Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt 2 Bitrus 1:1-5:20
  • Yaƙub

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaƙub
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
Yaƙub

WASIƘAR YAƘUB

1 Daga Yaƙub, bawan Allah da na Ubangiji Yesu Kristi, zuwa ga kabilu goma sha biyun nan da suke a warwatse:

Ina gaisuwa!

2 ꞌYanꞌuwana, ku riƙa farin ciki sosai saꞌad da kuke shan wahaloli dabam-dabam. 3 Ku sani cewa wahalar nan da kuke sha takan gwada bangaskiyarku kuma tana sa ku jimre. 4 Amma bari jimrewarku ta cika aikinta, domin ku zama cikakku kuma marasa laifi a kowace hanya, ba tare da kun rasa wani abu ba.

5 Don haka, idan akwai wani a cikinku da ba shi da hikima, bari ya ci-gaba da roƙon Allah, gama Allah yana ba wa kowa hikima hannu sake ba tare da kunyatar da mutum* ba, kuma Allah zai ba wa mutumin abin da ya roƙa. 6 Amma bari ya ci-gaba da roƙo a cikin bangaskiya, ba tare da shakka ko kaɗan ba, gama wanda yake shakka yana kama da raƙumin ruwa, wanda iska take kaɗawa nan da can. 7 Hakika, kada mutumin nan ya yi tsammanin zai samu wani abu daga wurin Jehobah;* 8 shi mai zuciya biyu ne, wanda hankalinsa ba ya zama wuri ɗaya a dukan abubuwan da yake yi.

9 Amma bari ɗanꞌuwa matalauci ya yi farin ciki* don Allah ya ɗaukaka shi, 10 kuma bari mai arziki ya yi farin ciki don an ƙasƙantar da shi, gama mai arzikin zai shuɗe kamar fure. 11 Domin kamar yadda in rana ta fito, takan yi zafi sosai, kuma ta sa shuke-shuke su bushe sai furensu su fāɗi kuma kyaunsu ya ɓace, haka ma mai arziki zai ɓace yayin da yake neman arziki.

12 Mutumin da ya ci-gaba da jimre wa matsaloli, yana farin ciki, domin in Allah ya amince da shi, zai sami rawanin rai wanda Jehobah* ya yi alkawarin ba ma waɗanda suka ci-gaba da nuna masa ƙauna. 13 Saꞌad da mutum yake shan wahala, kada ya ce: “Allah ne yake jarraba* ni.” Domin ba za a iya jarrabtar Allah da ayyukan mugunta ba, shi kuma ba ya jarrabtar kowa. 14 Amma kowane mutum yakan fāɗi cikin jarraba saꞌad da shaꞌawoyinsa suka kama shi kamar tarko. 15 Kuma idan shaꞌawoyin nan suka yi tsanani,* sukan haifi zunubi; kuma in an yi zunubi, hakan yakan kai ga mutuwa.

16 Kada a yaudare* ku ꞌyanꞌuwana ƙaunatattu. 17 Kowace baiwa mai kyau da kowace cikakkiyar kyauta daga sama ne, suna saukowa ne daga wurin Uba wanda ya yi haske, wanda ba ya jujjuyawa ko kuma canjawa* kamar inuwa. 18 Bisa ga nufinsa, ya ba mu rai ta wurin kalmarsa ta gaskiya, don mu zama nunan fari na halittunsa.

19 Ku sani fa, ya ꞌyanꞌuwana ƙaunatattu: Dole kowa ya zama mai saurin ji, ba mai saurin magana ko mai saurin fushi ba, 20 gama fushin mutum ba zai sa shi ya aikata adalcin Allah ba. 21 Saboda haka, ku kawar da dukan halin ƙazanta da kowace irin mugunta, kuma cikin rashin zafin rai, ku amince da kalmar da Allah ya shuka a cikin zuciyarku da za ta iya cece ku.*

22 Amma, ku zama masu aikata kalmar Allah ba masu ji kawai ba, kuna yaudarar kanku da tunanin ƙarya. 23 Gama idan wani yana jin kalmar Allah kuma ba ya aikatawa, yana kama da mutumin da yake kallon fuskarsa a madubi. 24 Bayan ya kalli kansa kuma ya tafi, sai nan da nan ya manta shi wane irin mutum ne. 25 Amma duk wanda ya bincika cikakkiyar doka da ke ba wa mutum ꞌyanci, kuma ya ci-gaba da yin hakan,* shi ba wanda yake ji kuma ya manta ba ne, amma ya zama mai yin aikin Allah; kuma zai yi farin ciki a cikin abin da yake yi.

26 Idan wani yana tsammanin shi mai bauta wa Allah ne, amma ba ya iya kame harshensa, yana ruɗin kansa* ne, kuma bautarsa ta zama banza. 27 Irin bautar* da ke da tsabta kuma marar tabo a gaban Allahnmu, shi ne: kula da marayu da gwauraye saꞌad da suke cikin ƙunci, kuma mutum ya zama marar tabo a wannan duniyar.

2 ꞌYanꞌuwana, kuna ganin zai yiwu ku ci-gaba da ba da gaskiya ga Ubangiji Yesu Kristi mai ɗaukaka, yayin da kuke nuna bambanci? 2 Gama idan mutum da ya saka zoben zinariya a yatsunsa da kuma riguna masu tsada ya shigo taronku, kuma wani talaka da ya saka kaya masu datti ma ya shigo, 3 shin kuna nuna kun fi son wanda ya saka riguna masu tsada kuma ku ce, “Kai ka zauna a wurin nan mai kyau,” kuma ku gaya wa talakan cewa, “Kai ka ci-gaba da tsayawa,” ko kuma, “Ka zauna a kujerar can da ke ƙarƙashin matashin ƙafafuna”? 4 Idan haka kuke yi, ba kwa ganin kuna ɗaukan wasu da muhimmanci fiye da wasu, kuma ba kun zama alƙalai masu yanke mugayen hukunce-hukunce ke nan ba?

5 Ku saurara, ꞌyanꞌuwana ƙaunatattu. Ba Allah ne ya zaɓi waɗanda mutanen duniya suke ɗaukan su talakawa, don su zama masu arziki a bangaskiya, kuma su gāji Mulkin da ya yi alkawarin ba ma waɗanda suke ƙaunar sa ba? 6 Amma kun rena talakawa. Ba masu arziki ba ne suke wulaƙanta ku kuma suke kai ku* gaban kotuna ba? 7 Ba sun yi saɓo ga suna mai kyau da aka ba ku ba? 8 Idan kuna bin dokar sarki da ke cikin nassi wadda ta ce, “Dole ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kuna yin abin da ya dace. 9 Amma idan kuka ci-gaba da nuna bambanci, kuna yin zunubi ne, kuma an yanke muku hukunci bisa ga dokar a matsayin masu zunubi.

10 Gama idan wani yana bin dukan abubuwan da ke cikin Doka* amma ya taka ɗaya daga cikin su, ya taka dukan Dokar ke nan. 11 Domin wanda ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisa.” Yanzu idan ba ka yi zina ba amma ka yi kisa, ka zama mai taka doka. 12 Ku ci-gaba da yin magana da kuma yin abubuwa kamar waɗanda za a yi musu shariꞌa bisa dokar masu ꞌyanci.* 13 Gama wanda ba ya nuna jinƙai, za a yi masa shariꞌa ba tare da jinƙai ba. Jinƙai yana yin nasara a kan shariꞌa.

14 ꞌYanꞌuwana, wace riba ce mutum zai samu idan ya ce yana da bangaskiya amma ba ya nuna hakan ta ayyukansa? Bangaskiyar ba za ta iya ceton sa ba, ko ba haka ba? 15 Idan wasu ꞌyanꞌuwa maza ko mata ba su da rigunan sakawa da kuma isasshen abinci na yau da kullum, 16 duk da haka, wani a cikinku ya ce musu, “Ku sauka lafiya; Allah ya sa ku sami abin sakawa da abinci na yau da kullum,” amma ba ku ba su abin da suke bukata don jikinsu ba, wane amfani ne hakan zai kawo? 17 Saboda haka, bangaskiya da kanta ba tare da ayyuka ba, banza* ce.

18 Ban da haka, wani zai ce: “Kana da bangaskiya, ni kuma ina da ayyuka. Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin ayyukana.” 19 Ka ba da gaskiya cewa akwai Allah ɗaya, ko ba haka ba? Hakan ya dace. Ko aljanu ma sun gaskata kuma sun yi rawan jiki. 20 Kai marar hikima, kana so in tabbatar maka cewa bangaskiya ba tare da ayyuka ba banza ce? 21 Ba an ɗauki Ibrahim ubanmu a matsayin mai adalci ta wurin ayyukansa ba, bayan ya miƙa ɗansa Ishaku a kan bagade? 22 To, ka ga yadda bangaskiyarsa take tafiya tare da ayyukansa kuma bangaskiyarsa ta zama cikakkiya ta wurin ayyukansa, 23 kuma ta hakan aka cika nassin da ya ce: “Ibrahim ya ba da gaskiya ga Jehobah,* kuma hakan ya sa an ɗauke shi a matsayin mai adalci,” shi ya sa aka kira shi abokin Jehobah.*

24 Kun ga cewa ayyuka suna sa a ɗauki mutum a matsayin mai adalci, ba bangaskiya kawai ba. 25 Haka ma, ba an ɗauki Rahab karuwar nan a matsayin mai adalci ta wurin ayyukanta bayan ta karɓi masu leƙen asirin da hannu bibbiyu, kuma ta sallame su ta wata hanya ba? 26 Hakika, kamar yadda jiki matacce ne idan ba shi da numfashi,* haka ma bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.

3 ꞌYanꞌuwana, kada da yawa daga cikinku su zama malamai, domin mun san cewa za a yi mana shariꞌa mafi tsanani. 2 Gama dukanmu mukan yi kuskure sau da yawa. Idan akwai wani da ba ya yin kuskure a abin da yake faɗa, shi cikakke ne, kuma yana iya kame dukan jikinsa. 3 Idan mun saka wa dawakai linzami a baki don su yi mana biyayya, za mu kuma iya ja-goranci dukan jikinsu. 4 Ku kuma dubi jiragen ruwa: Suna da girma sosai, kuma iska mai ƙarfi ne yake tura su, amma da ɗan ƙaramin sanda ne matuƙin jirgin yake juye jirgin zuwa duk inda yake so ya je.

5 Haka ma, harshe ɗan ƙarami ne a cikin gaɓoɓin jiki, amma duk da haka yana yin taƙama sosai. Ku dubi yadda ƙaramar wuta take iya ƙone daji mai girma ƙurmus! 6 Harshe ma wuta ne. A cikin gaɓoɓin jikinmu, harshe ne yake cike da rashin adalci, gama yana ƙazantar da dukan jiki, kuma ya hallaka rayuwar mutum, kuma yana hallaka abu kamar wutar Gehenna.* 7 Gama ꞌyanꞌadam suna iya shawo kan dabbobin daji, da tsuntsaye, da dabbobi masu rarrafe, da dabbobin ruwa, kuma sun yi hakan. 8 Amma ba ɗanꞌadam da zai iya shawo kan harshe. Yana da wuyan kamewa, yana da haɗari, kuma yana cike da guba mai kisa. 9 Da harshe muke yabon Jehobah* Uba, da shi ne kuma muke zagin mutane, waɗanda aka yi su “cikin kamannin Allah.” 10 Da baki ake yabo, da shi ne kuma ake zagi.

ꞌYanꞌuwana, bai dace abubuwa su faru haka ba. 11 Zai yiwu ruwa mai kyau da ruwa mai ɗaci su fito daga maɓuɓɓuga guda ɗaya ne? 12 ꞌYanꞌuwana, itacen ɓaure zai iya ba da ꞌyaꞌyan zaitun ne, ko kuma itatuwan inabi su ba da ꞌyaꞌyan ɓaure? Haka ma, ba zai yiwu ruwa mai kyau ya fito daga inda ruwan gishiri yake fitowa ba.

13 Wane ne a tsakaninku yake da hikima kuma yake fahimtar abubuwa? Sai ya nuna hakan ta wurin halinsa, kuma ya yi kome cikin rashin zafin rai wanda ake samu daga hikima. 14 Amma idan a zuciyarku kuna da kishi mai tsanani da son faɗa,* kada ku riƙa yin taƙama da kuma ƙarya a kan gaskiya. 15 Wannan ba hikima da take saukowa daga sama ba ce; amma ta duniya ce; ta waɗanda suke bin shaꞌawoyin jikinsu, da kuma ta aljanu. 16 Gama a duk inda akwai kishi da son kai,* za a kuma samu rikicewa da kowane mugun abu a wurin.

17 Amma hikimar da take saukowa daga sama, da farko tana sa mutum ya kasance da tsabta, saꞌan nan tana sa mutum ya yi abin da zai kawo salama, tana sa mutum kada ya nace a kan raꞌayinsa, tana sa mutum ya kasance a shirye ya yi biyayya, tana da yawan jinƙai da ꞌyaꞌya masu kyau, ba ta nuna bambanci, kuma ba ta yin munafunci. 18 Waɗanda suke yin abin da ke kawo salama, za su yi shuki a yanayi na salama kuma su girbi ꞌyaꞌyan adalci.

4 Mene ne ke jawo faɗa da jayayya a tsakaninku? Shin ba shaꞌawoyin jikinku waɗanda suke yaƙi a cikinku* ne ke jawo hakan ba? 2 Kuna shaꞌawar samun abubuwa, duk da haka ba ku samu ba. Kun ci-gaba da tsanan* mutane, da kwaɗayin abubuwan mutane, duk da haka ba ku samu ba. Kun ci-gaba da faɗa da jayayya. Ba ku da abu domin ba kwa roƙon kome. 3 Saꞌad da kuka roƙa kuma, ba kwa samuwa, domin kuna roƙo ne da mugun nufi, kukan yi amfani da su, don ku gamsar da shaꞌawoyin jikinku.

4 Ku marasa aminci,* ba ku sani cewa yin abota da duniya yana sa mutum ya zama abokin gāban Allah ba? Saboda haka, duk wanda yake so ya zama abokin duniya, yana mai da kansa abokin gāban Allah. 5 Ko kuna tsammanin cewa a banza ne nassi ya ce: “Zuciyarmu* da ke sa mu yi kishin mutane, tana sa mu yi tsananin shaꞌawar abubuwa dabam-dabam”? 6 Amma alherin Allah a gare mu yana sa mu guji shaꞌawoyin nan. Shi ya sa kalmar Allah ta ce: “Allah yana gāba da masu girman kai, amma yana yin alheri ga masu sauƙin kai.”

7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah; amma ku yi gāba da Ibilis, shi kuwa zai guje muku. 8 Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku. Ya ku masu zunubi, ku tsabtace hannayenku, kuma ku tsabtace zukatanku, ya ku masu zuciya biyu. 9 Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki, kuma ku yi kuka. Bari dariyarku ta zama makoki, kuma farin cikinku ya zama baƙin ciki. 10 Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Jehobah,* shi kuwa zai ɗaukaka ku.

11 ꞌYanꞌuwa, ku daina yin magana marar kyau game da juna. Duk wanda ya yi magana marar kyau game da wani ɗanꞌuwa, ko ya shariꞌanta ɗanꞌuwansa, ya yi magana marar kyau game da doka ke nan, kuma ya shariꞌanta doka. Gama idan ka shariꞌanta doka, kai ba mai bin doka ba ne, amma alƙali. 12 Allah ne kaɗai Mai Ba da Doka da kuma Alƙali, shi ne wanda yake da ikon ba da ceto ko ya hallaka mutum. Amma, wane ne kai da kake shariꞌanta maƙwabcinka?

13 Ku saurara, ku da kuke cewa: “Yau ko gobe za mu yi tafiya zuwa gari kaza, kuma za mu yi shekara ɗaya a wurin, za mu yi kasuwanci kuma mu ci riba,” 14 amma ba ku san yadda rayuwarku za ta kasance gobe ba. Gama ku kamar hazo ne da ke fitowa na ɗan lokaci sai anjima ya ɓace. 15 A maimakon haka, ya kamata ku ce: “Idan nufin Jehobah* ne, za mu rayu, kuma za mu yi kaza da kaza.” 16 Amma kuna fahariya, kuna kuma yawan taƙama game da kanku. Duk irin taƙamar nan ba shi da kyau. 17 Don haka, idan wani ya san yadda zai yi abin da ya dace, amma bai yi ba, hakan zunubi ne a gare shi.

5 Ku masu arziki, ku saurara, ku yi kuka da makoki don azabar da za ta faɗo muku. 2 Arzikinku ya ruɓe, kuma gara sun cinye rigunanku. 3 Zinariya da azurfarku sun yi tsatsa, kuma tsatsarsu za ta zama shaida a kanku, za ta kuma cinye jikinku. Abin da kuka tara zai zama kamar wuta a kwanakin ƙarshe. 4 Ga shi! Maꞌaikata da suka girbe amfanin gonakinku sun ci-gaba da kuka, domin kun ƙi ku biya su, kuma Jehobah* mai runduna ya ji kukan neman taimako da masu girbin suke yi. 5 Kun yi rayuwar jin daɗi da kuma gamsar da kanku a duniya. Kun ci kun yi ƙiba* kuna jiran ranar yanka. 6 Kun hukunta mai adalci kuma kun kashe shi. Shi ya sa yake* gāba da ku.

7 ꞌYanꞌuwana, ku riƙa haƙuri har sai lokacin da Ubangiji zai dawo. Manomi yakan ci-gaba da jira har sai lokacin da gonarsa za ta ba da amfani mai kyau, cikin haƙuri yakan jira har lokacin da za a yi ruwan sama na farko da na ƙarshe. 8 Ku ma ku riƙa yin haƙuri; ku sa zukatanku su yi ƙarfi, domin lokacin da Ubangiji zai dawo ya yi kusa.

9 ꞌYanꞌuwa, kada ku yi gunaguni game da juna, domin kada a yi muku shariꞌa. Ga shi! Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa. 10 ꞌYanꞌuwana, ku bi misalin annabawan da suka yi magana a cikin sunan Jehobah,* sun sha wahala sosai, amma sun ci-gaba da jimrewa. 11 Ga shi! Mukan ɗauki waɗanda suka jimre a matsayin masu farin ciki.* Kun ji game da jimrewar Ayuba, kun kuma ga abin da Jehobah* ya yi daga baya, cewa Jehobah* mai ƙauna ne sosai,* da kuma mai yawan jinƙai.

12 Fiye da kome ꞌyanꞌuwana, ku daina rantsuwa, ko da sama, ko da duniya, ko kuma da wani abu. Amma bari “E” naku ya zama e, kuma “Aꞌa” ta zama aꞌa, don kada Allah ya yi muku shariꞌa.

13 Akwai wanda yake shan wahala a tsakaninku ne? Bari ya ci-gaba da yin adduꞌa. Akwai wani mai murna a cikinku ne? Bari ya rera waƙoƙin yabo. 14 Akwai mai rashin lafiya a tsakaninku ne? Bari ya kira dattawan ikilisiya don su yi masa adduꞌa, su shafa masa māi cikin sunan Jehobah.* 15 Irin wannan adduꞌar da aka yi cikin bangaskiya, za ta sa marar lafiyar* ya samu sauƙi, kuma Jehobah* zai warkar da shi. Ƙari ga haka, idan ya yi zunubai, za a gafarta masa.

16 Saboda haka, ku gaya wa juna zunubanku kuma ku riƙa yi wa juna adduꞌa, domin a warkar da ku. Roƙon da mai adalci yake yi ga Allah yana da iko, kuma zai iya taimaka wa mutane sosai. 17 Iliya mutum ne kamar mu, duk da haka, saꞌad da ya yi adduꞌa da dukan zuciyarsa don kada a yi ruwan sama, ba a yi ruwan sama a ƙasar ba na shekara uku da wata shida. 18 Bayan haka, ya sake yin adduꞌa, sai aka yi ruwan sama kuma ƙasa ta ba da amfaninta.

19 ꞌYanꞌuwana, idan wani a cikinku ya bar bin hanyar gaskiya, kuma wani ya taimaka masa ya dawo, 20 sai ku sani cewa duk wanda ya sa mai zunubi ya daina mugayen abubuwan da yake yi, zai cece shi daga mutuwa, kuma Allah zai gafarta masa zunubansa masu yawa.

Ko kuma “ba tare da gori.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

A yaren Girka, “taƙama.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ko kuma “gwada.”

A yaren Girka, “yi ciki.”

Ko kuma “ruɗe.”

Ko kuma “matsawa.”

Ko kuma “rayukanku.” A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

Ko kuma “ya nace da bin ta.”

A yaren Girka, “zuciyarsa.”

Ko kuma “addinin.”

Ko kuma “jan ku zuwa.”

Ko kuma “Dokar Musa.”

A yaren Girka, “dokar ꞌyanci.”

Ko kuma “matacciya.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

A yaren Girka, “ruhu.”

Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Yana kuma iya nufin, “kuna son abin da zai amfane ku kawai.”

Ko kuma “gardama.”

A yaren Girka, “gaɓoɓinku.”

A yaren Girka, “kashe.”

A yaren Girka, “mazinata.”

A yaren Girka, “Ruhun.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

A yaren Girka, “kun sa zukatanku sun yi ƙiba kamar dabbobi.”

Yana kuma iya nufin, “Allah.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ko kuma “albarka.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ko kuma “mai jin tausayi ne sosai.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Yana kuma iya nufin, “wanda ya gaji.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba