WASIƘA ZUWA GA IBRANIYAWA
1 A zamanin dā, Allah ya yi magana da kakanninmu a lokuta da yawa, da kuma ta hanyoyi da yawa ta wurin annabawa. 2 Amma a wannan lokacin,* yana yin magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa a matsayin wanda zai gāji kome, kuma ta wurinsa ne ya yi zamanai.* 3 Shi ne hasken da ke nuna ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamannin Allah, kuma yana riƙe kome ta wurin ikon kalmarsa. Bayan ya tsabtace zunubanmu, ya zauna a hannun daman Allah Mai Daraja da ke sama. 4 Ta hakan ya fi malaꞌiku, da yake ya sami sunan da ya fi nasu ɗaukaka.
5 Alal misali, wanne ne daga cikin malaꞌiku wanda Allah ya taɓa ce masa: “Kai ɗana ne; yau na zama babanka”? Da kuma: “Zan zama baban shi, shi kuma zai zama ɗana”? 6 Amma saꞌad da ya sake kawo Ɗan farinsa duniya, ya ce: “Kuma bari dukan malaꞌikun Allah su rusuna* masa.”
7 Ƙari ga haka, ya ce game da malaꞌikun: “Ya mai da malaꞌikunsa ruhohi, kuma ya mai da masu yi masa hidima* harshen wuta.” 8 Amma game da Ɗan, ya ce: “Allah ne kujerar mulkinka har abadan abadin, kuma sandar mulkinka na adalci ne. 9 Kana ƙaunar adalci, kuma ka tsani mugunta. Shi ya sa Allah, wato Allahnka, ya naɗa ka da māi na ɗaukaka fiye da abokanka.” 10 Kuma: “Da farko, Ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma, aikin hannunka ne. 11 Za su shuɗe, amma kai kana nan; kuma dukansu za su koɗe kamar riga, 12 za ka nannaɗe su kamar riga, kuma za ka canja su kamar yadda mutum yake canja riga. Amma kai ba za ka canja ba, kuma shekarunka ba za su taɓa kai ƙarshe ba.”
13 Gama wane malaꞌika ne Allah ya taɓa gaya masa cewa: “Ka zauna a hannun damana har sai na sa abokan gābanka su zama matashin ƙafafunka”? 14 Ba dukansu ne ruhohi don hidima mai tsarki* ba, waɗanda aka aike su su yi hidima ga waɗanda za su gāji ceto ba?
2 Saboda haka, ya kamata mu ƙara mai da hankali ga abubuwan da muka ji, domin kada mu taɓa kaucewa daga hanya. 2 Gama idan abin da aka faɗa ta wurin malaꞌiku ya tabbata, kuma an hukunta kowane zunubi da rashin biyayya bisa ga adalci, 3 to, ta yaya za mu tsira idan muka yi watsi da ceto mai girma kamar haka? Gama an fara maganar ceton ta wurin Ubangijinmu, kuma waɗanda suka ji shi sun tabbatar mana cewa hakan gaskiya ne. 4 Allah ma ya ba da shaida ta wurin alamu, da abubuwan ban mamaki, da manyan ayyuka dabam-dabam, da kuma ruhu mai tsarki da ya rarraba wa bayinsa bisa ga nufinsa.
5 Gama ba malaꞌiku ne Allah ya sa su yi mulkin duniyar da ke zuwa ba, wato duniyar da muke maganar ta. 6 A wani wuri, wani ya ba da shaida cewa: “Wane ne mutum da ka damu da shi, ko kuma ɗan mutum da kake kula da shi? 7 Ka ba shi iko wanda da kaɗan ne na malaꞌiku ya fi shi; ka girmama shi da ɗaukaka da daraja, ka naɗa shi ya yi iko a kan dukan aikin hannunka. 8 Ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” Ta wurin sa kome a ƙarƙashinsa, babu wani abu da Allah bai sa a ƙarƙashinsa ba. Ko da yake a yanzu, ba kome ne yake a ƙarƙashinsa ba tukuna. 9 Amma mun ga Yesu, wanda aka mai da shi ya zama da iko wanda da kaɗan ne na malaꞌiku ya fi shi. Yanzu an girmama shi da ɗaukaka da daraja domin ya sha wahala har ya mutu, kuma saboda alherin Allah ne ya mutu domin kowa.
10 Gama ya dace cewa wanda dominsa ne kuma ta wurinsa dukan abubuwa suka wanzu, ya sa Shugaba mai ba su ceto ya zama cikakke ta wurin shan wahala domin ya kawo ma ꞌyaꞌya da yawa ɗaukaka. 11 Gama wanda yake tsarkakewa da kuma waɗanda ake tsarkake su, suna da uba ɗaya, shi ya sa ba ya jin kunyar kiran su ꞌyanꞌuwa, 12 kamar yadda ya faɗa cewa: “Zan yi shelar sunanka ga ꞌyanꞌuwana; a cikin ikilisiya zan yabe ka da waƙa.” 13 Ya kuma ce: “Zan dogara gare shi.” Ya sake cewa: “Ga ni nan! Tare da ƙananan yaran da Jehobah* ya ba ni.”
14 Saboda haka, da yake “ƙananan yaran” nama da jini ne, shi ma ya zama nama da jini a dā, domin ta wurin mutuwarsa, ya iya hallaka wanda yake da ikon jawo mutuwa, wato Ibilis, 15 kuma ta hakan ya iya ꞌyantar da dukan waɗanda suka zama bayi ga tsoron mutuwa a dukan rayuwarsu. 16 A gaskiya, yana taimaka wa zuriyar Ibrahim ne, ba malaꞌiku ba. 17 Dalilin nan ne ya sa ya bukaci ya zama kamar “ꞌyanꞌuwansa” ta kowace hanya, domin ya zama shugaban firistoci mai jinƙai da aminci a hidimarsa ga Allah. Ya yi hakan don ya ba da ransa a matsayin hadayar da ke sasanta mutane da Allah saboda zunubansu. 18 Da yake shi da kansa ya sha wahala saꞌad da ake gwada shi, zai iya taimaka ma waɗanda ake gwada su.
3 Saboda haka, ꞌyanꞌuwa tsarkaka, waɗanda suka samu gayyatar nan na zuwa sama, ku yi tunani a kan manzon nan da shugaban firistocin nan da muka ba da gaskiya gare shi, wato Yesu. 2 Ya kasance da aminci ga Wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ma ya yi ga dukan gidan Allah. 3 An ga cewa ya* cancanci daraja fiye da Musa, tun da yake wanda ya gina gida ya fi gidan daraja. 4 Hakika, kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma Allah ne ya gina kome. 5 Musa ya kasance da aminci a matsayinsa na bawa ga dukan gidan Allah kuma hakan ya zama shaida na abubuwan da za a faɗa a nan gaba, 6 amma Kristi ya kasance da aminci a matsayinsa na ɗa a gidan Allah. Mu ne gidansa, idan dai mun ci-gaba da riƙe ꞌyancin yin magana da muke da shi da kyau, da kuma begen da muke taƙama da shi har zuwa ƙarshe.
7 Saboda haka, kamar yadda ruhu mai tsarki ya ce, “A yau in kuka saurari muryarsa, 8 kada ku sa zukatanku su yi tauri kamar yadda kakanninku suka yi kuma suka ɓata mini rai sosai, a ranar da suka gwada ni a daji. 9 A dajin, kakanninku sun gwada ni, duk da cewa sun ga ayyukana na shekaru arbaꞌin. 10 Shi ya sa na yi fushi da wannan tsarar kuma na ce: ‘A kullum suna yin abubuwa marasa kyau a zukatansu, kuma har yanzu ba su zo ga sanin hanyoyina ba.’ 11 Sai na yi fushi kuma na rantse cewa: ‘Ba za su shiga cikin hutuna ba.’”
12 Ku yi hankali ꞌyanꞌuwa, don kada wani a cikinku ya zama da mugun zuciya marar bangaskiya ta wurin juya baya ga Allah mai rai; 13 amma ku ci-gaba da ƙarfafa juna kowace rana, muddin dai ana kiran sa “Yau,” domin kada ikon da zunubi yake da shi na ruɗin mutane ya sa zuciyar wani daga cikinku ta yi tauri. 14 Gama za mu samu abin da Kristi ya samu idan muka riƙe tabbacin nan da muke da shi tun farko da ƙarfi, har zuwa ƙarshe. 15 Kamar yadda aka faɗa, “A yau in kuka saurari muryarsa, kada ku sa zukatanku su yi tauri kamar yadda kakanninku suka yi kuma suka ɓata mini rai sosai.”
16 Gama su wane ne suka ji kuma suka ɓata masa rai sosai? Shin ba dukan waɗanda suka bar Masar a ƙarƙashin ja-gorancin Musa ba ne? 17 Ƙari ga haka, su wane ne Allah ya yi fushi da su har na shekaru arbaꞌin? Shin ba waɗanda suka yi zunubi kuma suka mutu a daji ba ne? 18 Kuma su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su shiga cikin hutunsa ba? Shin ba waɗanda suka yi rashin biyayya ba ne? 19 Don haka, mun ga cewa sun kasa shiga ne saboda rashin bangaskiyarsu.
4 Saboda haka, da yake alkawarin shiga cikin hutunsa yana nan har yanzu, bari mu yi hankali don kada wani a cikinku ya kasa shiga. 2 Gama mu ma mun ji labari mai daɗi da aka yi mana shelar sa kamar yadda aka yi musu; amma abin da suka ji bai amfane su ba, domin ba su kasance da bangaskiya mai ƙarfi kamar bangaskiyar waɗanda suka saurara ba. 3 Gama mu da muka ba da gaskiya mun shiga cikin hutun, kamar yadda ya faɗa cewa: “Sai na yi fushi kuma na rantse cewa, ‘Ba za su shiga cikin hutuna ba,’” ko da yake ya gama ayyukansa tun farkon duniya.* 4 Gama a wani wuri ya ce game da rana ta bakwai: “Kuma Allah ya huta daga dukan ayyukansa a rana ta bakwai,” 5 kuma a nan ya sake cewa: “Ba za su shiga cikin hutuna ba.”
6 Saboda haka, tun da yake akwai wasu mutanen da suka rage da za su shiga cikin hutun, kuma waɗanda aka fara yi musu shelar labari mai daɗi ba za su shiga ba saboda rashin biyayya, 7 ya sake keɓe ranar da ya kira “Yau” a cikin zaburar Dauda bayan dogon lokaci, kamar yadda wasiƙar nan ta faɗa a baya, “A yau in kuka saurari muryarsa, kada ku sa zukatanku su yi tauri.” 8 Gama da a ce Joshuwa ya kai su wurin hutawa, da Allah bai yi magana game da wata rana bayan hakan ba. 9 Don haka, akwai ranar hutu da ke kama da hutun assabaci da ya rage don mutanen Allah. 10 Gama mutumin da ya shiga cikin hutun Allah shi ma ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah ya huta daga nasa ayyuka.
11 Don haka, bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu shiga cikin wannan hutun domin kada wani ya bi misalin waɗanda ba su yi biyayya ba. 12 Gama kalmar Allah tana da rai da iko, kuma tana ci sosai fiye da* kowane takobi mai baki biyu,* takan soki mutum ta shiga ciki-ciki ta raba rai* da ruhu,* ta raba tsakanin gaɓoɓi da ɓargo,* kuma tana iya gane tunani da kuma nufi da ke cikin zuciya. 13 Kuma babu halitta da take ɓoye daga fuskarsa, amma kome yana a buɗe, a fili kuma a idanun wanda dole ne mu ba shi lissafin aikinmu.
14 Saboda haka, da yake muna da shugaban firistoci mai girma wanda ya shiga sama, wato Yesu Ɗan Allah, bari mu ci-gaba da yin shelar bangaskiyarmu a gare shi. 15 Gama shugaban firistocin da muke da shi ba wanda ba zai iya tausaya mana don kasawarmu ba ne, amma wanda aka gwada shi ta kowace hanya ne kamar yadda aka gwada mu, duk da haka bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka, bari mu matso kusa da kujerar mulki ta alheri tare da ꞌyancin yin magana, domin mu samu jinƙai, mu kuma samu alheri da zai taimaka mana a lokacin da ya dace.
5 Gama kowane shugaban firistoci da aka zaɓa daga cikin mutane, an naɗa shi ne domin ya yi hidima ga Allah a madadin mutanen, domin ya iya ba da kyaututtuka da hadayu don zunubai. 2 Tun da yake shi ma yana da nasa kasawa, yana iya bi da marasa sani da waɗanda suka kauce hanya cikin tausayi,* 3 kuma saboda kasawar nan tasa dole ne ya miƙa hadayu don zunubansa kamar yadda yake yi don mutane.
4 Mutum ba ya zaɓan kansa don ya yi aikin nan mai daraja, amma zai iya samun aikin nan ne kawai idan Allah ya zaɓe shi, kamar yadda ya zaɓi Haruna. 5 Haka ma Kristi bai ɗaukaka kansa ta wurin zama shugaban firistoci ba, amma ya sami ɗaukakar ce daga wurin Wanda ya ce masa: “Kai ɗana ne; yau na zama babanka.” 6 Ya kuma ce a wani wuri, “Kai firist ne har abada kamar Melkizedek.”
7 A lokacin da Kristi yake duniya, ya yi adduꞌoꞌi da kuma roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani da hawaye ga Wanda zai iya cece shi daga mutuwa, kuma an saurare shi domin yana tsoron Allah. 8 Ko da yake shi Ɗan Allah ne, ya koyi biyayya daga wahalolin da ya sha. 9 Kuma bayan da aka mai da shi cikakke, ya zama wanda zai ba da ceto na har abada ga dukan waɗanda suke masa biyayya, 10 domin Allah ya riga ya naɗa shi a matsayin shugaban firistoci kamar Melkizedek.
11 Muna da abubuwa da yawa da za mu faɗa game da shi, amma yana da wuya mu bayyana muku domin ba ku da saurin ganewa. 12 Ko da yake a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, har yanzu kuna bukatar wanda zai sake koya muku abubuwa na farko da kuka koya daga kalmar Allah, kuma kun koma kun zama waɗanda suke bukatar madara maimakon abinci mai kauri. 13 Gama duk wanda ya ci-gaba da shan madara bai san kome game da koyarwar adalci ba, domin shi ƙaramin yaro ne. 14 Amma abinci mai kauri na waɗanda suka manyanta ne, kuma ta wurin amfani da shi, sun iya horar da hankalinsu* don su iya bambanta tsakanin abu mai kyau da marar kyau.
6 Saboda haka, yanzu da muka sami ci-gaba daga abubuwan da muka koya da farko game da Kristi, bari mu yi ƙoƙari mu manyanta, kada mu soma daga farko kuma, wato daga koyarwa irin su tuba daga ayyuka marasa kyau da kuma bangaskiya ga Allah, 2 da koyarwa a kan baftisma, da sa hannaye a kan mutane, da tashin matattu da kuma hukunci na har abada. 3 Kuma za mu ci-gaba da manyanta idan Allah ya yarda.
4 Amma game da waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta daga sama, kuma suka sami ruhu mai tsarki, 5 waɗanda suka ɗanɗana kalma mai kyau ta Allah da kuma abubuwa masu kyau da za a ba wa* zamani* mai zuwa, 6 duk da haka sun kauce wa hanya, ba zai yiwu a sake sa su tuba ba, domin sun sake rataye Ɗan Allah a kan gungume da kansu kuma sun kunyatar da shi a gaban jamaꞌa. 7 Gama ƙasa takan sami albarka daga wurin Allah yayin da take shan ruwan sama da ke saukowa a kanta kullum, kuma ta haifar da tsire-tsire da ke ba da amfani ga waɗanda suke nome ta. 8 Amma idan tana haifar da ƙayoyi da mugayen ciyayi, ba ta da wani amfani kuma an kusa a laꞌanta ta, a ƙarshe kuma za a ƙone ta.
9 Amma ku kam, ꞌyanꞌuwana ƙaunatattu, muna da tabbacin cewa kun fi waɗanda suka kauce wa hanya, kuma kuna yin abubuwan da za su sa ku samu ceto, ko da yake muna magana haka. 10 Gama Allah ba marar adalci ba ne da zai manta da aikin da kuka yi, da kuma ƙaunar da kuka nuna ga sunansa ta wurin hidimar da kuke yi wa tsarkaka da yadda kuke ci-gaba da yi musu hidima. 11 Amma muna so kowannenku ya ci-gaba da yin ƙwazo haka domin ku iya kasancewa da cikakken tabbaci game da begenku har zuwa ƙarshe, 12 domin kada ku zama masu ƙiwuya, amma ku yi koyi da waɗanda suka sami abin da aka yi alkawarin sa ta wurin bangaskiya da kuma haƙuri.
13 Gama saꞌad da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba zai iya yin rantsuwa da wani da ya fi shi ba, ya yi rantsuwa da kansa, 14 yana cewa: “Hakika, zan albarkace ka kuma zan sa zuriyarka ta yi yawa.” 15 Don haka, bayan da Ibrahim ya yi haƙuri, ya sami wannan alkawarin. 16 Mutane sukan rantse da wanda ya fi su girma, kuma rantsuwarsu takan kawo ƙarshen kowace gardama, domin rantsuwar takan tabbatar da abin da suka faɗa. 17 Haka ma, saꞌad da Allah ya yanke shawarar nuna ma waɗanda za su gāji alkawarin dalla-dalla cewa nufinsa marar canjawa ne, ya tabbatar da hakan ta wurin yin rantsuwa, 18 domin ta wurin abubuwa biyu marasa canjawa waɗanda suka sa ba zai yiwu Allah ya yi ƙarya ba, mu da muka gudu zuwa mafaka, za mu iya samun ƙarfafa don mu riƙe begen nan da aka sa a gabanmu da ƙarfi sosai. 19 Muna da wannan bege da ke kama da ƙugiya* da ke riƙe rayukanmu,* begen tabbatacce ne kuma mai ƙarfi, shi ne kuma yake shigar da mu ciki har bayan labulen, 20 wurin da Yesu ya riga mu shiga, kuma ya shiga ne a madadinmu, ya kuma zama shugaban firistoci har abada kamar Melkizedek.
7 Gama wannan Melkizedek sarkin Salem, firist na Allah Mafi Ɗaukaka, ya haɗu da Ibrahim bayan da Ibrahim ya hallaka sarakuna, kuma ya albarkace shi, 2 Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya cikin goma na kome. Da farko, sunansa yana nufin “Sarkin Adalci,” da kuma sarkin Salem, wato, “Sarkin Salama.” 3 Ba shi da mahaifi, ba shi da mahaifiya, kuma ba a san daga zuriyar da ya fito ba, ba a san lokacin da aka haife shi ko kuma lokacin da ya mutu ba, da yake an mai da shi kamar Ɗan Allah, ya ci-gaba da zama firist har abada.
4 Ku dubi irin girman da mutumin nan yake da shi, har Ibrahim wanda shi ne kakan kakanninmu ya ba shi kashi ɗaya cikin goma na kaya mafi kyau* da ya kwashe daga yaƙi. 5 Hakika, bisa ga Doka,* an ba da umurni ga ꞌyaꞌyan Lawi waɗanda aka naɗa su firistoci su karɓi zakka daga wurin mutane, wato daga wurin ꞌyanꞌuwansu, ko da yake ꞌyanꞌuwansu ma daga zuriyar Ibrahim ne. 6 Amma mutumin nan wanda bai fito daga zuriyarsu ba ya karɓi zakka daga Ibrahim kuma ya albarkaci wanda aka yi masa alkawuran. 7 Yanzu ba shakka wanda ya sa albarkar ya fi wanda ya karɓi albarkar girma. 8 A wancan ɓangaren, waɗanda suke mutuwa ne suka karɓi zakka, amma a wannan ɓangaren, mutumin da aka ba da shaida a kansa cewa zai ci-gaba da rayuwa ne ya karɓi zakkar. 9 Kuma za a iya cewa ko Lawi ma da yake karɓan zakka, ya biya zakka ta wurin Ibrahim, 10 domin daga baya an haifi Lawi a zuriyar Ibrahim wanda ya haɗu da Melkizedek.
11 Da a ce firistoci na zuriyar Lawi za su iya sa mutane su zama cikakku* (domin aikin da firistoci suke yi sashe ne na Dokar da aka ba wa mutanen), da me zai sa a bukaci zuwan wani firist dabam wanda aka ce zai zama kamar Melkizedek ba kamar Haruna ba? 12 Da yake an canja tsarin firistocin, ya zama dole a canja Dokar ma. 13 Gama mutumin da aka faɗi abubuwan nan game da shi ya fito ne daga wata kabila dabam, kuma babu wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade. 14 A bayyane yake cewa Ubangijinmu ya fito daga kabilar Yahuda, amma Musa bai ce kome game da firistoci da za su fito daga kabilar ba.
15 Hakan ya ƙara bayyana sosai saꞌad da wani firist da ke kama da Melkizedek ya fito, 16 wanda ya zama firist, ba domin kabilar da ya fito kamar yadda doka ta ce ba, amma domin ikon da Allah ya ba shi na rai da ba za a iya hallaka ba. 17 Gama an ba da shaida game da shi cewa: “Kai firist ne har abada kamar Melkizedek.”
18 Saboda haka, an kawar da Doka ta dā domin ba ta da ƙarfi kuma ba ta da amfani. 19 Gama babu abin da Dokar ta sa ya zama cikakke, amma bege mai kyau da aka ba mu ne ya sa abubuwa suka zama cikakku, kuma hakan yana sa mu kusaci Allah. 20 Ƙari ga haka, da yake Allah ya yi rantsuwa a kan wannan 21 (hakika, wasu sun zama firistoci ba tare da rantsuwa ba, amma wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi game da shi cewa: “Jehobah* ya rantse, kuma ba zai canja raꞌayinsa ba,* ‘Kai firist ne har abada’”), 22 ta haka Yesu ya zama tabbacin yarjejeniya mafi kyau. 23 Ƙari ga haka, mutane da yawa sun zama firistoci ɗaya bayan ɗaya domin mutuwa ta hana su ci-gaba da yin hidimar firist, 24 amma da yake zai ci-gaba da rayuwa har abada, babu waɗanda za su gāje shi a matsayin firist. 25 Don haka, zai iya ba da cikakken ceto ga waɗanda suke zuwa wurin Allah ta wurinsa, domin a kullum yana a raye ya yi roƙo domin su.
26 Gama ya dace mu sami irin wannan shugaban firistoci, wanda mai aminci ne, marar laifi, marar ƙazanta, wanda ba ya kamar masu zunubi, kuma an ɗaukaka shi gaba da sammai. 27 Ba ya bukatar ya riƙa miƙa hadaya kowace rana don zunubansa, saꞌan nan ya miƙa hadaya don zunuban mutane kamar sauran shugabannin firistoci, domin ya yi hakan sau ɗaya tak saꞌad da ya ba da ransa. 28 Gama Dokar ta naɗa mutane masu kasawa a matsayin shugabannin firistoci, amma kalmar rantsuwa da aka yi bayan Dokar ta naɗa Ɗa ne, wanda aka mai da shi cikakke har abada.
8 Yanzu asalin abin da muke faɗa shi ne: Muna da irin wannan shugaban firistoci wanda ya zauna a hannun dama na kujerar mulki na Mai Daraja a sama, 2 shi mai hidima ne a wuri mai tsarki, kuma a tenti na gaskiya, wanda Jehobah* ne ya kafa, ba mutum ba. 3 Gama akan naɗa kowane shugaban firistoci domin ya miƙa kyaututtuka da kuma hadayu; don haka, ya dace ma da wannan ya miƙa hadaya. 4 Da a ce yana duniya, da bai zama firist ba, tun da yake akwai mutanen da Doka* ta riga ta naɗa don su miƙa kyaututtuka. 5 Hidima mai tsarki da mutanen nan suke yi misali ne kuma yana kama da* abubuwan da suke sama; kamar saꞌad da Musa yake so ya gina tenti, Allah ya ba shi umurni cewa: “Ka tabbata ka yi dukan abubuwa daidai kamar yadda aka nuna maka misalin su a kan tudun.” 6 Amma yanzu Yesu ya samu hidima mafi kyau* domin shi ne kuma mai tsayawa tsakani a wata yarjejeniya mafi kyau, wadda aka kafa ta a kan alkawura mafi kyau.
7 Da a ce yarjejeniya ta farkon ba ta da kasawa, da ba za a bukaci ta biyun ba. 8 Gama ya sami mutane da laifi saꞌad da ya ce: “Ga abin da Jehobah* ya faɗa, ‘Duba kwanaki suna zuwa, saꞌad da zan yi wata sabuwar yarjejeniya da jamaꞌar Israꞌila da kuma jamaꞌar Yahuda.’ 9 Jehobah* ya ƙara cewa, ‘Ba zai zama kamar yarjejeniyar da na yi da kakanninsu a ranar da na riƙe hannunsu kuma na fitar da su daga ƙasar Masar ba, domin ba su ci-gaba da kasancewa cikin yarjejeniyata ba, don haka na daina kula da su.’
10 “Jehobah* ya kuma ce, ‘Gama wannan ce yarjejeniya da zan yi da jamaꞌar Israꞌila bayan waɗancan kwanakin. Zan saka dokokina a cikin tunaninsu, zan kuma rubuta su a cikin zukatansu. Zan zama Allahnsu, kuma za su zama mutanena.
11 “‘Kuma babu wanda zai ƙara koyar da ɗan ƙasarsu da kuma ɗanꞌuwansa, yana cewa: “Ka san Jehobah!”* Gama dukansu za su san ni, daga ƙarami zuwa mafi girma da ke cikinsu. 12 Gama zan gafarta musu ayyukansu na mugunta, kuma ba zan sake tuna zunubansu ba.’”
13 Saꞌad da ya yi maganar “sabuwar yarjejeniya,” ya sa na farkon ta daina aiki. Abin da ya daina aiki kuma yake tsufa, ya kusan ɓacewa.
9 A yarjejeniya ta farkon, akwai dokokin da ake bi a hidima mai tsarki da kuma wuri mai tsarki a duniya. 2 Gama a ɗaki na farko da ke cikin tenti da aka gina, akwai sandar riƙe fitila da teburi da burodin da ake miƙa wa Allah; kuma ana kiran sa Wuri Mai Tsarki. 3 Amma a bayan labule na biyu, akwai ɗakin da ake kira Mafi Tsarki a tentin. 4 Yana da abin ƙona turare wanda aka yi da zinariya, da akwatin yarjejeniya wanda aka rufe shi gabaki-ɗaya da zinariya. A cikinsa akwai tulun zinariya da ke ɗauke da manna, da sandar Haruna da ta yi fure da kuma alluna na yarjejeniyar; 5 a samansa akwai siffofin cerub guda biyu* masu ɗaukaka, sun rufe murfin akwatin* da fikafikansu. Amma yanzu ba lokacin da za a yi maganar abubuwan nan dalla-dalla ba ne.
6 Bayan da aka gina waɗannan abubuwan haka, firistoci sukan shiga ɗaki na farko a tentin a-kai-a-kai don su yi hidimomi masu tsarki; 7 amma shugaban firistocin ne kaɗai yake shiga ɗaki na biyu a tentin sau ɗaya a shekara, kuma dole ne ya shiga da jini, wanda yake miƙawa a madadin kansa da kuma don zunuban da mutanen suka yi cikin rashin sani. 8 Ta hakan, ruhu mai tsarki ya nuna cewa saꞌad da tenti na farko yake nan, ba a riga an bayyana hanyar shiga wuri mai tsarki ba tukuna. 9 Wannan tenti misali ne na abin da ke faruwa a yanzu, kuma bisa ga wannan tsarin, ana miƙa kyaututtuka da kuma hadayu. Amma waɗannan abubuwan ba za su iya sa lamirin mutumin da yake hidima mai tsarki ya zama cikakke* ba. 10 Abubuwan nan sun shafi abinci da abin sha da kuma alꞌada na wanke-wanke* kawai. Su umurnai ne da aka bayar a cikin Doka* game da jiki, kuma dole ne su bi Dokar har sai lokacin da Allah ya shirya don ya daidaita abubuwa.
11 Amma saꞌad da Kristi ya zo a matsayin shugaban firistoci na abubuwa masu kyau da sun riga sun faru, ya bi ta wurin tenti mafi girma kuma cikakke wanda ba a yi da hannaye ba, wato ba na wannan duniya ba ne. 12 Ya shiga cikin wuri mai tsarki, ba tare da jinin awaki da na bijimai ba, amma da nasa jinin, ya yi hakan sau ɗaya tak kuma ya samo mana ceto na har abada. 13 Gama idan jinin awaki da na bijimai da kuma tokar ƙaramar saniya da aka yayyafa a kan waɗanda suka ƙazantu, sun tsarkake su da kuma tsabtace jikinsu, 14 babu shakka jinin Kristi zai yi fiye da hakan, wanda ta wurin ruhu na har abada ya miƙa jikinsa marar tabo ga Allah a matsayin hadaya, ya tsabtace lamirinmu daga ayyuka marasa amfani don mu iya yin hidima mai tsarki ga Allah mai rai.
15 Shi ya sa ya zama mai tsayawa tsakani na sabuwar yarjejeniyar, domin waɗanda Allah ya kira su su iya karɓan gādo na har abada da aka yi musu alkawarin sa, hakan ya yiwu ne saboda ya mutu don ya ꞌyantar da mutane daga zunubansu a ƙarƙashin tsohuwar yarjejeniyar. 16 Tun da yake an yi yarjejeniya da Allah, dole ne mutumin da ya yi yarjejeniyar* ya mutu, 17 domin mutuwa ce take sa yarjejeniya ta soma aiki, tun da yake ba ta soma aiki idan mutumin da ya yi yarjejeniyar yana da rai. 18 Shi ya sa yarjejeniya ta farkon ma ba ta soma aiki ba, sai da aka yi amfani da jini. 19 Gama saꞌad da Musa ya gama karanta wa mutanen duka Dokokin, sai ya ɗauki jinin bijimai tare da na awaki, da ruwa, da jar ulu, da hissof,* kuma ya yayyafa a kan littafin* da kuma a kan dukan mutanen, 20 yana cewa: “Wannan ne jinin yarjejeniyar da Allah ya umurce ku ku kiyaye.” 21 Haka ma ya yayyafa jinin a kan tentin da dukan abubuwan da ake amfani da su don a yi hidima mai tsarki.* 22 Hakika, bisa ga Dokar, kusan dukan abubuwa ana iya tsabtace su da jini, kuma idan ba a zubar da jini ba, ba za a iya gafarta wa kowa ba.
23 Don haka, ya zama dole ne a yi amfani da wannan hanyar a tsabtace abubuwan da misali ne na abubuwan da ke sama, amma abubuwan da ke sama suna bukatar hadayu mafi kyau. 24 Gama Kristi bai shiga wuri mai tsarki da aka yi da hannaye ba, wanda misali ne na ainihin, amma ya shiga sama ne, kuma a yanzu yana gaban Allah a madadinmu. 25 Bai yi hakan don ya riƙa miƙa kansa a-kai-a-kai ba, kamar yadda shugaban firistoci yakan shiga cikin wuri mai tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba. 26 In da haka ne, da Kristi ya sha wahala a-kai-a-kai tun daga farkon duniya.* Amma yanzu ya bayyana kansa sau ɗaya tak a kwanakin ƙarshe* don ya kawar da zunubai ta wurin yin hadaya da kansa. 27 Kuma kamar yadda dole ne mutane su mutu sau ɗaya tak, amma bayan sun mutu sai a yi musu shariꞌa, 28 hakan nan ma, aka miƙa Kristi sau ɗaya tak don ya ɗauke zunuban mutane da yawa; kuma a karo na biyu da zai bayyana, ba don zunubi ba ne,* kuma waɗanda suke neman sa da ƙwazo don su samu ceto za su gan shi.
10 Tun da yake Dokar* alama ce na abubuwa masu kyau da ke zuwa, amma ba ita ce ainihin abubuwan ba, ba za ta taɓa iya mai da mutane da ke yin kusa da Allah cikakku ta wurin hadayu da ake miƙawa a-kai-a-kai kowace shekara ba. 2 Da a ce haka ne, da ba a daina miƙa hadayu ba? Domin muddin waɗanda suke hidima mai tsarki suka tsabtace kansu, lamirinsu ba zai sake damun su game da zunubansu ba. 3 A maimakon haka, waɗannan hadayun suna tuna wa mutanen zunubansu a kowace shekara, 4 domin ba zai yiwu jinin bijimai da na awaki su kawar da zunubai ba.
5 Saboda haka, saꞌad da ya shigo duniya, ya ce: “‘Hadaya da bayarwa ba ka so ba, amma ka shirya mini jiki. 6 Ba ka amince da hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na wanke zunubi ba.’ 7 Sai na ce: ‘Ga shi! Na zo don in yi nufinka, Ya Allah (a cikin naɗaɗɗen littafi an rubuta game da ni).’” 8 Bayan ya fara da cewa: “Ba ka so ba, kuma ba ka amince da hadayu, da bayarwa, da hadayu na ƙonawa, da kuma hadayu na wanke zunubi ba,” wato hadayun da ake miƙawa bisa Doka, 9 sai ya ce: “Ga shi! Na zo don in yi nufinka.” Ya kawar da abin da yake na farko don ya kafa abin da yake na biyu. 10 Ta wurin “nufin” nan na Allah an tsarkake mu saꞌad da aka miƙa jikin Yesu Kristi sau ɗaya tak.
11 Ƙari ga haka, kowane firist yakan yi hidimarsa mai tsarki* kowace rana, yana miƙa hadayu iri ɗaya a-kai-a-kai waɗanda ba za su iya kawar da zunubai gabaki-ɗaya ba. 12 Amma wannan mutumin ya miƙa hadaya sau ɗaya tak har abada kuma ya zauna a hannun dama na Allah, 13 tun daga lokacin yana jira har sai lokacin da za a sa abokan gābansa su zama matashin ƙafafunsa. 14 Gama ta wurin hadaya ɗaya da ya miƙa ne ya mai da waɗanda aka tsarkake cikakku har abada. 15 Ƙari ga haka, ruhu mai tsarki ma ya ba mu shaida, gama bayan da ya ce: 16 “Jehobah* ya ce, ‘Wannan ce yarjejeniyar da zan yi da su bayan waɗancan kwanakin, zan sa dokokina a cikin zukatansu, zan kuma rubuta su a cikin tunaninsu.’” 17 Sai ya ce: “Ba zan sake tuna da zunubansu da kuma mugayen ayyukansu ba.” 18 Kuma idan an gafarta wa mutum waɗannan zunuban, ba a bukatar miƙa hadaya don zunubi.
19 Saboda haka, ꞌyanꞌuwa, tun da muna iya shiga wuri mai tsarki da ƙarfin zuciya ta wurin jinin Yesu, 20 wanda ya buɗe mana sabuwar hanya da take kai ga samun rai ta wurin labulen, wato jikinsa, 21 kuma tun da muna da firist mai iko da ke kula da gidan Allah, 22 bari mu matso kusa da Allah da dukan zuciyarmu da cikakkiyar bangaskiya, domin an tsabtace zukatanmu daga lamiri marar kyau, kuma an yi wa jikinmu wanka da ruwa mai tsabta. 23 Bari mu ci-gaba da yin shelar begenmu yayin da muke tsayawa daram, gama wanda ya yi mana wannan alkawarin mai aminci ne. 24 Bari mu lura* da juna, ta hakan za mu iya motsa juna don mu nuna ƙauna kuma mu yi ayyuka masu kyau, 25 kada mu fasa zuwa taronmu, kamar yadda wasu suka saba yi, amma mu riƙa ƙarfafa juna, kuma mu yi hakan sosai yayin da kuke ganin ranar tana matsowa kusa.
26 Gama idan muna yin zunubi da gangan bayan mun sami cikakken ilimin gaskiya, babu wata hadaya kuma da za ta wanke zunubanmu, 27 a maimakon haka, abin da ya rage shi ne, jiran hukunci cikin tsoro da kuma fushi da yake ci kamar wuta, da za ta cinye waɗanda suke gāba da Allah. 28 Duk wanda ya ƙi yin biyayya ga Dokar Musa, akan kashe shi ba tare da an ji tausayin sa ba, muddin mutane biyu ko uku sun ba da shaida. 29 Balle ma mutumin da ya rena, ya kuma ƙi* Ɗan Allah, kuma ya ɗauki jinin yarjejeniya da aka tsabtace shi da shi a matsayin abu marar daraja, wanda kuma ya zagi ruhun alheri, ba kwa ganin hukuncin da za a yi masa zai fi tsanani? 30 Gama mun san Wanda ya ce: “Ramuwa tawa ce; ni kuwa zan rama.” Ya kuma ce: “Jehobah* zai yi wa mutanensa shariꞌa.” 31 Abin ban tsoro ne Allah mai rai ya hukunta mutum.
32 Amma ku ci-gaba da tunawa da kwanakin dā, waɗanda bayan da kuka ga haske, kun jimre ma wahaloli yayin da kuke fama sosai. 33 A wasu lokuta akan tsananta muku da wulaƙanta ku a gaban jamaꞌa, a wasu lokuta kuma kukan jimre tare da waɗanda ake tsananta musu da kuma wulaƙanta su. 34 Kun ji tausayin waɗanda aka sa a kurkuku, kuma saꞌad da aka ƙwace kayanku kun yi farin ciki domin kun san cewa kuna da dukiya mafi kyau wadda za ta dawwama.
35 Saboda haka, kada ku yi watsi da ƙarfin zuciyarku,* don za ku sami lada sosai. 36 Kuna bukatar jimrewa, domin bayan kun yi nufin Allah, za ku samu cikar alkawarin da ya yi. 37 Kuma a cikin “ɗan ƙanƙanin lokaci, wanda yake zuwa zai iso, kuma ba zai ɓata lokaci ba.” 38 “Amma bawana mai adalci zai rayu saboda bangaskiyarsa,” kuma “idan ya ja da baya, ba zan* yi farin ciki da shi ba.” 39 Mu ba waɗanda suke ja da baya zuwa ga hallaka ba ne, amma mu masu bangaskiya ne don mu ceci rayukanmu.*
11 Bangaskiya ita ce kasancewa da tabbaci a kan abin da mutum yake begen sa, da kuma hujja da ke tabbatar da abubuwan da ba a iya gani. 2 Gama ta wurin ta ne Allah ya nuna wa mutanen dā* cewa sun yi abin da yake so.
3 Ta wurin bangaskiya ne muka gane cewa Allah ya tsara duniya* da kyau ta wurin kalmarsa, ta hakan ne abubuwan da ake gani sun fito daga abubuwan da ba a iya gani.
4 Ta wurin bangaskiya ne Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi ta Kayinu daraja, kuma ta wurin bangaskiyar ne ya sami shaida cewa shi mai adalci ne, gama Allah ya amince da kyaututtukan da ya bayar, kuma duk da cewa ya mutu, yana magana ta wurin bangaskiyarsa.
5 Ta wurin bangaskiya ne aka ɗauke Enok domin kada ya ga mutuwa, kuma ba a sake ganin sa ba domin Allah ya ɗauke shi. Gama kafin a ɗauke shi, ya sami shaida cewa ya faranta wa Allah rai sosai. 6 Ƙari ga haka, ba zai yiwu a faranta wa Allah rai in ba tare da bangaskiya ba, domin duk mai zuwa wurin Allah, dole ne ya yarda cewa akwai Allah kuma cewa shi ne mai ba da lada ga masu neman sa da dukan zuciyarsu.
7 Ta wurin bangaskiya ne Nuhu, bayan ya sami gargaɗi daga wurin Allah game da abubuwan da ba a gan su ba tukuna, ya nuna cewa shi mai tsoron Allah ne kuma ya gina jirgin ruwa don ya ceci mutanen gidansa. Kuma ta wurin bangaskiyarsa, ya sanar da cewa duniyar nan ta cancanci hukunci, kuma ya zama magāji na adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.
8 Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, saꞌad da aka kira shi ya yi biyayya ta wurin zuwa wurin da za a ba shi a matsayin gādo, ya tafi duk da cewa bai san wurin da za shi ba. 9 Ta wurin bangaskiya ya yi rayuwa a matsayin baƙo a ƙasar da Allah ya yi masa alkawari, ya yi zama a cikin tentuna tare da Ishaku da Yakubu, waɗanda su ma za su gāji alkawarin nan tare da shi. 10 Gama yana jiran birni wanda yake da tushe na gaske, wanda Allah ne ya zana kuma ya gina shi.
11 Ta wurin bangaskiya ne Saratu ma ta sami ƙarfin iya ɗaukan ciki ko da yake ta wuce shekarun haifuwa, domin ta ɗauki Wanda ya yi mata alkawarin a matsayin mai aminci. 12 Wannan dalilin ne ya sa ta wurin mutum ɗaya wanda yake kamar matacce,* aka haifi yara da yawa kamar taurarin da ke sama da kuma kamar yashi da ke bakin teku da ba a iya ƙirgawa.
13 A cikin bangaskiya ne dukan mutanen nan suka mutu ko da yake ba su ga cikar alkawuran da aka yi musu ba. Amma sun hango su daga nesa kuma sun karɓe su da farin ciki, har suka sanar wa mutane cewa su baƙi ne kuma suna zama na ɗan lokaci ne a ƙasar. 14 Gama mutanen da suka yi magana haka, sun nuna a fili cewa da dukan zuciyarsu suna neman wuri da zai zama nasu. 15 Duk da haka, da a ce sun ci-gaba da yin tunani a kan wurin da suka bari, da sun sami zarafin komawa. 16 Amma yanzu suna ƙoƙarin samun wuri mafi kyau, wato wurin da yake na sama, shi ya sa Allah bai ji kunya a kira shi Allahnsu ba, gama ya shirya wani birni domin su.
17 Ta wurin bangaskiya ne saꞌad da aka gwada Ibrahim, ya yarda, har kamar ya gama miƙa Ishaku a matsayin hadaya; mutumin da ya karɓi alkawarin nan da farin ciki ya yi ƙoƙarin miƙa makaɗaicin ɗansa a matsayin hadaya, 18 ko da yake an riga an gaya masa cewa: “Waɗanda za a kira zuriyarka za su fito ta wurin Ishaku ne.” 19 Amma ya yi tunani cewa Allah zai iya ta da Ishaku ko daga mutuwa ne, kuma za mu iya cewa daga mutuwa ne ya karɓi Ishaku.
20 Ta wurin bangaskiya kuma, Ishaku ya albarkaci Yakubu da Isuwa kuma ya gaya musu abubuwan da za su faru a gaba.
21 Ta wurin bangaskiya, Yakubu, saꞌad da ya kusan mutuwa, ya albarkaci kowane ɗaya daga cikin ꞌyaꞌyan Yusufu kuma ya yi sujada yayin da yake jingine a kan sandarsa.
22 Ta wurin bangaskiya, Yusufu saꞌad da ya kusan mutuwa ya yi magana game da yadda ꞌyaꞌyan Israꞌila za su bar Masar kuma ya ba da umurni game da ƙasusuwansa.*
23 Ta wurin bangaskiya, iyayen Musa sun ɓoye shi har na wata uku bayan an haife shi, domin sun ga cewa yaron kyakkyawa ne kuma ba su ji tsoron umurnin sarki ba. 24 Ta wurin bangaskiya ne Musa, saꞌad da ya yi girma bai yarda a kira shi ɗan ꞌyar Firꞌauna ba, 25 ya fi so a wulaƙanta shi tare da mutanen Allah maimakon ya ji daɗin zunubi na ɗan lokaci, 26 domin a wurinsa shan wulaƙanci a matsayinsa na Shafaffe* arziki ne da ya fi dukiyoyin Masar, gama ya mai da hankali sosai ga ladan da zai samu. 27 Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, bai ji tsoron fushin sarki ba, gama ya ci-gaba da tsayawa daram kamar yana ganin Wanda ba a iya ganin sa. 28 Ta wurin bangaskiya, ya yi Bikin Ƙetarewa kuma ya yayyafa jini domin kada mai hallaka ya yi wa ɗan farinsu lahani.*
29 Ta wurin bangaskiya sun ƙetare Jar Teku a busasshiyar ƙasa, amma saꞌad da mutanen Masar suka yi ƙoƙarin yin hakan, ruwan ya haɗiye su.
30 Ta wurin bangaskiya, katangar Jeriko ta fāɗi bayan da mutanen suka zagaya ta na kwanaki bakwai. 31 Ta wurin bangaskiya, Rahab karuwar nan ba ta hallaka tare da mutanen da suka yi rashin biyayya ba, domin ta marabci ꞌyan leƙen asirin cikin salama.
32 Me kuma zan ƙara cewa? Gama lokaci ba zai ishe ni ba idan na ci-gaba da ba ku labarin Gidiyon, da Barak, da Samson, da Jefta, da Dauda, tare da Samaꞌila da sauran annabawa. 33 Ta wurin bangaskiya, sun ci nasara a kan mulkoki, sun sa a yi adalci, sun sami abubuwan da aka yi musu alkawari, sun rufe bakunan zakoki, 34 sun tsayar da ikon wuta, sun tsira daga bakin takobi, daga marasa ƙarfi an mai da su masu ƙarfi, sun zama jarumai a yaƙi, kuma sun kori sojojin da suka kawo musu hari. 35 Mata sun karɓi ƙaunatattunsu da aka ta da daga mutuwa, amma an azabtar da wasu mutane domin sun ƙi su yi watsi da bangaskiyarsu don a yantar da su, sun yi hakan ne domin su sami tashin matattu mafi kyau. 36 Hakika, wasu sun sha gwaji ne ta wurin baꞌa da bulala da aka yi musu, fiye ma da hakan, wasu an ɗaure su da sarƙa kuma an jefa su a kurkuku. 37 An jejjefe su da duwatsu, an gwada su, an raba su kashi biyu, an yanka su da takobi, sun yi ta yawo da fatan tumaki da na awaki, sun shiga cikin bukata, sun sha ƙunci, an wulaƙanta su, 38 kuma duniya ba ta cancanci su zauna a cikinta ba, sun yi ta yawo a hamada da tuddai da kogwanni da kuma ramuka na duniya.
39 Duk da haka, dukan mutanen nan, ko da yake sun sami shaida mai kyau saboda bangaskiyarsu, ba su ga cikar alkawarin da Allah ya yi musu ba, 40 gama tun dā, Allah ya ga wani abin da zai fi amfanar mu, domin kada su zama cikakku ba tare da mu ba.
12 Saboda haka, da yake muna da irin wannan taron shaidu masu yawa kewaye da mu, bari mu jefar da kowane kaya mai nauyi da zunubin da ke saurin zama mana tarko, kuma bari mu yi tseren nan da aka sa a gabanmu da jimrewa, 2 yayin da muke zuba ido sosai ga Shugaba da kuma wanda yake sa bangaskiyarmu ta zama cikakkiya, wato Yesu. Saboda farin cikin da aka sa a gabansa, ya jimre a kan gungumen azaba,* bai ji kunya ba, kuma ya zauna a hannun dama na kujerar mulki na Allah. 3 Hakika, ku yi tunani sosai game da wanda ya jimre irin maganganu marasa kyaun nan daga masu zunubi, waɗanda ba za su amfane su ba, domin kada ku gaji kuma ku fid da zuciya.
4 A cikin famar da kuka yi a kan zunubi, ba ku taɓa yin tsayayya da shi har ya kai ga zub da jininku ba. 5 Kun kuma manta da shawarar nan da Allah ya ba ku gabaki-ɗaya saꞌad da ya kira ku ꞌyaꞌya yana cewa: “Ɗana, kada ka yi tunanin cewa horo daga wurin Jehobah* ba shi da amfani ko kuma ka fid da zuciya saꞌad da ya yi maka gyara; 6 gama waɗanda Jehobah* yake ƙauna ne yake yi musu horo. Hakika, duk wanda ya karɓa a matsayin ɗa, yakan yi masa bulala.”*
7 Ku ɗauki wahalar da kuke sha a matsayin horo* ne ake muku. Allah yana bi da ku kamar yaransa. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya yi masa horo? 8 Amma idan dukanku ba ku sami horon nan ba, ku ba yaransa na gaske ba ne, ku yaran wani ne. 9 Ƙari ga haka, ubanninmu na jiki sukan yi mana horo, kuma muna girmama su. Bai kamata mu fi kasancewa a shirye mu miƙa kanmu ga Uba wanda yake ja-goranci rayuwarmu ta wurin ruhunsa kuma mu ci-gaba da rayuwa ba? 10 Gama sun yi mana horo na ɗan lokaci bisa ga abin da suke gani ya dace, amma Allah yana yin hakan ne domin mu amfana, kuma mu kasance da tsarki kamar yadda yake. 11 A gaskiya, babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yin sa, amma yana da zafi. Duk da haka, daga baya yana kawo salama da adalci ga waɗanda suka karɓi horon.
12 Saboda haka, ku ƙarfafa hannayen da suka gaji da gwiwoyi marasa ƙarfi. 13 Ku ci-gaba da sa hanyoyin da za ku bi su miƙe, domin kada gurgu ya ƙara jin rauni, maimakon ya warke. 14 Ku yi iya ƙoƙarinku ku zauna lafiya da dukan mutane kuma ku kasance da tsarki, idan ba haka ba, babu mutumin da zai ga Ubangiji. 15 Ku yi hankali sosai, kada wani ya kasa samun alherin Allah, domin kada wata jijiya mai guba ta taso a tsakaninku ta jawo matsala kuma ta ƙazantar da mutane da yawa. 16 Ku kuma lura kada wani a cikinku ya zama wanda yake yin lalata* ko wanda ba ya daraja abubuwa masu tsarki yadda Isuwa ya yi, wanda ya sayar da gādonsa na ɗan fari don kwanon abinci ɗaya tak. 17 Gama kun sani cewa daga baya saꞌad da yake so ya gāji albarkar, an ƙi shi; ko da yake ya yi ƙoƙari sosai, har da zub da hawaye don ya canja shawarar,* amma hakan bai yiwu ba.
18 Gama ba ku zo kusa da abin da ake iya taɓawa ba, wanda aka kunna masa wuta, wanda yake da baƙin gajimare, da tsananin duhu, da guguwa mai ƙarfi, 19 da ƙarar kakaki da ake busawa, da murya da take furta kalmomi, wadda saꞌad da mutanen suka ji, suka roƙa kada a ƙara yi musu magana. 20 Gama ba su iya jimre ma umurnin nan da aka ba su ba, cewa: “Ko da dabba ce ta taɓa tudun, dole a jejjefe ta da duwatsu har ta mutu.” 21 Ƙari ga haka, abin da suka gani ya ba su tsoro har Musa ya ce: “Na ji tsoro kuma jikina yana rawa.” 22 Amma kun zo kusa da Tudun Sihiyona da kuma birnin Allah mai rai, wato Urushalima ta sama, tare da dubun dubban malaꞌiku 23 da suka taru, da ikilisiyar ꞌyaꞌyan fari waɗanda aka rubuta sunayensu a sama, da Allah Alƙalin dukan mutane, da masu adalci waɗanda ruhu mai tsarki yake yi musu ja-goranci kuma suka zama cikakku, 24 da Yesu mai tsayawa tsakani na sabuwar yarjejeniya, da kuma jinin da aka yayyafa wanda yake da daraja fiye da jinin Habila.
25 Ku mai da hankali don kada ku ƙi saurarar wanda yake magana. Gama idan waɗanda suka ƙi saurarar wanda yake ba da gargaɗi daga sama ga mutane a duniya ba su tsira ba, to tabbas ba za mu tsira ba idan muka ƙi saurarar wanda yake magana daga sama! 26 A lokacin, muryarsa ta jijjiga duniya, amma yanzu ya yi alkawari cewa: “Ba duniya kaɗai zan sake jijjiga ba, zan kuma jijjiga sama.” 27 Furucin nan “zan sake” yana nufin zai kawar da abubuwan da aka jijjiga, wato abubuwan da aka halitta, domin abubuwan da ba a jijjiga ba su ci-gaba da kasancewa. 28 Saboda haka, da yake za mu samu Mulkin da ba za a iya jijjiga shi ba, bari mu ci-gaba da samun alheri, ta hakan za mu iya yi wa Allah hidima mai tsarki cikin tsoro da girmamawa, don ya amince da ita. 29 Gama Allahnmu wuta ne mai cinye abu ƙurmus.
13 Ku ci-gaba da nuna wa juna ƙauna irin ta ꞌyanꞌuwa. 2 Kada ku daina karɓan baƙi,* gama ta yin haka ne wasu suka kula da malaꞌiku ba da saninsu ba. 3 Ku tuna da waɗanda suke kurkuku kamar dai kuna kurkuku tare da su, da kuma waɗanda ake wulaƙanta su, kamar dai kuna shan wahala tare da su* ne. 4 Bari aure ya zama abu mai daraja a gare ku duka, kuma kada gadon aurenku ya zama da ƙazanta, gama Allah zai shariꞌanta masu lalata* da masu zina. 5 Bari yadda kuke rayuwa ya nuna cewa ku ba masu son kuɗi ba ne, yayin da kuke gamsuwa da abubuwan da kuke da su a yanzu. Gama ya ce: “Ba zan taɓa barin ka ba, kuma ba zan taɓa yashe ka ba.” 6 Don mu iya kasancewa da ƙarfin zuciya kuma mu ce: “Jehobah* mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba. Mene ne mutum zai iya yi mini?”
7 Ku tuna da waɗanda suke ja-goranci a cikinku, waɗanda suka faɗa muku kalmar Allah, kuma yayin da kuke lura da sakamakon irin rayuwar da suka yi, ku yi koyi da bangaskiyarsu.
8 Yesu Kristi kuwa ba ya canjawa, yadda yake jiya, haka yake yau, haka kuma zai kasance har abada.
9 Kada ku bar koyarwa da suka yi dabam da waɗanda kuka saba ji su sa ku kauce hanya, gama gwamma alheri ya sa zuciya ta yi ƙarfi maimakon abinci,* domin ba ya amfanar waɗanda suke ɗaukan sa da muhimmanci.
10 Muna da bagade kuma waɗanda suke hidima mai tsarki a tentin ba su da izinin cin abinci a kan bagaden. 11 Gama shugaban firistoci yakan ɗauki jinin dabbobi ya shiga wuri mai tsarki ya miƙa a matsayin hadaya ta zunubi. Amma jikunan dabobbin akan ƙona su a bayan sansani. 12 Saboda haka, Yesu ma ya sha wahala a bayan gari don ya tsabtace mutanen Allah da jininsa. 13 Bari mu je mu same shi a bayan sansanin ɗauke da kunyar da ya sha, 14 gama ba mu da wani birni a nan da zai kasance har abada, amma da dukan zuciyarmu muna neman birnin da zai zo. 15 Ta wurinsa, bari mu riƙa miƙa wa Allah hadaya ta yabo, wato kalmomin da ke fitowa daga bakinmu da ke shelar sunansa ga jamaꞌa. 16 Ƙari ga haka, kada ku manta ku yi alheri kuma ku raba abin da kuke da shi da wasu, gama irin hadayun nan suna faranta wa Allah rai.
17 Ku yi biyayya ga waɗanda suke ja-goranci a cikinku kuma ku miƙa kanku gare su, gama suna lura da ku* a matsayin waɗanda za su ba da lissafin abin da suka yi, domin su iya yin hakan da farin ciki ba tare da gunaguni ba, gama hakan zai yi muku lahani.
18 Ku ci-gaba da yi mana adduꞌa domin mun san cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna so mu yi kome cikin gaskiya. 19 Amma musamman ina roƙon ku, ku yi adduꞌa domin in iya dawo gare ku da wuri.
20 Yanzu, bari Allah na salama wanda ya ta da babban makiyayin tumakin nan, wato Ubangijinmu Yesu daga mutuwa da jinin yarjejeniya ta har abada, 21 ya ba ku kowane abu mai kyau don ku yi nufinsa, kuma ya yi amfani da Yesu Kristi ya sa ku yi abin da zai faranta masa rai, bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abadan abadin. Amin.
22 Yanzu, ina roƙon ku ꞌyanꞌuwa, cewa ku saurari kalmomin ƙarfafan nan cikin haƙuri, gama gajeriyar wasiƙa ce na rubuta muku. 23 Ina so ku sani cewa an saki ɗanꞌuwanmu Timoti, idan ya zo da wuri, zan zo tare da shi don in gan ku.
24 Ku miƙa gaisuwata ga dukan waɗanda suke ja-goranci a cikinku, da kuma dukan tsarkaka. Waɗanda suke Italiya suna aika muku gaisuwarsu.
25 Bari alheri ya kasance da dukanku.
A yaren Girka, “ƙarshen kwanakin nan.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “durƙusa.”
Ko kuma “hidima ga jamaꞌa.”
Ko kuma “hidima ga jamaꞌa.”
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Wato, Yesu.
Da alama wannan yana nufin lokacin da Adamu da Hauwaꞌu suka haifi yara.
Ko kuma “kaifinta ya fi na.”
Ko kuma “ta fi kowane takobi mai baki biyu ci.”
Wato, yadda mutum yake a zahiri. A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Wato, yadda mutum yake a ciki.
Wani abu kamar kitse da ke cikin ƙashi.
Ko kuma “a hankali.”
Ko kuma “yadda suke tunani.”
A yaren Girka, “ikon.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “anka.”
A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “ganima mafi kyau.”
Ko kuma “Dokar Musa.”
Ko kuma “kamilai.”
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ko kuma “ba zai yi da-na-sani ba.”
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ko kuma “Dokar Musa.”
A yaren Girka, “inuwa ne na.”
Ko kuma “hidima ga jamaꞌa.”
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Cerub malaꞌiku ne masu iko sosai.
A yaren Girka, kalmar tana iya nufin murfin hadaya ta sasantawa.
Ko kuma “kamili.”
A yaren Girka, “baftisma dabam-dabam.”
Ko kuma “Dokar Musa.”
Ko kuma “mai tsayawa tsakani na yarjejeniyar.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “naɗaɗɗen littafin.”
Ko kuma “hidima ga jamaꞌa.”
Da alama wannan yana nufin lokacin da Adamu da Hauwaꞌu suka haifi yara.
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “ba don ya magance zunubi ba ne.”
Ko kuma “Dokar Musa.”
Ko kuma “hidimarsa ga jamaꞌa.”
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ko kuma “damu.”
A yaren Girka, “tattaka.”
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
A yaren Girka, “ꞌyancinku na yin magana.”
Ko kuma “raina ba zai.”
A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ko kuma “kakanninmu.”
Ko kuma “wannan zamanin.” Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Wato, ba ya iya haifuwa.
Ko kuma “yadda za a binne shi.”
A yaren Girka, “Kristi.”
A yaren Girka, “taɓa ɗan farinsu.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ko kuma “horo mai tsanani.”
Ko kuma “koyarwa.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Wato, ya canja raꞌayin mahaifinsa.
Ko kuma “yi wa baƙi alheri.”
A yaren Girka, “tun da yake ku jiki ɗaya.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Wato, dokoki a kan abinci.
Ko kuma “rayukanku.” A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.