Hagu: Wata ’yar’uwa a Alabama, Amirka, ta saka faifain jawabin Dan’uwa Rutherford, a shekara ta 1930; Dama: Siwizalan
SASHE NA 1
Gaskiya Game Da Mulkin—Tanadar da Abubuwan da Suke Ƙarfafa Dangantakarmu da Allah
A CE ka karanta wa ɗalibinka wani nassi kuma sai ya kalle ka cike da mamaki domin yadda ya fahimci batun da kuka tattauna. Sai ya ce, “Kana nufin Littafi Mai Tsarki yana koyar da cewa za mu yi rayuwa a Aljanna a wannan duniyar har abada?” Sai wanda kuke wa’azi tare ya yi murmushi kuma ya ce, “Me ka karanta a Littafi Mai Tsarki yanzu?” Cike da mamaki ɗalibinka ya kaɗa kansa ya ce, “A gaskiya ban taɓa sanin hakan ba sai yau.” Sai ka tuna cewa ya yi irin wannan furucin ’yan makonnin da suka shige sa’ad da ya koyi cewa sunan Allah shi ne Jehobah.
Hakan ya taɓa faruwa da kai kuwa? Bayin Allah da yawa sun shaida hakan. Wasu abubuwa za su iya tuna mana da kyauta mai tamani da muke da ita, wato gaskiyar da aka koya mana daga Littafi Mai Tsarki! Ka ɗan dakata ka yi tunani a kan wannan tambayar: Ta yaya ka sami wannan kyautar? Za mu tattauna tambayar nan a wannan sashen. Yadda bayin Allah suke samun ƙarin haske game da koyarwar Allah da sannu-sannu yana tabbatar da mu cewa an kafa Mulkin Allah. A cikin shekaru ɗari yanzu, Sarki, Yesu Kristi, yana aiki wurjanjan don ya ga cewa an koya wa bayin Allah gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.