Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • nwt 1 Timotawus 1:1-5:28
  • 1 Tasalonikawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 1 Tasalonikawa
  • Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna)
1 Tasalonikawa

WASIƘA TA FARKO ZUWA GA TASALONIKAWA

1 Daga ni Bulus, da Silbanus,* da kuma Timoti, zuwa ga ikilisiyar Tasalonikawa wadda ke da haɗin kai da Allah Uba, da kuma Ubangiji Yesu Kristi:

Bari alheri da kuma salama su kasance tare da ku.

2 A kullum muna gode wa Allah saꞌad da muka ambata dukanku a cikin adduꞌoꞌinmu, 3 gama a gaban Allahnmu da Ubanmu, mun ci-gaba da tuna da aikin da kuke yi cikin aminci, da famar da kuke yi don ƙauna, da kuma jimrewarku saboda begen da kuke da shi cikin Ubangijinmu Yesu Kristi. 4 Gama ꞌyanꞌuwa waɗanda Allah yake ƙauna, mun san cewa Allah ya zaɓe ku ne 5 domin labari mai daɗi da muka yi muku waꞌazin sa, ba da baki ne kawai ba, amma da iko, da ruhu mai tsarki, da kuma cikakken tabbaci ne, kun kuma san irin halayen da muka nuna saꞌad da muke tare da ku don amfaninku. 6 Kuma kun yi koyi da mu da kuma Ubangiji, da yake kun amince da kalmar cikin farin cikin da ruhu mai tsarki yake bayarwa, duk da cewa ana tsananta muku, 7 ta hakan kun zama abin koyi ga dukan masu bi da ke Makidoniya da kuma Akaya.

8 A gaskiya, ba kawai kun yi waꞌazin kalmar Jehobah* a Makidoniya da Akaya ba, amma bangaskiyarku ta yaɗu zuwa koꞌina, har ma ba ma bukatar mu faɗi kome. 9 Gama su da kansu sun ci-gaba da yin magana game da lokaci na farko da muka haɗu da ku, da yadda kuka bar gumakanku, kuka komo ga Allah, domin ku bauta wa Allah na gaskiya mai rai, 10 kuma ku jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tayar daga mutuwa, wato Yesu, wanda ya cece mu daga fushin da ke zuwa.

2 ꞌYanꞌuwa, ba shakka ku da kanku kun san cewa ziyarar da muka kawo muku ta kawo sakamako masu kyau. 2 Gama ko da yake da farko mun sha wahala, kuma an wulaƙanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, mun yi ƙarfin zuciya* ta wurin Allahnmu, don mu gaya muku labari mai daɗi na Allah, duk da yawan gāba da muka fuskanta. 3 Gama gargaɗin da muka yi muku, bai fito daga kuskure ko daga ƙazanta ko kuma daga yaudara ba, 4 amma kamar yadda Allah ya yarda ya danƙa mana labari mai daɗin, ba ma magana don mu faranta wa mutane rai, sai dai don mu faranta ran Allah ne, wanda yake bincika zukatanmu.

5 A gaskiya, kun san cewa ba mu taɓa yi muku daɗin baki don mu ruɗe ku ba; ko mu yi munafunci don muna so mu sami wani abu daga wurinku ba; Allah shi ne shaidarmu! 6 Kuma ba mu taɓa neman ɗaukaka daga wurin mutane, ko daga wurinku, ko daga wurin wasu ba, duk da cewa a matsayinmu na manzannin Kristi za mu iya zama nawaya a kanku. 7 A maimakon haka, kamar yadda mace mai shayarwa take reno da kuma lura da yaranta, haka mun lura da ku cikin sauƙin kai. 8 Saboda muna ƙaunar ku sosai, shi ya sa muka yi marmarin yi muku waꞌazin labari mai daɗi na Allah, har mu ba da rayukanmu* don muna ƙaunar ku sosai.

9 Babu shakka ꞌyanꞌuwa, kun tuna aiki da fama da muka yi. A lokacin da muka yi muku waꞌazin labari mai daɗi na Allah, mun yi aiki dare da rana, don kada mu zama nawaya ga wani a cikinku. 10 Ku shaidu ne, haka ma Allah shaida ne na yadda muka yi shaꞌani da ku masu bi cikin aminci da adalci da kuma rashin laifi. 11 Kun san cewa mun yi ta yi muku gargaɗi da ƙarfafa ku, da ba da shaida a kan kowannenku, kamar yadda uba yake yi wa yaransa, 12 domin ku yi rayuwar da ta dace a gaban Allah, wanda ya kira ku ga Mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.

