Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • yc darasi na 14 pp. 30-31
  • Mulkin da Za A Yi Bisa Dukan Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mulkin da Za A Yi Bisa Dukan Duniya
  • Ku Koyar da Yaranku
  • Makamantan Littattafai
  • Aminan Allah Za Su Zauna A Cikin Aljanna
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
  • Minene Nufin Allah ga Duniya?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Waye Za A Ta Da Daga Matattu? A Ina Za Su Zauna?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • “Sai Mun Haɗu a Aljanna!”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Ku Koyar da Yaranku
yc darasi na 14 pp. 30-31
Yesu Kristi yana sarauta bisa Aljanna a duniya

DARASI NA 14

Mulkin da Za A Yi Bisa Dukan Duniya

Ka san ko wane Mulki ne muke magana a kai?— E, Mulkin Allah ne, kuma shi ne zai sa duniya ta zama aljanna. Za ka so ka ƙara koya game da wannan Mulkin?—

Kowane mulki yana da sarki. Kuma sarkin yana sarauta bisa mutanen ƙasarsa. Ka san ko wane ne Sarkin Mulkin Allah?— Yesu Kristi ne. Yana sama. Ba da daɗewa ba, zai zama Sarki bisa kowa a duniya! Kana ganin za mu yi farin ciki idan Yesu ya zama Sarki bisa duniya?—

Mene ne kake so ka ga ya faru a cikin Aljanna?

Za mu yi farin ciki sosai! A cikin Aljanna, mutane za su daina faɗa da juna. Dukan mutane za su ƙaunaci juna. Babu wanda zai yi rashin lafiya ko ya mutu. Makafi za su soma gani, kurame za su soma jin magana kuma guragu za su yi gudu su yi tsalle. Mutane za su samu abinci da yawa. Dabbobi za su yi wasa da juna kuma mu ma za mu yi wasa da su. Za a ta da waɗanda suka mutu. Maza da mata da ka karanta labarinsu a wannan ƙasidar, kamar su Rifkatu da Rahab da Dauda da kuma Iliya za su tashi daga mutuwa! Za ka so ka gan su sa’ad da aka ta da su?—

Jehobah yana ƙaunarka kuma yana so ka yi farin ciki. Idan ka ci gaba da koya game da Jehobah kuma ka yi masa biyayya, za ka yi rayuwa har abada a cikin aljanna mai kyau! Abin da kake so ke nan?—

KARANTA NASOSSIN NAN

  • Ishaya 2:4; 11:6-9; 25:8; 33:24; 35:5, 6

  • Yohanna 5:28, 29; 17:3

TAMBAYOYI:

  • Wane ne Sarkin Mulkin Allah?

  • Yesu zai zama Sarki bisa su wane ne?

  • Yaya abubuwa za su zama idan Yesu ya soma sarauta bisa duniya?

  • Idan kana so ka rayu har abada a cikin Aljanna, mene ne za ka yi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba