Sashe 16
Almasihu Ya Bayyana
Jehobah ya bayyana Yesu Banazare a matsayin Almasihun da aka yi alkawarinsa tun da daɗewa
JEHOBAH zai taimaka wa mutane ne su gane Almasihun da aka yi alkawarinsa? E. Yi la’akari da abin da Allah ya yi. Hakan ya faru ne bayan ƙarnuka huɗu da kammala Nassosin Ibrananci. A cikin wani birni mai suna Nazarat, a arewacin Galili, an kai wa wata mace budurwa mai suna Maryamu ziyara mafi ban mamaki. Wani mala’ika mai suna Jibra’ilu ya bayyana a gare ta kuma ya gaya mata cewa Allah zai yi amfani da ƙarfin ikonsa, ruhunsa mai tsarki, ya sa ta haifi ɗa, duk da cewa ita budurwa ce. Wannan ɗan shi ne Sarkin da aka yi alkawarinsa tun da daɗewa, wanda zai yi sarauta har abada! Wannan yaron zai kasance Ɗan Allah, wanda Allah zai tura ransa daga sammai zuwa mahaifar Maryamu.
Maryamu ta karɓi wannan aiki mai muhimmanci cikin tawali’u. Saurayinta, wani kafinta mai suna Yusufu, ya aure ta ne bayan Allah ya aika masa mala’ika don ya tabbatar da shi yadda Maryamu ta sami cikin. Annabcin nan kuma fa da ya ce za a haifi Almasihu a Bai’talami? (Mikah 5:2) Wannan ɗan ƙaramin garin yana da nisan mil 90 da Nazarat!
Wani sarki ɗan Roma ya kafa doka cewa a yi ƙirge. An umurci mutane su je su yi rajista a birnin da aka haife su. Kamar dai an haifi Yusufu da Maryamu ne a Bai’talami, hakan ya sa Yusufu ya tafi tare da matarsa da ke da juna biyu zuwa birnin. (Luka 2:3) Maryamu ta haihu a inda ake ajiye dabbobi, kuma ta kwantar da jaririn a cikin sakarkari. Bayan haka, Allah ya aiki mala’ika ya je ya gaya wa makiyaya da ke gefen dutse cewa yaron da aka haifa shi ne Almasihu ko Kristi da aka yi alkawarinsa.
Daga baya, wasu za su ba da shaida cewa Yesu ne Almasihun da aka yi alkawarinsa. Annabi Ishaya ya annabta cewa akwai mutumin da zai taso don ya shirya hanya domin aiki mai muhimmanci da Almasihu zai yi. (Ishaya 40:3) Mai share fagen shi ne Yohanna Mai Baftisma. Sa’ad da ya ga Yesu, ya ce da babbar murya: “Duba, ga Ɗan rago na Allah wanda yana ɗauke da zunubin duniya!” Nan da nan wasu daga cikin almajiran Yohanna suka bi Yesu. Ɗaya daga cikinsu ya ce: “Mun sami Almasihu”—Yohanna 1:29, 36, 41.
Akwai kuma ƙarin shaida. A lokacin da Yohanna ya yi wa Yesu baftisma, Jehobah da kansa ya yi magana daga sama kuma ya ce: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.” (Matta 3:16, 17) Almasihun da aka yi alkawarinsa tun da daɗewa ya bayyana!
A wane lokaci ne hakan ya faru? A shekara ta 29 A.Z., daidai lokacin da shekaru 483 da Daniyel ya annabta suka ƙare. Hakika, wannan sashe ne mai girma na shaidar da ta tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu, ko Kristi. Amma wane saƙo ne zai sanar a lokacin da yake duniya?
—An ɗauko daga Matta surori 1 zuwa 3; Markus sura ta 1; Luka sura ta 2; Yohanna sura ta 1.
◼ Ta yaya ne Jehobah ya yi amfani da mala’ika ya bayyana cewa Yesu ne Almasihu?
◼ Ta yaya ne Allah ya yi amfani da Yohanna Mai Baftisma ya nuna cewa Yesu ne Kristi?
◼ Ta yaya ne Jehobah da kansa ya bayyana Ɗansa a matsayin Almasihu?
[Akwati a shafi na 19]
ƊAN ALLAH A WANE AZANCI?
Jehobah ne Uban Yesu, amma ba kamar yadda mutane suke zama uba ba. Ba a haifi Yesu ta hanyar auratayya ba, Allah ne ya halicce shi. Shi ne mutumi na farko da Jehobah ya halitta. (Kolossiyawa 1:15-17) Tun da yake Jehobah ne ya ba Yesu rai sa’ad da ya halicce shi, za a iya kiran shi Uban Yesu. Bayan ya halicci wannan Ɗa ruhu, Jehobah ya yi amfani da shi a matsayin “gwanin mai-aiki” ya halicci dukan abubuwa, har da sararin samaniya.—Misalai 8:30.
[Taswira a shafi na 19]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta ●
Markus ●
Luka ●
Yohanna ●
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa