiki. Ka ɗan yi jinkirin fita saboda gajiya kuma kana jin cewa zai dace ka ɗan huta! Amma sai ka yi addu’a game da batun kuma ka fita wa’azi. A ranar ka fita wa’azi ne tare da wata tsohuwar ’yar’uwa mai aminci wadda jimiri da alherinta sun taɓa zuciyarka sosai. Yayin da kuke bi gida-gida kuna wa’azin Mulkin, sai ka tuna cewa ’yan’uwa maza da mata a faɗin duniya ma suna yin hakan kuma suna yin amfani da irin littattafan da kuke amfani da su. Ƙari ga haka, duk kuna amfana ne daga koyarwa iri ɗaya. Sa’ad da ka koma gida, ka ji wani irin sabon ƙarfi kuma ka yi murnar cewa ba ka zauna a gida ba!
A yanzu haka, wa’azin bishara shi ne aiki mafi muhimmanci na Mulkin Allah. Yesu ya annabta cewa za a yi aikin wa’azin nan a faɗin duniya a wannan kwanaki na ƙarshe. (Mat. 24:14) Ta yaya annabcin nan yake cika? A wannan sashen, za mu tattauna game da mutanen da suke wa’azin Mulkin da tsarin da suke bi da kuma kayan aikin da suke amfani da shi da ke taimaka wa miliyoyin mutane a faɗin duniya su ga cewa Mulkin Allah abu ne na gaskiya.