Taimako don a Fahimci Littafi Mai Tsarki
Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da muhimman koyarwa dominka.
• Yana bayyana abin da Mahalicci ya ce game da ma’anar rayuwa.
• Yana ba da gargaɗi mafi kyau a kan yadda za a iya jure da matsaloli da yawa na rayuwar yanzu.
• Yana nuna abin da ake bukata don a amince da mu sa’ad da dukanmu muka tsaya a gaban kujerar shari’a ta Allah.
Ana tafiyar da nazarorin Littafi Mai Tsarki 5,000,000 a kai a kai a dukan duniya.
An yi shiri da zai yi daidai da yanayinka. KYAUTA.
Ka rubuta zuwa adireshi da ke ƙasan nan wanda ke kusa da kai ko ka tambayi duk wani Mashaidin Jehovah da yake inda kake zama.