WASIƘA ZUWA GA KOLOSIYAWA
1 Daga Bulus, manzon Kristi Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma ɗanꞌuwanmu Timoti, 2 zuwa ga tsarkaka da kuma ꞌyanꞌuwa masu aminci da ke da haɗin kai da Kristi a Kolosi:
Bari alheri da salama daga wurin Allah Ubanmu su kasance tare da ku.
3 A kullum mukan gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, saꞌad da muka yi adduꞌa a madadinku, 4 tun lokacin da muka ji game da bangaskiyarku ga Kristi Yesu da kuma ƙaunar da kuke nuna wa dukan tsarkaka, 5 kuna yin hakan ne domin abin da kuke begen sa da aka ajiye muku a sama. Dā ma kun ji game da begen nan ne ta wurin saƙon gaskiya na labari mai daɗi 6 da aka kawo muku. Kamar yadda labari mai daɗin yake ba da ꞌyaꞌya kuma yake ƙara yaɗuwa a dukan duniya, haka ma yake faruwa a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji kuma kuka gane alherin Allah, daidai yadda yake. 7 Abin da kuka koya ke nan daga ƙaunataccen abokin hidimarmu Abafaras, wanda yana yi wa Kristi hidima cikin aminci a madadinmu. 8 Ya kuma gaya mana game da ƙaunar da ruhu mai tsarki yake taimaka muku ku nuna.
9 Hakan ne kuma ya sa tun daga ranar da muka ji hakan, ba mu taɓa daina yin adduꞌa a madadinku ba, da kuma roƙo cewa Allah ya cika ku da cikakken ilimi game da nufinsa, da kowace irin hikima, da kuma ruhu da zai taimaka muku ku fahimci kome. 10 Ta hakan ne za ku yi rayuwar da ta dace da bayin Jehobah,* kuma ku faranta masa rai a kowace hanya, yayin da kuke ba da ꞌyaꞌya a kowane kyakkyawan aiki kuma kuke ƙaruwa cikin cikakken ilimi game da Allah; 11 kuma bari ku sami ƙarfafa, da dukan ƙarfin da kuke bukata ta wurin ikonsa mai ɗaukaka don ku iya jimrewa da kyau cikin haƙuri da kuma farin ciki, 12 yayin da kuke gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci samun gādon da za a ba wa tsarkaka da suke cikin haske.
13 Ya cece mu daga ikon duhu, kuma ya kai mu cikin mulkin Ɗansa da yake ƙauna, 14 wanda ta wurin fansar da ya biya ne muka sami ꞌyanci, wato gafarar zunubanmu. 15 Shi ne siffar Allah da ba a iya gani, ɗan farin dukan halittu; 16 domin ta wurinsa ne aka halicci dukan abubuwa, a sama da kuma a duniya, abubuwan da ake gani, da kuma abubuwan da ba a iya gani, ko kujerun sarauta ne, ko masu mulki, ko gwamnatoci, ko hukumomi. An halicci dukan abubuwa ta wurinsa kuma dominsa. 17 Ƙari ga haka, an halicce shi kafin duk sauran abubuwa, kuma ta wurinsa ne aka sa dukan sauran abubuwa suka soma wanzuwa, 18 kuma shi ne kan jikin, wato ikilisiya. Shi ne farko, wato wanda ya fara tashi daga mutuwa, don ya zama na farko a cikin dukan abubuwa; 19 domin Allah ya ji daɗin mai da shi cikakke a dukan kome, 20 kuma ta wurinsa ne Allah ya yi sulhu tsakaninsa da dukan abubuwa, ko da a duniya ne suke, ko kuma a sama, ya yi sulhun ne da jinin da Kristi ya zubar a kan gungumen azaba.*
21 Hakika, a dā kun yi nisa da Allah kuma kuna gāba da shi domin kun sa zukatanku a kan ayyukan mugunta, 22 amma yanzu ya yi amfani da jikin Ɗansa da ya mutu ya yi sulhu da ku, domin ya miƙa ku ga kansa a matsayin tsarkaka, marasa tabo kuma marasa zargi, 23 idan dai kun ci-gaba cikin bangaskiya, kuna tsaye daram a kan tushen, ba kwa jijjiguwa kuma ba ku kauce wa begen da kuka samu daga labari mai daɗi da kuka ji ba, wanda aka yi waꞌazin sa ga dukan halittu da ke ƙarƙashin sama. Ni Bulus, na zama mai hidimar wannan labari mai daɗi.
24 Yanzu ina farin cikin shan wahaloli saboda ku, amma a ganina ban gama shan wahalar da ya kamata in sha a madadin jikin Kristi ba, wato ikilisiya. 25 Na zama mai hidima na ikilisiyar bisa ga amanar da Allah ya ba ni a madadinku don in yi waꞌazin kalmar Allah da kyau, 26 wato, sirri mai tsarki da aka ɓoye tun daga zamanai* da suka wuce da kuma tsarar da suka wuce. Amma yanzu Allah ya bayyana su ga tsarkakansa, 27 Allah ya yi farin cikin nuna wa mutanen nan daga alꞌummai, arziki mai ɗaukaka na wannan sirri mai tsarki, sirrin shi ne Kristi na da haɗin kai da ku, wanda yake nufin cewa kuna da begen samun ɗaukaka tare da shi. 28 Shi ne wanda muke shelar sa, muna yi wa kowa gargaɗi kuma muna koyar da kowa cikin kowace irin hikima, domin mu iya miƙa kowa cikakke cikin haɗin kai da Kristi. 29 Saboda haka ne ina aiki da ƙwazo, ina yin iya ƙoƙarina da taimakon ikonsa da ke aiki a jikina.
2 Gama ina so ku san yawan fama da nake yi a madadinku da waɗanda suke Laudikiya, da kuma a madadin dukan waɗanda ba su taɓa gani na ba. 2 Ina yin hakan ne domin su samu ƙarfafa kuma su zama da haɗin kai cikin ƙauna. Ta hakan za su samu dukan arziki saboda tabbacin da suke da shi a kan abin da suka fahimta, domin su samu cikakken ilimi game da sirri mai tsarki na Allah, wato Kristi. 3 Dukan dukiyoyi na hikima da na daraja, an ɓoye su da kyau a cikinsa. 4 Ina faɗan hakan ne domin kada wani ya ruɗe ku da maganganun yaudara. 5 Ko da yake ba na tare da ku a zahiri,* amma ina tare da ku cikin ruhu, ina farin cikin jin yadda kuke yin abubuwa cikin tsari kuma bangaskiyarku ga Kristi tana nan daram.
6 Saboda haka, kamar yadda kuka karɓi Kristi Yesu Ubangiji, ku ci-gaba da rayuwa cikin haɗin kai da shi, 7 ku kafu, kuma ku ginu cikin Kristi, ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya, kamar yadda aka koya muku, kuma ku riƙa yin godiya sosai.
8 Ku lura kada wani ya ja hankalinku* ta wurin hikimar duniyar nan, da ilimin ruɗu na banza, domin suna bisa alꞌadar mutane ne, ko kuma bisa ga hanyoyi da raꞌayoyin duniya, ba bisa ga Kristi ba; 9 domin a cike Kristi yake da dukan halayen Allah. 10 Don haka, kun zama cikakku ta wurinsa, wanda shi ne shugaban dukan gwamnatoci da hukumomi. 11 Ta wurin dangantakarku da shi, ku ma an yi muku kaciya, amma kaciyar ba wadda aka yi da hannaye ba ne. A maimakon haka, kun kawar da jiki mai zunubi, wato kun yi kaciyar da take na Kristi ke nan. 12 Gama an binne ku tare da shi, domin kun yi irin baftismarsa, kuma saboda dangantakarku da shi, an ta da ku tare don bangaskiyarku ga ikon Allah, wanda ya ta da shi daga mutuwa.
13 Ƙari ga haka, ko da yake a dā ku matattu ne saboda zunubanku da kuma rashin kaciyarku, Allah ya sa kun rayu tare da shi, ya gafarta dukan zunubanmu da dukan zuciyarsa 14 kuma ya share dokokin da aka rubuta da hannu waɗanda suke gāba da mu. Ya kawar da su ta wajen rataye su a kan gungumen azaba.* 15 Ta wurin gungumen azabar,* ya yi nasara a kan gwamnatoci da hukumomi, ya nuna a fili cewa ya yi nasara a kan su, kuma yana zagayawa da su a matsayin fursunonin da ya kama.
16 Saboda haka, kada ku bar wani ya shariꞌanta ku game da abin da kuke ci ko kuke sha, ko game da yin wani biki, ko bikin sabon wata, ko kuma hutu a Ranar Assabaci. 17 Waɗannan abubuwa misali* ne na abubuwan da ke zuwa, amma ainihin abin da ke zuwa shi ne Kristi. 18 Kada ku bar wani ya sa ku rasa ladan, wato wanda yake nuna sauƙin kai na ƙarya, yana bautar malaꞌiku, kuma “yana dogara ga”* abubuwan da ya gani. Yana ɗaga kai ba tare da wani dalilin da ya dace ba, domin yana tunani yadda mutum ajizi yake yi, 19 irin mutumin nan ba a haɗe yake da kan ba, wanda ke ba wa jiki dukan abubuwan da yake bukata kuma yake amfani da gaɓoɓi da jijiyoyi ya haɗa jikin tare. Kan yana sa jikin ya yi girma, kuma girman daga wurin Allah ne.
20 Idan kun riga kun mutu tare da Kristi a bin hanyoyi da raꞌayoyin duniya, me ya sa kuke rayuwa kamar har yanzu ku na duniya ne ta wajen ƙara miƙa kanku ga dokokin nan cewa: 21 “Kada ka yi amfani da wannan, ko ka ɗanɗana wannan, ko kuma ka taɓa wannan,” 22 waɗannan kuwa duk abubuwa ne da za su lalace bayan an yi amfani da su, kuma su dokoki ne da koyarwar mutane? 23 Ko da yake dokokin nan suna da alamar hikima, amma ba sa taimaka wa mutum ya guje wa shaꞌawoyin jiki, kuma hakan na faruwa ne domin mutane suna zaɓa wa kansu yadda za su yi bauta, suna nuna sauƙin kai na ƙarya da kuma wahalar da jikinsu.
3 Amma idan an ta da ku tare da Kristi ne, ku ci-gaba da yin ƙoƙarin samun abubuwan da ke sama, wurin da Kristi yake zaune a hannun dama na Allah. 2 Ku riƙa yin tunani a kan abubuwan da suke sama, ba a kan abubuwan da suke duniya ba. 3 Gama kun mutu, kuma an ɓoye ranku tare da Kristi cikin haɗin kai da Allah. 4 Saꞌad da aka bayyana Kristi, wanda shi ne ranmu, ku ma za a bayyana ku tare da shi cikin ɗaukaka.
5 Saboda haka, ku kashe gaɓoɓin jikinku da ke duniyar nan, waɗanda daga cikinsu ne shaꞌawoyin nan suke tasowa, wato lalata,* da ƙazanta, da muguwar shaꞌawar yin jimaꞌi, da shaꞌawa marar kyau, da haɗama, wadda ita ce bautar gumaka. 6 Saboda abubuwan nan ne fushin Allah yake zuwa. 7 A dā ku ma kuna yin abubuwan nan. 8 Amma yanzu, dole ne ku kawar da dukan abubuwan nan daga jikinku, wato fushi, da zafin rai, da mugunta, da zage-zage, da kuma maganganun iskanci. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya. Ku cire tsohon hali* da ayyukansa, 10 kuma ku saka sabon hali, wanda ake sabunta shi ta wurin cikakken ilimi, bisa ga siffar Wanda ya halicce shi. 11 Sabon halin ba ya nuna bambanci tsakanin mutumin Girka da Bayahude, da mai kaciya da marar kaciya, da baƙo, da ɗan ƙauye, da bawa da mai ꞌyanci; amma Kristi ne kome kuma a cikin kowa.
12 Saboda haka, a matsayinku na waɗanda Allah ya zaɓa, masu tsarki kuma ƙaunatattu, ku saka* ƙauna, da tausayi, da alheri, da sauƙin kai, da rashin zafin rai, da kuma haƙuri. 13 Ku ci-gaba da jimre abin da kuke yi wa juna, da gafarta wa juna daga cikin zuciyarku ko da wani yana da dalilin yin fushi don laifin da wani ya yi masa. Kamar yadda Jehobah* ya gafarta muku da dukan zuciyarsa, dole ne ku ma ku yi hakan. 14 Amma ban da dukan abubuwan nan, ku saka* ƙauna, gama ita ce asalin abin da ke kawo haɗin kai.
15 Ƙari ga haka, bari salamar Kristi ta yi mulki a zukatanku, gama saboda salamar ce aka kira ku ku zama jiki ɗaya. Kuma ku nuna cewa ku masu godiya ne. 16 Bari kalmar Kristi ta kasance a cikinku da kyau, kuma ta ba ku kowace irin hikima. Ku ci-gaba da koyar da juna, da ƙarfafa* juna da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo ga Allah, da waƙoƙin ibada da aka rera tare da godiya, kuma kuna rera waƙa ga Jehobah* daga zukatanku. 17 Ko da mene ne kuke yi, ko a furucinku ko a ayyukanku, ku yi kome cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.
18 Ku mata, ku miƙa kanku ga mazanku, kamar yadda ya dace da masu bin Ubangiji. 19 Ku maza, ku ci-gaba da ƙaunar matanku kuma kada ku riƙa yawan fushi da su.* 20 Ku yara, ku riƙa yi wa iyayenku biyayya a cikin kome, don hakan na faranta ran Ubangiji. 21 Ku ubanni, kada ku riƙa yin abin da zai ɓata wa yaranku rai, domin kada su karaya.* 22 Ku bayi, ku yi biyayya cikin kome ga shugabanninku,* ba kawai saꞌad da suke ganin ku don ku faranta wa mutane rai ba, amma ku yi hakan tsakaninku da Allah, da kuma don tsoron Jehobah.* 23 Ko da mene ne kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku* kamar ga Jehobah* ne kuke yin shi, ba ga mutane ba, 24 domin kun san cewa daga wurin Jehobah* ne za ku sami gādon a matsayin lada. Ku yi hidima ga Shugabanmu, Kristi. 25 Hakika, duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifin da ya yi, kuma ba za a nuna bambanci ba.
4 Ku shugabanni, ku bi da bayinku cikin adalci kuma a hanyar da ta dace, kuna tuna cewa ku ma kuna da Shugaba a sama.
2 Ku nace da yin adduꞌa, ku zauna a faɗake a yin ta, tare da gode wa Allah. 3 Ƙari ga haka, ku yi adduꞌa a madadinmu ma cewa Allah ya buɗe mana hanyar yin waꞌazin kalmarsa don mu yi shelar sirri mai tsarki game da Kristi, gama wannan dalilin ne ya sa aka ɗaure ni a kurkuku, 4 ku kuma yi adduꞌa in yi shelar sa da kyau, yadda ya kamata in yi.
5 Ku ci-gaba da bi da mutanen waje cikin hikima, kuma ku riƙa amfani da lokacinku a hanyar da ta fi dacewa.* 6 A kullum, bari abubuwan da kuke faɗa su kasance da daɗin ji, kamar an saka gishiri, don ku san yadda za ku amsa wa kowane mutum.
7 Tikikus ƙaunataccen ɗanꞌuwana, mai hidima da aminci, kuma bawan Ubangiji kamar ni, zai gaya muku dukan abubuwa game da ni. 8 Ina aika muku shi domin ku san yadda muke kuma ya ƙarfafa zukatanku. 9 Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunataccen ɗanꞌuwana mai aminci, wanda ya fito daga wurinku; su biyun za su gaya muku dukan abubuwan da suke faruwa a nan.
10 Aristarkus wanda yake cikin kurkuku tare da ni, yana aika muku gaisuwarsa, har da Markus wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas (wanda aka ba ku umurni cewa ku marabce shi idan ya zo wurinku), 11 tare da Yesu wanda ake kira Justus. Mutanen nan suna cikin waɗanda aka yi wa kaciya, su ne kaɗai abokan aikina na Mulkin Allah, kuma sun zama abin ƙarfafa a gare ni sosai. 12 Abafaras bawan Kristi Yesu ya aika muku gaisuwarsa, a kullum yana yin adduꞌoꞌi sosai a madadinku, domin a ƙarshe ku zama cikakku, ku kuma kasance da tabbaci sosai a kan dukan nufin Allah. 13 Gama na ba da shaida a kansa cewa yana ƙoƙari sosai a madadinku, da a madadin waɗanda suke Laudikiya da kuma Hirafolis.
14 Luka, likitan nan da muke ƙauna, ya aika muku gaisuwarsa, har da Dimas. 15 Ku miƙa gaisuwata ga ꞌyanꞌuwan da ke Laudikiya, da kuma ga ꞌyarꞌuwa Nimfa da ikilisiyar da ke gidanta. 16 Bayan an karanta wannan wasiƙar a tsakaninku, ku kuma shirya a karanta wasiƙar a ikilisiyar da ke Laudikiya, ku ma ku karanta wadda aka aiko daga Laudikiya. 17 Ƙari ga haka, ku gaya wa Arkibus cewa: “Ka mai da hankali ga hidimar da ka karɓa daga wurin Ubangiji, domin ka iya yin ta da kyau.”
18 Ni Bulus nake rubuta muku wannan gaisuwar da hannuna. Ku ci-gaba da tuna cewa an ɗaure ni a kurkuku. Bari alherin Allah ya kasance tare da ku.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
A yaren Girka, “jiki.”
Ko kuma “kama hankalinku.”
Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Yana kuma iya nufin, “Kristi.” Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
A yaren Girka, “inuwa.”
Wannan furuci ne daga abin da masu bautar gumaka suke faɗa saꞌad da suke shigar da mutum cikin ƙungiyarsu.
A yaren Girka, por·nei′a. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
A yaren Girka, “mutuntaka.”
Yadda ake saka riga.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Yadda ake saka riga.
Ko kuma “gargaɗi.”
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ko kuma “kada ku riƙa yi musu hasala.”
Ko kuma “fid da rai.”
A yaren Girka, “shugabanninku na jiki.”
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
A yaren Girka, psy·kheʹ. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ka duba sashen Wasu Bayanai na A5.
Ko kuma “ku nemi lokaci.”