Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • dg kashi 2 pp. 3-4
  • Sashe na 2—Duniya Yantacce Daga Shan Wahala

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sashe na 2—Duniya Yantacce Daga Shan Wahala
  • Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Makamantan Littattafai
  • Sashe na 1—Allah Yana Kula Da Mu Kuwa Da Gaske?
    Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Dukan Wahala Za Ta Ƙare Ba Da Daɗewa Ba!
    Dukan Wahala Za Ta Ƙare Ba Da Daɗewa Ba!
  • Za Mu Amfana Idan Muka Jimre Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Me Ya Sa Allah Ya Kyale Wahala?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
dg kashi 2 pp. 3-4

Sashe na 2—Duniya Yantacce Daga Shan Wahala

1, 2. Wane ra’ayi wanda ya bambanta ne mutane dayawa suke da shi?

AMMA, miliyoyin mutane a dukan duniya fa suna da ra’ayin da ya bambanta ƙwarai. Sun tsinkaye gaba mai-ban al’ajibi ga mutane. Sun faɗi cewa a nan duniya bada jimawa ba za a samu duniya yantacce daga mugunta da shan wahala. Suna da gabagaɗin cewa bada jimawa ba za a kawas da abinda ke mumuna kuma a kafa wata sabuwar duniya sarai. Sun faɗi ma cewa an soma kafa tushin wannan sabuwar duniyar ko yanzu haka!

2 Mutanen nan sun gaskata cewa sabuwar duniyar zata yantu sarai daga yaƙi, zalunci, aika laifi, tarar shari’a, da talauci. Zata zama duniya ce mara ciwo, baƙinciki, zub da hawaye, har da mutuwa. A lokacin fa mutane zasu kai ga kamiltawa kuma su rayu har abada cikin farinciki bisa duniya ta aljanna. I fa, waɗanda sun mutu ma za a tashe su kuma su samu damar rayuwa har abada!

3, 4. Me yasa irin mutane nan suke da gabagaɗi game da ra’ayinsu?

3 Anya wannan ra’ayi na gaban mafalki ne kawai, tunanin son samu wani abu ne da baya yiwuwa? A’a, ba haka ba. Gama a kafe yake sosai bisa bangaskiya mai-ƙarfi cewa wannan Aljanna mai-zuwan tabbaci ne. (Ibraniyawa 11:⁠1) Me yasa suke da jin tabbaci haka? Domin maɗaukakki Mahaliccin dukan sarari ne ya yi alkawalin haka.

4 Game da alkawalan Allah fa, Littafi Mai-tsarki ya ce: “Babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda [“Jehovah,” New World Translation] Allahnku ya ambace su a kanku. Dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya ya sare daga ciki.” “Allah ba mutum ba ne, da zaya yi ƙarya . . . Ya faɗi, ba zaya aikata ba? Ya kuwa yi magana, ba zaya tabbatas ba?” “[“Jehovah,” NW ] mai-runduna ya rantse, ya ce, Hakika, yadda na sa tsammani, hakanan zaya faru; kamar yadda na nufa kuma, hakanan zaya tsaya.”​—⁠Joshua 23:14; Littafin Lissafi 23:19; Ishaya 14:⁠24.

5. Waɗanne tambayoyi ne ake bukatar amsawa?

5 Amma, idan nufin Allah ne ya kafa duniya ta aljanna yantacce daga shan wahala, me yasa ya kyale munanan abubuwa su auko daɗai? Me yasa ya jira har shekaru dubu shidda yanzu don ya gyara al’amura? Ashe waɗancan ƙarnuka na shan wahala zasu nuna cewa Allah baya kula da mu da gaske ba, ko kuwa cewa baya wanzu ba ma?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba