Gabatarwa
Ka Taɓa Yin Tunanin?
Mene ne gaskiya game da Allah?
Ta yaya za ka iya sa rayuwar iyalinka ta kasance mai farin ciki?
Me ya sa matsaloli suka yi yawa a duniya a yau?
Me ya sa Allah ya ƙyale wahala?
Mene ne Allah ya nufa ga duniya?
Ina matattu suke?
Ta yaya mala’iku suke taimaka mana?
Ta yaya za ka iya kusantar Allah?
Miliyoyin mutane sun samu amsoshi masu gamsarwa na waɗannan tambayoyin ta wajen yin nazarin Nassosi Masu Tsarki. Kai ma za ka iya yin hakan.
Idan za ka so ƙarin bayani, don Allah ka tuntuɓi mawallafin wannan mujallar a adireshi mafi kusa da kai a cikin waɗanda aka jera a ƙasa.