13 Hakika, wannan ne ma ya sa ba mu taɓa daina gode wa Allah ba, domin saꞌad da kuka karɓi kalmar Allah da kuka ji daga wurinmu, ba ku karɓe ta kamar kalmar mutane ba. Amma kun karɓe ta daidai yadda take, a matsayin kalmar Allah, wadda kuma take aiki a cikinku masu bi. 14 Gama ku ꞌyanꞌuwa, kun zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah waɗanda suke da haɗin kai da Kristi Yesu a Yahudiya, domin kun sha wahala a hannun ꞌyan ƙasarku. Kuma irin wahalolin ne su ma suke sha a hannun Yahudawa, 15 waɗanda su ne kuma suka kashe Ubangiji Yesu, da annabawa, kuma suka tsananta mana. Ƙari ga haka, ba sa faranta wa Allah rai, amma suna gāba da abin da zai amfani dukan mutane, 16 ta wurin ƙoƙarin hana mu yin magana ga mutanen alꞌummai don su samu ceto. Ta yin hakan, suna ƙara cika mudun zunubansu. Kuma a ƙarshe, fushinsa ya zo a kansu.

17 Amma ꞌyanꞌuwa, saꞌad da aka raba mu da ku na ɗan lokaci, (a jiki, ba a zukatanmu ba), da yake muna kewar ku sosai, mun yi iya ƙoƙarinmu don mu iya ganin ku.* 18 Saboda wannan dalilin ne mun so mu zo wurinku, a gaskiya, ni Bulus na yi ƙoƙari, ba sau ɗaya ba amma har sau biyu; duk da haka Shaiɗan ya rufe mana hanya. 19 Gama mene ne begenmu, ko farin cikinmu, ko rawanin ɗaukakarmu a gaban Ubangijinmu Yesu saꞌad da ya dawo? Shin ba ku ba ne? 20 Hakika, ku ne ɗaukakarmu da farin cikinmu.

3 Da muka kasa daurewa, sai muka ga zai fi dacewa a bar mu mu kaɗai a Atina; 2 kuma mun aika muku Timoti ɗanꞌuwanmu kuma bawan Allah* wanda yake yin waꞌazin labari mai daɗi game da Kristi, don ya sa ku tsaya daram kuma ya ƙarfafa ku saboda bangaskiyarku, 3 domin kada tsanantawar nan ta jijjiga wani. Gama ku da kanku kun san cewa ba za mu iya guje wa shan wahalolin nan ba. 4 Lokacin da muke tare da ku, mun sha gaya muku tun da wuri cewa za mu fuskanci tsanantawa, kuma abin da ya faru ke nan, kamar yadda kuka sani. 5 Shi ya sa, da na kasa ci-gaba da daurewa, sai na aiki Timoti domin ya duba yadda bangaskiyarku take, kada ya zama cewa Mai Jarraba* ya jarrabce ku, kuma famar da muka yi ya zama a banza.

6 Amma ga shi Timoti ya dawo daga wurinku yanzu, kuma ya ba mu labari mai daɗi game da bangaskiyarku da ƙaunarku, cewa a kullum kuna tunawa da mu da farin ciki, kuma kuna marmarin ganin mu kamar yadda mu ma muke yi. 7 Shi ya sa ꞌyanꞌuwa, a dukan damuwarmu da kuma tsanantawa da muke fuskanta, mun sami ƙarfafa domin ku da kuma bangaskiyar da kuke nunawa. 8 Muna sake samun ƙarfafa* idan kuna tsaye daram cikin Ubangiji. 9 Gama ta yaya za mu nuna godiya ga Allah game da ku domin farin cikin da muke yi sosai a gaban Allah saboda ku? 10 Dare da rana, muna yin iya ƙoƙarinmu wajen roƙon Allah don mu iya ganin ku* kuma mu ba ku abin da kuka rasa a bangaskiyarku.

11 Yanzu bari Allahnmu, Uba da kansa, da kuma Ubangijinmu Yesu su buɗe mana hanya don mu iya zuwa wurinku. 12 Ƙari ga haka, bari Ubangiji ya sa ku ƙaru, hakika, ya kuma sa ku ƙara nuna ƙauna ga juna, kuma ga kowa, kamar yadda muka yi muku, 13 domin ya sa zukatanku su yi ƙarfi, su zama marasa laifi, masu tsarki kuma a gaban Allahnmu da kuma Uba, saꞌad da Ubangijinmu Yesu zai zo da dukan tsarkakansa.

4 A ƙarshe ꞌyanꞌuwa, kamar yadda kuka karɓi umurni daga wurinmu a kan yadda za ku yi rayuwa don ku faranta wa Allah rai, hakika, haka ma kuke yin rayuwa, muna gaya muku kuma muna roƙon ku ta wurin Ubangiji Yesu, cewa ku ci-gaba da yin hakan sosai. 2 Gama kun san umurnin da muka ba ku ta wurin Ubangiji Yesu.

3 Gama wannan shi ne nufin Allah, cewa ku zama masu tsarki kuma ku guji yin lalata.* 4 Ya kamata kowannenku ya san yadda zai yi iko da jikinsa cikin tsarki da kuma mutunci,* 5 ba tare da haɗama, da muguwar shaꞌawar yin jimaꞌi irin na alꞌummai da ba su san Allah ba. 6 Kada wani ya wuce gona da iri kuma ya cuci ɗanꞌuwansa a wannan batun, don Jehobah* yana hukunta waɗanda suka yi abubuwan nan, kamar yadda muka gaya muku a dā kuma muka gargaɗe ku sosai a kai. 7 Gama Allah bai kira mu don ƙazanta ba, sai dai mu zama masu tsarki. 8 Don haka, mutumin da yake watsi da wannan, ba da mutum ya yi watsi ba, amma da Allah ne, wanda yake ba ku ruhunsa mai tsarki.

9 Amma game da ƙaunar ꞌyanꞌuwa, ba kwa bukatar mu rubuta muku wani abu, domin Allah ya koya muku ku ƙaunaci junanku. 10 Hakika, kuna hakan ga dukan ꞌyanꞌuwa da ke duk fāɗin Makidoniya. Amma muna roƙon ku ꞌyanꞌuwa, ku ci-gaba da yi har ma fiye da hakan. 11 Ku yi iya ƙoƙarinku ku yi rayuwa cikin natsuwa, kuna mai da hankali ga shaꞌaninku kawai, kuma kuna aiki da hannayenku kamar yadda muka umurce ku, 12 domin ku iya yin rayuwar da ta dace a gaban mutanen waje, ba tare da bukatar wani abu ba.

13 Ƙari ga haka ꞌyanꞌuwa, ba ma so ku zama da rashin sani game da waɗanda suka mutu,* domin kada ku yi baƙin ciki, kamar yadda sauran mutanen da ba su da bege suke yi. 14 Domin idan mun ba da gaskiya cewa Yesu ya mutu kuma an ta da shi, haka ma Allah zai ta da waɗanda suka mutu ta wurin Yesu, don su kasance tare da shi.* 15 Gama wannan ne muke gaya muku ta wurin kalmar Jehobah* cewa, mu da za mu kasance da rai lokacin da Ubangiji zai dawo ba za mu riga waɗanda suka mutu tashiwa daga mutuwa ba; 16 domin Ubangiji da kansa zai sauko daga sama ya ba da umurni da muryar shugaban malaꞌiku, ya kuma busa kakakin Allah, kuma waɗanda suka mutu cikin haɗin kai da Kristi za su fara tashiwa. 17 Bayan haka, mu da muke raye a lokacin, za a ɗauke mu zuwa cikin gajimare tare da su, don mu haɗu da Ubangiji a sararin sama; ta hakan, za mu kasance da Ubangiji kullum. 18 Don haka, ku ci-gaba da ƙarfafa juna da kalmomin nan.

5 Yanzu ꞌyanꞌuwa, ba kwa bukatar a rubuta muku kome game da lokuta da kuma zamanai da abubuwan nan za su faru. 2 Gama ku da kanku kun san cewa ranar Jehobah* tana zuwa daidai yadda ɓarawo yake zuwa da dare. 3 A duk lokacin da suka soma cewa, “Akwai salama da zaman lafiya!” sai farat ɗaya su hallaka, kamar yadda zafin haifuwa* yakan kama mace mai ciki, kuma ba yadda za a yi su tsira. 4 Amma ku ꞌyanꞌuwa, ba a duhu kuke ba, har da ranar nan za ta zo muku ba tsammani kamar yadda wayewar gari takan sami ɓarayi ba labari, 5 gama dukanku ꞌyaꞌyan haske ne, da kuma ꞌyaꞌyan rana. Mu ba na dare ko na duhu ba ne.

6 Saboda haka, kada mu yi barci kamar yadda sauran suke yi, amma mu ci-gaba da zama da shiri kuma mu ci-gaba da yin amfani da hankalinmu da kyau. 7 Waɗanda suke barci, suna barci da dare ne, waɗanda suke buguwa kuma, suna buguwa da dare ne. 8 Amma mu da muke na rana, bari mu ci-gaba da yin amfani da hankalinmu da kyau, kuma mu saka rigar ƙarfe na bangaskiya da ƙauna, da kuma begen samun ceto kamar hular kwano 9 domin Allah bai zaɓe mu don ya hukunta mu ba, amma don mu samu ceto ne ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi. 10 Ya mutu a madadinmu, domin ko da muna da rai ko mun mutu,* mu yi rayuwa tare da shi. 11 Saboda haka, ku ci-gaba da ƙarfafa juna* da gina juna kamar yadda kuke yi a yanzu.

12 Yanzu ꞌyanꞌuwa, muna roƙon ku ku riƙa girmama waɗanda suke aiki da ƙwazo a tsakaninku, da waɗanda suke yi muku ja-goranci cikin Ubangiji, da kuma yi muku gargaɗi; 13 kuma cikin ƙauna, ku mutunta su fiye da kima saboda aikin da suke yi. Ku riƙa yin abin da zai kawo salama a tsakaninku. 14 Ban da haka ꞌyanꞌuwa, muna ƙarfafa ku, ku gargaɗi waɗanda ba sa bin tsari, ku yi magana a hanyar da za ta ƙarfafa waɗanda suka yi sanyin gwiwa, ku taimaki marasa ƙarfi, kuma ku riƙa yin haƙuri da kowa. 15 Ku tabbata cewa babu wanda ya rama mugunta da mugunta ga wani, amma a kullum ku riƙa yin abu mai kyau ga junanku da kuma ga kowa.

16 Ku riƙa yin farin ciki a kowane lokaci. 17 Ku yi adduꞌa babu fasawa. 18 Ku riƙa godiya domin kome. Wannan shi ne nufin Allah a gare ku cikin Kristi Yesu. 19 Kada ku dakatar da aikin da ruhu yake yi a cikinku.* 20 Kada ku raina annabci. 21 Ku tabbatar da dukan abubuwa; ku riƙe abu nagari da ƙarfi sosai. 22 Ku guji kowace irin mugunta.

23 Bari Allah na salama da kansa ya tsarkake ku gabaki-ɗaya. Kuma ya sa ruhunku da ranku* da jikinku su zama lafiyayyu a kowace hanya, ya kuma keɓe su a matsayin marasa laifi, har zuwa ranar da Ubangijinmu Yesu Kristi zai dawo. 24 Wanda yake kiran ku mai aminci ne, kuma tabbas zai yi hakan.

25 ꞌYanꞌuwa, ku ci-gaba da yin adduꞌa a madadinmu.

26 Ku gaishe da dukan ꞌyanꞌuwa da sumba mai tsarki.

27 Na roƙe ku cikin sunan Ubangiji, ku tabbata cewa an karanta wasiƙar nan ga dukan ꞌyanꞌuwa.

28 Bari alherin Ubangijinmu Yesu Kristi ya kasance tare da ku.

Ana kuma kiran sa, Silas.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ko kuma “ƙarfin hali.”

A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

A yaren Girka, “don mu iya ganin fuskokinku.”

Yana kuma iya nufin, “abokin aikin Allah.”

Ko kuma “Ibilis.”

A yaren Girka, “muna rayuwa.”

A yaren Girka, “don mu iya ganin fuskokinku.”

A yaren Girka, por·nei′a. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

Ko kuma “daraja.”

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

A yaren Girka, “yi barci.”

Wato, Yesu.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.

Ko kuma “naƙuda.”

A yaren Girka, “yi barci.”

Ko kuma “yi wa juna taꞌaziyya.”

A yaren Girka, “Kada ku kashe wutar ruhu.”

A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba