Menene Suka Gaskata?
SHAIDUN JEHOVAH sun gaskata da Maɗaukaki Allah, Jehovah, Mahaliccin sama da ƙasa. Abubuwa masu wuya da suke wanzuwa, da ke na al’ajabi a duniya da suka kewaye mu sun nuna cewa Mahalicci mai basira da kuma iko ne ya yi su duka. Yadda ayyukan maza da mata ke nuna halayensu, haka ma na Jehovah Allah suke nuna nasa. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa ‘tun halittar duniya al’amura nasa da ba su ganuwa, ta wurin abubuwa da an halitta ana ganinsu.’ Haka ma, ba tare da murya ba ko kuma kalmomi ‘sammai suna bayana ɗaukakar Allah.’—Romawa 1:20; Zabura 19:1-4.
Mutane ba sa mulmula tukwanen ƙasa ko kuma su yi telibijin da kwamfita ba tare da wani dalili ba. Halittar duniya ta tsiro da ta dabbobi sun fi ban mamaki. Ba za mu iya gane yadda aka yi jikin mutum da biliyoyin ƙwayoyin gina jiki ba—ƙwaƙwalwa ma da muke yin tunani da ita aba ce ta ban al’ajabi! Idan mutane suna da dalilin da ya sa suka ƙera abubuwa da ba su da muhimmanci, hakika Jehovah Allah yana da dalilin halitta da ya yi, masu ban mamaki! Misalai 16:4 ya ce “Ubangiji ya halicci kowane abu domin nufin kansa.”
Jehovah yana da dalilin da ya sa ya yi duniya, yadda ya gaya wa mutane biyu na fari: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya . . . ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari, da kowane abu mai-rai wanda ke rarrafe a ƙasa.” (Farawa 1:28) Domin sun yi rashin biyayya, wannan mata da miji sun kasa cika duniya da iyalai masu adalci da za su kula da duniya da tsire-tsire da dabbobinta da kyau. Amma kasawarsu ba ta sa nufin Jehovah ya susuce ba. Shekaru dubbai daga baya, aka rubuta: “Allah; mai-sifanta duniya . . . , ya halicce ta ba wofi ba.” Ya “kamanta ta domin wurin zama.” Ba za ta halaka ba, amma “duniya kuwa ta dawwama.” (Ishaya 45:18; Mai-Wa’azi 1:4) Za a gano nufin Jehovah game da duniya: “Ƙudurina za ya tabbata, zan kuma cika dukan nufina.”—Ishaya 46:10.
Saboda haka, Shaidun Jehovah suka gaskata cewa duniya za ta kasance har abada, kuma dukan mutane rayayyu da matattu, da za su jitu da nufin Jehovah game da duniya mai kyau za su zauna a cikinta har abada. Dukan mutane sun gaji ajizanci daga Adamu da Hauwa’u, saboda haka dukan mutane masu zunubi ne. (Romawa 5:12) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Hakkin zunubi mutuwa ne.” “Masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba.” “Mai-rai da ya yi zunubi, shi za ya mutu.” (Romawa 6:23; Mai-Wa’azi 9:5; Ezekiel 18:4, 20) Ta yaya za su rayu kuma su sami albarka ta duniya? Sai ta hadayar fansa na Kristi Yesu, gama ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya bada gaskiya gareni, ko ya mutu, za shi rayu.” “Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29; 11:25; Matta 20:28.
Yaya wannan zai faru? An yi bayani cikin “bishara ta mulkin,” da Yesu ya soma yi lokacin da yake duniya. (Matta 4:17-23) A yau Shaidun Jehovah suna yin wa’azin bishara a hanya ta musamman.
[Taswira a shafi na 13]
ABIN DA SHAIDUN JEHOVAH SUKA GASKATA
Imani Dalilai na Nassi
Littafi Mai Tsarki Kalmar 2 Tim. 3:16, 17; 2 Bit. 1:20, 21;
Allah ne kuma gaskiya ne Yoh. 17:17
Littafi Mai Tsarki ya fi Mat. 15:3; Kol. 2:8
al’ada tabbaci Zab. 83:18; Isha. 26:4;
Sunan Allah Jehovah ne 42:8, AS; Fit. 6:3
Kristi Ɗan Allah ne, kuma Mat. 3:17; Yoh. 8:42; 14:28;
bai kai Allah ba 20:17; 1 Kor. 11:3; 15:28
Kristi ne na farko a cikin Kol. 1:15; R. Yoh. 3:14
abubuwa da Allah ya halitta
Kristi ya mutu a kan gungume Gal. 3:13; Ay. Man. 5:30
ne, ba a kan gicciya ba
Kristi ya ba da ransa na Mat. 20:28; 1 Tim. 2:5, 6;
mutum fansa domin mutane 1 Bit. 2:24
masu biyayya
Hadayar Kristi kaɗai ta isa Rom. 6:10; Ibran. 9:25-28
An tashi Kristi daga matattu 1 Bit. 3:18; Rom. 6:9;
ya zama ruhu mara mutuwa R. Yoh. 1:17, 18
Bayyanuwar Kristi a ruhu ne Yoh. 14:19; Mat. 24:3;
2 Kor. 5:16; Zab. 110:1, 2
Yanzu muna ‘lokaci na ƙarshe’ Mat. 24:3-14; 2 Tim. 3:1-5;
Mulki a ƙarƙashin Kristi zai Isha. 9:6, 7; 11:1-5;
yi sarautar duniya cikin Dan. 7:13, 14; Mat. 6:10
adalci da salama
Mulkin zai kawo yanayin Zab. 72:1-4; R. Yoh. 7:9, 10,
rayuwa mai kyau a duniya 13-17; 21:3, 4
Duniya ba za ta taɓa halaka Mai-Wa. 1:4; Isha. 45:18;
ba ko kuma jama’a su ƙare Zab. 78:69
Allah zai kawar da tsarin R. Yoh. 16:14, 16; Zeph. 3:8;
abubuwa na yanzu a yaƙin Dan. 2:44; Isha. 34:2;
Har–Magedon 55:10, 11
Za a halaka miyagu har abada Mat. 25:41-46; 2 Tass. 1:6-9
Mutane da Allah ya amince da Yoh. 3:16; 10:27, 28; 17:3;
su za su sami rai madawwami Mar. 10:29, 30
Hanya ɗaya ce kaɗai zuwa rai Mat. 7:13, 14; Afis. 4:4, 5
Mutuwa da ’yan Adam suke yi Rom. 5:12; 6:23
domin zunubin Adamu ne
Kurwan ’yan Adam ba ta Eze. 18:4; Mai-Wa 9:10;
wanzuwa bayan an mutu Zab. 6:5; 146:4; Yoh. 11:11-14
Jahannama kabari ne na mutane Ayu. 14:13 Dy; R. Yoh. 20:13, 14,
AV (hasiya)
Tashin matattu ne begen 1 Kor. 15:20-22; Yoh. 5:28, 29;
matattu 11:25, 26
Mutuwar da Adamu ya jawo za 1 Kor. 15:26, 54; R. Yoh. 21:4;
ta ƙare Isha. 25:8
Ƙaramin garke 144,000 ne Luka 12:32; R. Yoh. 14:1, 3;
kawai za su je sama su 1 Kor. 15:40-53;
kuma yi sarauta tare da R. Yoh. 5:9, 10
Kristi
An sake haifan 144,000 sun 1 Bit. 1:23; Yoh. 3:3;
zama ’ya’yan Allah na ruhu R. Yoh. 7:3, 4
An yi sabon alkawari da Irm. 31:31; Ibran. 8:10-13
Isra’ila ta ruhaniya
An gina ikilisiya ta Kristi Afis. 2:20; Ish. 28:16;
a kansa ne Mat. 21:42
Ga Jehovah ne kaɗai za a yi Yoh. 14:6, 13, 14; 1 Tim. 2:5
addu’a ta wurin Kristi
Bai kamata a yi amfani da Fit. 20:4, 5; Lev. 26:1;
sifoffi ba wajen bauta 1 Kor. 10:14; Zab. 115:4-8
Tilas ne a ƙi sihiri K. Sha 18:10-12; Gal. 5:19-21;
Lev. 19:31
Shaiɗan ne mai sarauta mara 1 Yoh. 5:19; 2 Kor. 4:4;
ganuwa a duniya Yoh. 12:31
Bai kamata Kirista ya yi 2 Kor. 6:14-17; 11:13-15;
hulɗa da ƙungiyoyin addinai Gal. 5:9; K. Sha 7:1-5
ba
Ya kamata Kirista ya kasance Yaƙ. 4:4; 1 Yoh. 2:15;
a ware daga duniya Yoh. 15:19; 17:16
Suna yin biyayya ga dokokin Mat. 22:20, 21; 1 Bit. 2:12; 4:15
mutane da ba su saɓa ba
da dokokin Allah
Karɓa ƙarin jini ta baki ko Far. 9:3, 4; Lev. 17:14;
ta jijiya karya dokokin Ay. Man. 15:28, 29
Allah ne
Dole ne a yi biyayya ga 1 Kor. 6:9, 10; Ibran. 13:4;
dokokin Littafi Mai Tsarki 1 Tim. 3:2; Mis. 5:1-23
a kan ɗabi’u
Isra’ila ce kaɗai aka ba K. Sha 5:15; Fit. 31:13;
dokar bin Assabaci kuma Rom. 10:4; Gal. 4:9, 10;
ta ƙare da Dokar Musa Kol. 2:16, 17
Ajin limamai da laƙabi na Mat. 23:8-12; 20:25-27;
musamman ba daidai ba ne Ayu. 32:21, 22
Mutum bai bayyana kawai ba
amma an halicce shi ne Isha. 45:12; Far. 1:27; Mat. 19:4
Yin baftisma ta wurin Mar. 1:9, 10; Yoh. 3:23;
nutsarwa gaba ɗaya cikin Ay. Man. 19:4, 5
ruwa yana nuna keɓe kai
Kiristoci da farin ciki suna Rom. 10:10; Ibran. 13:15;
ba da shaida ta gaskiyar Isha. 43:10-12
Nassi ga jama’a
[Akwati a shafi na 12]
Jehovah ya halicce . . . DUNIYA . . . ya sa mutane su kula da ita . . . su zauna har abada a cikinta