Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt 2 Timotawus 1:1-3:18
  • 2 Tasalonikawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 2 Tasalonikawa
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
2 Tasalonikawa

WASIƘA TA BIYU ZUWA GA TASALONIKAWA

1 Daga ni Bulus, da Silbanus,* da kuma Timoti, zuwa ga ikilisiyar Tasalonikawa wadda ke da haɗin kai da Allah Ubanmu, da kuma Ubangiji Yesu Kristi:

2 Bari alheri da salama daga Allah Uba, da kuma Ubangiji Yesu Kristi su kasance tare da ku.

3 ꞌYanꞌuwa, dole ne mu gode wa Allah kullum saboda ku. Hakan ya dace domin bangaskiyarku tana ƙaruwa sosai, kuma ƙaunar da kowannenku ke nuna wa juna tana daɗa ƙaruwa. 4 Saboda haka, mu da kanmu muna taƙama da ku a cikin ikilisiyoyin Allah, domin jimrewarku, da bangaskiyarku, duk da yawan tsanantawa da kuma wahalolin* da kuke sha. 5 Wannan tabbaci ne cewa Allah yana yin shariꞌar adalci, kuma hakan ne zai sa ku cancanci shiga Mulkin Allah, wanda kuke shan wahala domin sa.

6 Da yake Allah mai adalci ne, zai sāka ma waɗanda suke wahalar da ku ta wurin wahalar da su. 7 Amma ku da ake wahalar da ku, za a ꞌyantar da ku tare da mu a lokacin da za a bayyana Ubangiji Yesu daga sama tare da malaꞌikunsa masu iko 8 cikin harsunan wuta, a lokacin zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda ba sa yin biyayya ga labari mai daɗi game da Ubangijinmu Yesu. 9 Ubangijinmu zai yi ma waɗannan mutane shariꞌa kuma zai yi musu hukunci ta wurin hallaka su har abada, kuma ya kawar da su daga gabansa da kuma ɗaukakar ikonsa 10 a lokacin da zai zo domin ya samu ɗaukaka tare da tsarkakansa, kuma dukan waɗanda suka ba da gaskiya za su yabe shi a ranar domin kun gaskata da abubuwan da muka gaya muku.

11 Saboda haka ne muke yi muku adduꞌa a kowane lokaci, cewa Allahnmu ya ga kun cancanci ya kira ku kuma ya yi amfani da ikonsa ya yi dukan abubuwa masu kyau da yake so, kuma ya taimaka muku ku yi dukan aikin da bangaskiyarku take sa ku yi. 12 Ta hakan za a ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu a cikinku, kuma za ku samu ɗaukaka cikin haɗin kai da shi bisa ga alherin Allahnmu da kuma na Ubangiji Yesu Kristi.

2 Amma ꞌyanꞌuwa, game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kristi da kuma yadda za mu taru a wurinsa, muna roƙon ku 2 kada ku bari a yi saurin rikitar da hankalinku, ko hankalinku ya tashi saboda saƙon da aka ce daga wurin Allah ne ko maganar da aka yi da baki, ko ta wasiƙar da ta yi kamar daga wurinmu ne ta fito, cewa ranar Jehobah* ta zo.

3 Kada ku bari wani ya yaudare* ku ko ta yaya, domin ranar ba za ta zo ba, sai an yi ridda* tukuna, kuma sai an bayyana mutumin da ke taka doka, wato ɗan hallaka. 4 Yana gāba kuma yana ɗaukaka kansa fiye da duk wani abin da ake kira allah, ko abin da ake yi wa sujada, shi ya sa ya zauna a haikalin Allah, yana nuna a fili cewa shi allah ne. 5 Ba ku tuna cewa saꞌad da nake tare da ku nakan gaya muku abubuwan nan ba?

6 Yanzu kun san abin da ke hana mutumin nan mai taka doka bayyana, domin a bayyana shi saꞌad da lokacinsa ya yi. 7 A gaskiya, abubuwan sirri da mutumin nan yake yi, sun riga sun fara aiki, kuma za su ci-gaba da zama sirri har sai wanda yake hana shi bayyana yanzu ba ya nan. 8 Saꞌan nan za a bayyana mutumin nan mai taka doka. Saꞌad da Ubangiji Yesu ya nuna a fili cewa ya dawo, zai kawar da mutumin nan da numfashin* bakinsa kuma ya hallaka shi. 9 Za a gane bayyanar mutumin nan mai taka doka ta wurin ayyukan Shaiɗan tare da ayyukan ban mamaki da alamun ƙarya da ayyukan alꞌajibi 10 kuma zai yi amfani da kowane irin rashin adalci don ya ruɗi mutane, abubuwan nan za su faru da mutanen da Allah zai hukunta ta wurin hallaka su domin ba su so gaskiya ko su amince da ita don su tsira ba. 11 Shi ya sa Allah ya bari a yi amfani da ƙaryace-ƙaryace a ruɗe su, domin su gaskata da ƙaryar, 12 ta hakan za a yi wa dukansu hukunci domin ba su yarda da gaskiyar ba, kuma suna jin daɗin yin rashin adalci.

13 Amma, ꞌyanꞌuwa waɗanda Jehobah* yake ƙauna, muna da hakkin gode wa Allah a kowane lokaci domin ku, saboda tun da farko Allah ya zaɓe ku don ku samu ceto ta wurin tsarkake ku da ruhunsa da kuma amincewarku da gaskiya. 14 Ya kira ku ta wurin labari mai daɗi da muke shelar sa domin ku sami ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kristi. 15 Saboda haka ꞌyanꞌuwa, ku tsaya daram kuma ku ci-gaba da bin abubuwan* da muka koya muku, ko da mun yi hakan ne ta maganar baki, ko kuma ta wasiƙar da muka aika muku. 16 Ƙari ga haka, bari Ubangijinmu Yesu Kristi da kansa, da Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya yi mana ƙarfafa marar ƙarewa, kuma ya ba mu bege mai kyau ta wurin alherinsa, 17 ya ƙarfafa zukatanku kuma ya sa ku tsaya daram a cikin kowane aiki mai kyau da kuma maganar da kuke yi.

3 A ƙarshe ꞌyanꞌuwa, ku ci-gaba da yin adduꞌa a madadinmu, domin kalmar Jehobah* ta yi ta yaɗuwa da sauri kuma mutane su karɓe ta da daraja kamar yadda kuka yi, 2 kuma don a kāre mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama bangaskiya ba mallakar dukan mutane ba ce. 3 Amma Ubangiji mai aminci ne, kuma zai ƙarfafa ku da kuma kāre ku daga mugun nan. 4 Ƙari ga haka, da yake mu mabiyan Ubangiji ne, muna da tabbaci cewa kuna bin umurnan da muka ba ku, kuma za ku ci-gaba da bin su. 5 Bari Ubangiji ya ci-gaba da bi da zukatanku da kyau don ku ƙaunaci Allah, kuma ku jimre domin Kristi.

6 Yanzu ꞌyanꞌuwa, muna ba ku umurni cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kristi, cewa ku daina tarayya da dukan ꞌyanꞌuwa da ba sa yin abin da ya dace kuma ba sa bin umurnan* da kuka* koya daga wurinmu. 7 Gama ku da kanku kun san yadda ya kamata ku yi koyi da mu, domin saꞌad da muke tare da ku, ba mu yi rayuwa yadda muka ga dama ba,* 8 kuma ba mu ci abincin wani ba tare da biya ba. A maimakon haka, mun yi aiki sosai, da fama dare da rana domin kada mu sa ku kashe kuɗi da yawa wajen kula da mu. 9 Ba wai ba mu da ikon gaya muku ku ba mu abubuwa ba ne, amma mun yi hakan ne, domin mu zama abin koyi a gare ku. 10 Hakika, saꞌad da muke tare da ku, mukan ba ku umurnin nan cewa: “Duk wanda ba ya so ya yi aiki, kada ku bar shi ya ci abinci.” 11 Gama mun ji cewa wasu a cikinku ba sa yin abin da ya dace, ba sa aiki sam, amma suna sa baki a batun da bai shafe su ba. 12 Muna ba wa irin mutanen nan umurni da kuma gargaɗi cikin Ubangiji Yesu Kristi cewa, su yi aiki ba tare da sa baki a batun da bai shafe su ba, kuma su ci abincin da suka yi aiki a kai.

13 Ku ꞌyanꞌuwa, kada ku gaji da yin abin da yake nagari. 14 Amma duk wanda ba ya biyayya ga abin da muka faɗa ta wurin wasiƙar nan, ku yi hankali da mutumin, kuma ku daina tarayya da shi, domin ya ji kunya. 15 Duk da haka, kada ku ɗauke shi kamar abokin gāba, amma ku ci-gaba da yi masa gargaɗi a matsayin ɗan­ꞌuwa.

16 Yanzu bari Ubangiji na salama da kansa ya ci-gaba da ba ku salama ta kowace hanya. Bari Ubangiji ya kasance tare da dukanku.

17 Ni Bulus nake rubuta muku wannan gaisuwar da hannuna, wannan ce alama a kowace wasiƙata; haka nake rubutu.

18 Bari alherin Ubangijinmu Yesu Kristi ya kasance tare da dukanku.

Ana kuma kiran sa Silas.

Ko kuma “ƙunci.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ko kuma “ruɗe.”

Ko kuma “yi wa Allah tawaye.”

A yaren Girka, “ruhun.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

A yaren Girka, “alꞌadun.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ko kuma “alꞌadar.”

Yana kuma iya nufin, “suka.”

Ko kuma “ba mu ƙi bin tsari ba.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba